Thursday, January 23, 2020

Home Fateema Habeeb 24
..
Fateema Habeeb  24

                    na
Jamilu el hussain zazzau

           dedicated to
     Amina baba kaduna

3 weeks letter,

A kullum soyayyar fatima sake bijirowa habib keyi acikin zuciyar sa, zaune yake watarana a cikin gida yana tunanin ta, kawai zuciyar shi ta rada mishi cewa ya tashi ya tafi lodge din su domin yay tozali da ita ko zuciyar ta sami saukin tunanin da takeyi,

tashi yayi ya debi ruwa ya  shiga bandaki, yana fitowa sami lotion mai kamshi ya shafa, sannan ya canza kaya kai tsaye ya nufi lodge din, ko tsoro babu cikin zuciyar habib kai tsaye yasa kai ya shiga ciki,

yana shiga ya iske duk basa nan dakunan su akulle duk sun shiga cikin gari, yana duba igiyar shanyar dake ciki ya iske kayan fatima tayi wanki, maka ya dauka a jikin wani window ya rubuta, zanyi alfaharin kasancewa tare dake har karshen rayuwa ta, yana gama rubutun ajikin mayafin ta ya mayar da makan ya fito yay tafiyar sa,

6:00pm na yamma fatima su dawo daga cikin gari, suna shiga lodge ta kwashe shanyanta ta shiga dasu daki, bayan sun gama abinci kowa taje tai sallah, sannan su dawo kan abincin suna ci suna fira, zuwa karfe goma su fito atare sukai brush sannan su koma daki su kwanta,

misalin karfe sha biyu na dare a kawo nepa, fatima na farkawa ta gansu acikin haske sun manta basu kashe kwan dakinsu ba,

tana zame mayafin kwanciyar a jikin ta taga wannan rubutun, da sauri ta saki mayafin ta tsandara ihu, a firgice kadija ta farka tana tambayar ta lafiya kuwa?

karar kwan kwasa kofa suji, cikin faduwar gaba kadija tace waye? copper yusif yace mune ihu muji me yake faruwa ne? kai tsaye ta taso ta bude musu kofar su shigo,

watso mata kallo suyi gaba daya suna tambayar ta lafiya kike zabga irin wannan ihun acikin daren nan, bargon ta nuna musu tace ku duba mayafin kwanciya ta kuga rubutun dake ciki,  copper yusif ya tsuguna ya dauka gami da karantawa ya gani,

sannan ya kalle su yace yanzu kunga dare ne, saboda haka abinda nake so daku kowa ya koma daki ya kwanta, idan Allah ya kaimu gobe saimu shiga da bargon school mu nunawa principal, suce ok ba damuwa, kai tsaye kowa ya koma daki ya kwanta,

washe gari da safe bayan sun shirya, copper's sama da biyar su jera tare da fatima zuwa cikin school, suna shiga school din kai tsaye su zame zuwa office din principal,

permission su dauka, yace yes ku shigo, ganin su da yawa yasa principal ya dago kai yace lafiya kuwa? kadan kadija ta saki fuska tace lafiya qalau sir,

from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp   08104550703
No comments:
Write comments

Follow Admin On Twitter naimismo1
Join Our Newsletter