Fateema Habeeb 11
na
Jamilu el hussain zazzau
dedicated to
Amina baba kaduna
washe gari habib na gama shirin school mahaifin shi ya dauke shi a mashin dinsa suka nufi makarantar,
suna shiga harabar school din ya samu waje ya faka mashin din ajikin wata bishiyar dogon yaro dake harabar school din, kai tsaye ya tasa habib agaba sunufi office din principal,
sallama yayi, principal yace bissimilah ku shigo, suna shigowa malam sani ya mika masa hannu su gaisa, sannan ya samu waje ya zauna, habib kuma na gefe yana tsaye,
duk irin halin da habib ke ciki malam sani ya kwashe ya fadawa principal, kadan principal ya dago kai ya kalli malam sani yace gaskiya yanzu ayyuka sun min yawa, saboda haka bazan iya sauraran wannan case din ba, amma yanzu barina hadaka da class master din su domin ya bincika ma,
kallo principal ya watso ma habib, yace jeka staff ka kira min malamin ajinku, da sauri habib yaje staff yakira malam ayuba su dawo tare,
kallon malam ayuba principal yayi, yace malam ayuba wannan bawan Allah da kake gani mahaifin yaron nanne, yazo yay min bayani cewa yaron shi na cikin damuwa matuka, kuma yana tunanin matsalar daga nan school take, saboda haka abinda nake so dakai katasa keyar yaron nan kuje ka bincike shi yafada maka abinda ke damun sa,
malam ayuba yace ok sir, kallon habib yayi yace wuce muje, habib na gaba malam ayuba na biye dashi sutafi class din su,
suna shiga students su mike duk su gasshe shi, yace ku zauna, kallon su yayi ya nuna habib yace kunsan wannan? duk su hada baki suce eh, yace ko akwai abinda ya hadashi da wani acikin ku? class kowa ya girgida kai yace aa,
mikewa monitan class din yayi, yace sir gaskiya akwai abinda ke damun shi kwana biyun nan, domin kullum ya shigo class baya kula kowa saide ya koma gefe yay ta tunani, ko walwala beyi da jama'a, kallo malam ayuba ya wurgo ma habib yace mu koma,
agaba ya taso shi su dawo office din principal, kallon su principal yayi yace ma malam ayuba ya akayi? dalla dalla malam ayuba yay mar bayani, principal ya kalli malam sani yace to megida kadai jiko?
malam sani yace eh naji, principal yace to zaka iya komawa idan ya sanar damu zamu nemeka muyima bayani, malam sani yace to madalla nagode, ya basu hannu su gaisa ya fito daga office din, kai tsaye yaje ya dauki mashin din sa yanufi gida,
mahaifin habib na fita principal yakira displine master yace kaga yaron nan akwai abinda ke damun sa, iyayen sa sunyi sunyi dashi yaki fada musu shine su taso keyar shi zuwa makaranta, muma nan mun tambaye shi yaki fada mana, saboda haka abinda nakeso dakai ka tasa shi agaba kuje saiya fada maka,
displine yace ok sir, fuska ya daure ya dakawa habib tsawa yace wuce muje, kai tsaye ya tasa habib zuwa office din shi, suna zuwa yasa habib yasa guiwar sa akasa shi kuma ya jawo kujerarsa ya zauna, sannan ya dauko wata dorina mai baki biyu ya ajiye kusa dashi,
hararan habib yayi, yace to zakai min bayani ko saina zaneka? dago kai habib yayi, yace sir nifa ba abinda ke damuna, barazana displine yay tama habib amma duk da haka baisa habib ya fadi komai ba, ganin haka yace mishi tashi mu koma,
kai tsaye ya taso shi su dawo office din principal, suna dawowa yace ma principal nima nayi nayi dashi yaki fadamin, kallon habib principal yayi, yace tunda kace babu abinda ke damunka tashi ka wuce class, jaka habib ya dauka kai tsaye ya wuce class din su,
zuwa yamma bayan an tashi daga makaranta principal su hadu da mahaifin habib a kasuwa yay mishi bayanin duk yadda su kayi da habib amma yaki fada musu, malam sani yace nagode ba damuwa, sukai sallama ya wuce,
from the experience of jamilu zazzau
WhatsApp 08104550703

No comments:
Write comments