Fateema Habeeb 13
na
Jamilu el hussain zazzau
dedicated to
Amina baba kaduna
kallon habib principal yayi, yace jeka kiramin malamin dake kira muku rijista, da sauri habib yaje yakira malam ayuba su dawo tare,
kallon malam ayuba principal yayi, yace shin yaron nan na zuwa school? nadan lokaci kadan malam ayuba yay shiru, sannan ya girgida kai yace gaskiya ya kwana biyu bezo ba, jin haka yasa malam sani ya kalli habib cikin bacin rai yace to ina kake zuwa?
shiru habib yayi yaki magana, ganin haka yasa malam sani yace ma principal malam buhari inason kuba yaron nan kashi har saiya fada muku gurinda yake zuwa, yana fadin haka ransa abace ya tashi ya wuce,
tsawa principal ya dakawa habib, yace idiot sa guiwar ka akasa,
sallama suji, copper yusif ne ya shigo yace sir akwai chalk anan kuwa? principal yace eh akwai, na staff yakare ne? copper yusif yace yes sir, principal yace ok kwasa da yawa katafi dashi, ya diba zai fita principal yace copper idan kaje kace ma displine yazo da sauri inason ganin shi, yace ok sir, yana zuwa ya fadama displine, da sauri displine yabar abinda ya keyi ya kama hanya,
yana shigowa yace gani sir, principal yace ok abinda nakeso dakai kaje da yaron nan kabashi kashi sosai har saiya fada maka gurinda yake zuwa baison zuwa school, displine yace ok sir, kallon habib yayi yace tashi muje,
agaba ya tasa shi zuwa office din shi, suna shiga yace sa guiwar ka akasa dan ubanka, da sauri habib yay nildown, displine ya kalle shi yace to zaka fadamin ne ko saina sosa maka baya?
kadan habib ya dago kai yace babu inda nake zuwa, dariyar mugunta displine yayi yace yaro kenan, cire riga dan ubanka, a tsorace habib yacire rigar sa domin yasan halin displine din, ya rage daga shi sai singlet,
ko tausayi babu displine yay ta tsala masa dorina yana cewa zaka fadamin ko kuwa? nin shi kawai habib ya keyi yakasa magana, kafin kace wani abu yayi masa rudu rudu da jiki, duk dukan da habib yasha baisa ya fadi komai ba,
ganin haka yasa displine yace yaro idan kasan wata bakasan wata ba, fatanya ya dauka yace tashi muje, tsakiyar rana ya fita dashi ya nuna mishi wani katon fili cinkushe da ciyawa, yace kaga duk girman wajen nan kai zaka nome shi duka idan baka fadamin gurinda kake zuwa ba, ya mika mishi fatanyar yace gashinan fara nizan wuce office idan ka shirya fadamin saika ajiye fatanyar kazo office ka sameni,
dukawa habib yayi ya dau fatanyar ya dukufa noman ciyawa ko hutawa beyi, har lokacin tashi yayi displine bezo ya sallame shi ba, haka students kowa ya shiga wuce wa yana kallon shi, har students kowa ya gama wuce wa gida sai shi kadai ya rage yana ta famar aiki,
zuwa can displine yazo domin ya duba ya gani ko habib yayi aikin da yasa shi, yana zuwa ya taras habib yayi aikin tas abin ya bashi mamaki, dariya yayi yace yaro kenan, wato kai dan taurin kai ko? ba damuwa, yanzu zaka fadamin ne kokuwa?
shiru habib yayi kamar ba dashi ya keyi ba, dariyar mugunta displine ya saki gami da nunawa habib wani katon fili yace tunda kace kai kangararre ne to yau anan zaka yini, dauki fatanya ka cigaba da aiki,
dukawa habib yayi ya dauki fatanyar ya nufi gurin, murmushi displine yayi yasa kai ya kama hanyar gida, duk a tunanin sa habib zai kira shi ya fada mishi, ko dago kai habib beyi ba ya cigaba da aikin,
duk school kowa ya watse, ya rage sai shi kadai ga yunwa ga gajiyan aiki, ga kuma zafin rana dake damunsa da kuma zafin dukan daya sha, sai misalin karfe biyar na yamma ya gama aikin,
yana gamawa ya dauki rigarsa ya saka yana tafiya da kyar yanufi gida, murja na zaune a inuwa tana hutawa habib ya shigo gida wujiga wujiga, tsabar tausayi har tana hawaye, tace habib bansan lokacin daka fara gagara ba, yanzu kaki fada musu gurinda kake zuwa ka gwammace aita dukan ka kamar jaki ko?
shiru yayi bece komai ba yasami waje ya zauna, kai tsaye murja ta tashi ta dauko mishi abincin sa,
6:00pm malam sani ya dawo daga kasuwa, yana shigowa ya iske habib ya baje a tabarma yana huta gajiyar horon da yasha, hararan shi yayi yace shasha shan banza mai kunin kashi, mu zuba nida kai muddin kace gagara zakayi ni kuma zan cigaba da basu umarni suna baka kashi, a ranar habib yakasa zuwa ko ina saboda wahalar da yasha,
from the experience of jamilu zazzau
WhatsApp 08104550703