Abinda aka sani da aure a dukkan al’adu, yaruka da addinai shine namiji ya samu macen da yake, ya jawo hankalinta akan ta yarda suyi zaman
tare, ya biya haqqoqinta sannan mutane su shaida akan cewa ta zama matarsa saboda haka an halatta masa yin duk wasu abubuwa da kan iya gudana tsakanin mace da namiji. Yana daga cikin al’adun kuma cewa daga ranar ita macen zata bar gidansu ta koma gidan shi wanda ta zaba kuma ta aura a matsayin mijin nata.
Akan daura aure tare sharudda da yawa wandanda suka banbanta daga al’ada zuwa al’ada. A al’ada da addini na bahaushe, sharuddan da sukan biyo aure sun hada da samarda muhalli ko gurin zama ga matar, ciyar da ita, sama mata tufafi da kuma kula da lafiyarta.
By NAIMISMO1











No comments:
Write comments