Sunday, December 23, 2018

Home HUKUNCHIN GUDANAR DA GWAJE-GWAJAN LAFIYA KAFIN AURE
..
Kusan dukkan malamai a wannan zamani sun hadu a kan muhimmancin gudanar da gwaje-gwajen lafiya kafin aure don kaucewa wasu cututtukan da ke yin karan-tsaye ga dorewar aure, ko su sabbaba cuta ko naqasa ga ‘ya‘yan da za a haifa. Amma sun yi sa6ani game da wajabcinsa a kan wadanda ke son yin aure. Wasu malamai na ganin cewa Hukuma ko iyaye na iya wajabta gudanar da gwaje-gwajen lafiya a kan wadanda ke son yin aure, wasu malaman kuma na ganin kawai a bar mutane su za6i abin da suke so, ba tare da an wajabta masu ba.
Daga cikin masu ganin wajabcin gudanar da gwaje-gwajen lafiya kafin aure akwai: Muhammad Az-Zuhailiy, da Naasir Al-Maimaan, da Usaamah Al-Ashqar. Waxanda ke ganin halascin gudanar da gwaje-gwajen ba tare da wajabci ba sun hada da: Ibn Baaz, da Abdullah ibn Jebreen, da Abdulkareem Zaydaan, da Muhammad Ra’afat Uthmaan.
Allah ya shiryar da baki daya akan bin Sunnar Manzon Allah da tafarkin magabata na kwarai. Amin


No comments:
Write comments

Follow Admin On Twitter naimismo1
Join Our Newsletter