Tuesday, August 27, 2019
YADDA AKE TUNKARAR BUDURWA
YADDA AKE TUNKARAR BUDURWA
Daga Shafin www.Naimismo.com.ng
Idan kaga 'yar budurwa tana tafiya sai kaga tashiga zuciyarka kuma kanason yi mata magana..
* Dafa rko dai ka tabbata kaima kahadu ma'ana kadau wanka mai kyau saboda wanka yana daya daga ckn abunda ke sato maka zuciyara mace..sai karka yi mata magana sai ka tabbata tazo dai dai gurin da babu mutane sosai don wata tana da alkunya.
* Daka karasa gurinta dakaje sai kafara yi mata sallama kamar yanda addininmu yatanadar nasan indai ta cika musulma zata amsamaka kaga kasamo hankalinta kenan.
* Sai kace ranki yadade kiyi hakuri fah nasan ba mutuncin kyakkyawar mace mai haiba da asali bane tatsaya ta kula namiji a yayin datake tafiya izuwa wani guri, amma kiyi hakuri nima bayin kaina bane wani sashen bangaren jikinane ya uzuramin dole sai nayi hakan tun yayin da idanuwana sukai arba da wannan kyakkyawar surar taki.
* Kar dai incikaki da surutu nasan kina sauri ne saboda haka nake neman wata alfarma guda 2 zuwa 3 agunki.
Wannan kuma kai-kaisan me zaka tambaya 😁
Read More»
Friday, August 23, 2019

KO DAI AIKIN GAMA ZAI GAMA DA GANDUJE A KOTU NE?

1 – An tabbatar da hargitsa kuri’un Gama da aka yi a zaben farko na ranar 9 Ga Maris, wanda aka kama Mataimakin Gwamna, Nasiru Gawuna, Kwamishina Murtala Sule Garo da Shugaban Karamar Hukuma.
2 – An tabbatar da an kekketa kuri’u da dama a wurin.
3 – A zabe na biyu da aka maimaita, an tabbatar da tafka magudi da jam’iyya mai mulki a Kano, APC ta yi a wurare da dama.
3 – An tabbatar da tada hankulan jama’a, cin zarafin ‘yan jam’iyyar adawa, hana wasu da dama yin zabe. Wasu kuma kafin su je har an dangwale kuri’un na su.
4 – An tabbatar da ’yan-ta-kife sun sari mutane da dama, aka jikkata masu tarin yawa.
5 – An tabbatar da yin hatsaniya, a wuraren da zugar ‘yan-ta-kife dauke da muggan makamai suka rika fatattakar masu zabe.
5 – An tabbatar da cin zarafin masu sa-ido kan zabe.
6 – An tabbatar da cin zarafin ‘yan jarida ba daya ba.
7 – An tabbatar da sakacin jami’an tsaro a wasu wurare.
8 – Bayanai da dama sun ki gamsar da jama’a yadda PDP da dan takarar ta Abba Yusuf ba su ci kuri’un kirki a zaben da aka maimaita ba.
9 – Bayanai sun kasa gamsar da jama’a da yawa, yadda Ganduje da APC suka samu tulin kuri’un da suka wuce misali, har a mazabun da PDP ke da rinjaye da kuma inda rahotanni suka nuna an hana masu adawa fitowa su yi zabe.
10 – Rahotanni sun nuna akwai inda maza suka shiga layi da katin zaben mata suka rika dangwala kuri’a.
11 – Akwai bidiyo da dama wadanda suka rika nuna yadda ‘yan-takifen APC suka rika tayar da hargitsi da yamutsi da rincimi a wuraren zabe. Kuma sun a dauke da muggan makamai.
12 – Yadda Maitaimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda mai lura da yadda aka gudanar da zaben da aka maimaita a ranar 23 Ga Maris, ya ce an yi zabe lami lafiya.
13 – Wannan abin dubawa ne da iron basira, musamman idan alkalai suka gamsu da cewa an tafka yamutsin hargitsa zabe da kuma hana ‘yan adawa yin zaben da sauran hauragiyar da ta faru a ranar.
Kungiyar Tarayya Turai ta gamsu da bayanan da masu sa-ido suka gabatar mata cewa an yi haurgiya a zaben.
Kungiyoyin sa-ido na cikin gida na sauran na kasashen ketare sun ce an yi hauragiya, an yi amfani da makaman da aka ji wa masu adawa raunuka.
Amnesty International ma ta ce a binciki abin da ya faru ranar zaben.
’Yan jaridu da dama sun bada labarin wainar da aka toya. Wadanda aka ci wa zarafi kuma sun bayyana abin da ya faru da su.
Babbar hujja kuma ita ce kasassabar da Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas ya yi, inda aka nuno shi a wani bidiyo kafin zabe ya na rantsuwa cewa ko PDP ta ci zabe ba za su ba ta ba. Su ke da gwamnati, su ke da sojoji, su ke da ’yan sanda, kuma su ke da SSS.
Duk a cikin bidiyon an nuno shi ya na zuga wasu gungun matasa kana bin da ya ke so su yi a ranar zabe. Shin wadanne hujjoji kotu za ta kara nema, fiye da wadannan? ✍🏻
🌎NAIMISMO1🌎

Subscribe to:
Comments (Atom)