Fateema Habeeb 12
na
Jamilu el hussain zazzau
dedicated to
Amina baba kaduna
2 weeks letter, habib ya dauke kafa da zuwa school, kullum yay shirin school saiya zame can bayan gari gurinda ya ajiye hotunan fatima, bashi da aikin daya wuce zana hotunan ta da kuma jera baitocin soyayya,
ganin kwana biyu baizo school bane yasa abdurrahaman yaje har gidan su domin ya duba yaga ni ko lafiya yasa be zuwa,
yana shiga gidan ya iske murja zaune tana wanke wanke, sallama yay mata ta amsa, tace malam abdul yau kaine agidan namu? yace eh umma, aciki ladabi ya gasshe ta, yace dama nazo duba habeeb ne,
da sauri murja ta dago kai ta dube shi dakyau tace wani habib kuma? shida ya wuce school tun dazu, kai abdurrahaman ya girgida yace umma habib baizo school yau ba, hasalima ya kwana biyu bai zuwa, wannan dalilinne ma yasa nace bari nazo na duba nagani ko bashi da lafiya ne,
jin wadan nan jerin bayanan na abdurrahaman ya batawa murja rai sosai, kallo ta sake watso mishi, tace kaga abdul dan Allah kafada min gaskiyar abinda kasani,
rantsewa abdurrahaman yayi, yace wallahi umma habib yakai kusan sati biyu rabon shi da school, kuma a zahirin gaskiya bansan gurin da yake zuwa ba, murja tace nagode yaro jeka abinka zai dawo gidan zai fada mana gurin da yake zuwa, abdurrahaman yace to sai anjima, kai tsaye ya kama hanya ya koma school,
1:30pm atashi daga school, kai tsaye habib ya kama hanya yabi bayan dalibai yanufi gida kamar wanda yaje school, yana shiga gida ko zama baiyi ba murja ta daka mishi tsawa tace daga ina kake? yace daga school nake, tace rufe min baki makaryaci, dazun nan abokin ka yazo neman ka, yace kusan sati biyu kenan baka zuwa school din, shin ina kake tafiya?
kai habib ya dago yace wallahi karya ya keyi kullum sai naje, tace to shikenan bari mahaifin ka ya shigo na sanar dashi, daki habib ya shiga, tashi guda zufa yafara keto mar yana tunanin abinda zai biyo baya muddin mahaifin shi yasan bai zuwa school,
yamma nayi malam sani ya dawo daga kasuwa, kamar kullum murja taje ta tarbe shi ta kawo mishi ruwa mai sanyi da abinci, bayan ya huta ta kwashe labarin da abdurrahaman ya kawo mata tsaf ta fada mishi, nadan lokaci kadan malam sani yay shiru yana mamaki, sannan ya numfasa yace to shikenan tunda yace karya ne kibari gobe zan tasa keyarsa agaba muje makarantar domin na tabbatar da gaskiyan lamarin, tace to megida Allah ya kaimu, yace amin, sannan suka shiga wata firar,
washe gari da safe habib na gama shiryawa malam sani ya dauke bisa yamaya din shi sai school din, suna shiga yay parking su sauko ya tasa agaba sunufi office din principal, tunda ga waje yay sallama, principal yace yes ku shigo,
suna shigowa malam sani ya bashi hannu su gaisa, principal yace har yanzu wancen matsalar ce batakare ba? kai malam sani ya girgida yace ba ita bace, wannan wata matsalar ce kuma daban,
principal yace to inajinka meke faruwa? tsaf malam sani ya kwashe labarin da murja ta bashi ya fadawa principal, kai principal ya girgida yace babbar magana, barina aika akira for master dinsu muji koya abin yake,
from the experience of jamilu zazzau
WhatsApp 08104550703










No comments:
Write comments