Fateema Habeeb 22
na
Jamilu el hussain zazzau
dedicated to
Amina baba kaduna
ok meyasa kai wannan rubutun? budar bakin sa yace sir gaskiya banji dadin abinda tasa aima same name dina bane, principal yace ok za kaci ubanka,
kallon teachers din nan yayi yace ku bashi kashi, atare su fara tsulan shi, ji kake tas tas tas tako ina, ganin jikin sa yayi laushi principal yace ku kyale shi haka, kallo ya watso mishi yace stupid tashi ka wuce class gobe ka sake, cikin tsamin jiki takwaran habib ya tashi ya koma class din su,
3 weeks da faruwar wannan al amarin, class teacher din su habib ya aike shi staff ya dauko mishi register, yana shiga staff habib ya iske teachers din dake ciki sai famar dibar fira su keyi, fakar idon su yayi ya karisa kujerar fatima, wani littafi ya gani a saman table dinta da sauri ya bude bangon littafin ya rubutu I love u fatima, yana rubutawa ya mayar da sauri ya aje, kai tsaye yaje ya dauki register din ya fita,
12:pm na rana fatima ta dawo staff, tana shigowa ta iske kadija zaune tana hutawa, kallo ta watso mata kawa baki da class ne? kai kadija ta dago su hada ido tace sai zuwa 12:50pm,
bag fatima ta ajiye sannan ta sami waje ta zauna, tana kallon book dinnan taga alamar kamar an taba, domin habib bai mayar dashi inda ya same shi ba, tana budewa taga wannan rubutun, fuska a daure ta nunawa kadija tace kawa kinga abinda wani dan iska yay min ko,
amsa kadija tayi tace mugani me aka rubuta? tana dubawa tai murmushi tace haba to menene don ance I love u? bafa I hate u aka rubuta ba, kai fatima ta girgida tace lallai ne kawa yanzu na fahimci ko kadan bakya son gaskiya,
numfashi kadija taja, tace bahaka bane kawai dai kin kasa fahimta tane, amma dan Allah mubar maganar nan iya mu biyu basai kowa ya sani ba, domin kina fada za ace habib ne koda bashi ya aikata ba,
ummm aini nama fiso ace shi dinne a farfasa mishi jiki, domin na tsane shi sosai, hannu kadija ta dora a kafadar ta tace naji, amma dan Allah akan wannan kiyi hakuri idan ki sake gani saiki dau mataki koma me zakiyi bazan hanaki ba, numfasawa fatima tayi tace to shikenan, nan suka bar wannan firar suka shiga wata saugar,
ana gab da tashi school kadija taje har class din su habib ta kira shi, a waje su tsaya, tace kaga habib tambayar ka nake so nayi amma banso kai min karya, fuska a sake yace ba damuwa malama yi tambayar ki naji,
tace kaine kaje har staff kayi wa fatima rubutu a bangon littafin tako? nadan lokaci kadan yay shiru sannan ya dago kai yace hakane nine,
tace haba habib meyasa kai haka, shin taya ma akayi ka shigo har cikin staff babu wanda ya ganka? uncle ne ya aike ni staff na dauko mishi register, ina shiga na iske teachers sai dibar fira su keyi duk hankalin su baya kaina, kawai sai nayi amfani da wannan damar na rubuta,
shiru kadija tayi tana sauraran shi, yana gamawa tace tabbas kayi babban kuskure domin da ace wani ya ganka fa? kai ka sani da yanzu wani labarin ake ba wannan ba, saboda haka ina baka shawara kada ka sake aikata irin wannan kaji,
yace zan kiyaye insha Allahu, tace to shikenan Allah yasa, yace amin malama nagode,
from the experience of jamilu zazzau
WhatsApp 08104550703










Munajin dadin irin wannan labarai haka
ReplyDelete