Thursday, January 23, 2020

Home Fateema Habeeb 25
..
Fateema Habeeb  25



                   na
Jamilu el hussain zazzau



             dedicated to
       Amina baba kaduna



ALLAH KA JIKAN MAHAIFINA, ALLAH KA GAFARTA MISHI, YA ALLAH KA KAI HASKE KABARINSA, ALLAH KASA MUTUWA HUTUCE AGARESHI DA SAURAN MUSULMI BAKI DAYA




Waje kowannen su ya samu ya zauna, principal ya dago kai gami da kallon su rike da biro a hannusa yace to ina jinku meke faruwa ne? bargon lullubar fatima copper yusif ya amsa ya mikawa principal yace sir kalli yadda yaron nan yaje har lodge dinmu yay ma fatima rubutu a jikin mayafin kwanciyar ta,

amsar bargon principal yayi, tsaf ya karanta abinda ke ciki abin ya bashi mamaki, kai ya dago ya bisu da kallo daya bayan daya, sannan yace kuna da tabbacin cewa shiya rubuta?

budar bakin copper kadija tace of course sir, domin yayi irin hakan sau da yawa ni nake kare shi, kawai gajiya nayi shiyasa nake ganin ya kamata nabari a hukunta shi ko zai gane kuskuren sa,

na dan lokaci kadan principal yay shiru, sannan ya dago kai ya kalle su yace ba damuwa ku tashi kuje, hukumar makaranta zatai zama a kanshi, atare su hada baki suce thanks u sir, sannan suka fito daga office din su wuce staff,

principal na kammala abinda ya keyi ya fito, kanshi tsaye ya nufi staff ya kira sajan sunufi class din su habib, suna shiga students duk su mike, yace kar ku damu ku zauna, ina habib sani? hannu habib ya daga yace sir ganinan,

harara sajan ya jefo masa yace stupid come out, kai tsaye habib ya kama hanya ya fito, yana zuwa gabansu sajan ya zabga mishi mari yace wawan banza wuce muje, a gaba su tasa keyar habib zuwa office din principal,

suna shiga su saka shi ya zube akasa, kafin kace wani abu sajan yafara sauke mishi dorina ajiki, kallo principal ya watso mishi yace kyale shi haka, sannan ya kalli habib ya nuna masa mayafin fatima yace meyasa kai wannan rubutun?

dago kai habib yayi ya kalli rubutun, sannan ya sunkuyar dakai kasa, tsawa principal ya daka mishi yace ba dakai nakeyi ba, baza kai magana ba? kadan habib ya dago kai yace sorry sir, ran principal abace yace sorry for what? yace please sajan ci min uban yaron nan, ji kake tas, tas, ganin jikinsa yayi laushi yace barshi haka,

kallo principal ya watso ma habib cikin bacin rai yace idiot go back to your class, sannan ka jira hukuncin da hukumar makaranta zata yanke akan ka, tashi habib yayi cikin tsamin jiki yanufi class din su,

yana fita principal ya kalli sajan yace jeka kiramin vice da admin master kace kome su keyi su bari suzo akwai al amari na ujila, sajan yace ok sir, da sauri sajan yaje ya sanar dasu, cikin hanzari kowannen su ya kamo hanya yazo,

kallo vice ya watso ma principal gami da cewa sir lafiya kuwa? a tsanake principal ya basu labarin duk abubuwan da habib yay ma fatima, nanfa su shiga cancel meeting, daga karshe duk bakin su yazo daya, suka yanke shawarar cewa kawai a kore shi daga school din,




from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp  08104550703
No comments:
Write comments

Follow Admin On Twitter naimismo1
Join Our Newsletter