Matsala #1
#Dacewa
Babbar matsala ta farko da ake samu a Rayuwar Aure shine idan ya kasance ka auri macen da bata dace da kai saboda daya daga cikin wadannan dalilai:
1. Macen da aka aura maka ita ba dan tana sonka ba, sai san anfi qarfinta a gidansu.
2. Macen da ka aura wacce ka tabbata dan abin duniya (kudi, suna, sarauta dss) ta aure ka.
3. Macen da kaima ba dan soyayya ka aure ta ba sai dan sha’awa, kyawunta, dangantakarta dss
4. Macen da kake tunanin ta aure ka ne kawai saboda bata da wani zabin.
5. Macen da bata gama yin hankali ba.
Wadannan da ma sauran dalilai da yawa wanda sukan kawo rashin dacewa tsakanin ma’aura suna kawo babbar matsala a Rayuwar Aure, wanda yawanci sai bayan anyi auren ake gane haka, lokacin da an riga an makara da ayi wani gyara akai. Saboda haka ina kira garemu ‘Yan Mata da Samari mu daure mu yaqi zuciyoyinmu mu auri masoyan da muka tabbatar zabin zuciyoyinmu ne kuma sun dace damu domin samun ingantacciyar Rayuwar Aure!
#Halayen Boye
Samari da ‘yan mata kowa yana iya qoqarinsa wajen ganin ya nunawa masoyinsa halin kirki a lokacin neman aure. Daga cikin matsalolin da ake samu a cikin Rayuwar Aure musamman a farko-farkonta shine a lokacin da ma’auratan suka fara gane halayen juna na gaskiya, wadanda a lokacin da zumar soyayya take dibarsu basu san dashi ba, hakan yakan kawo canji ga irin girma da mutuncin da ma’auratan zasu dinga bawa junansu, musamman idan akayi rashin sa’a daya daga cikinsu ya zamo yana da wani hali na qyama wanda da yake boyewa.
Shawarar da zan bayar anan shine sai mu dinga kulawa sosai a lokacin neman aure, samun kusanci da mutanen gidan masoyan namu ta hanyar qannenshi/ta da abokanshi/qawayenta zai taimaka wajen sanin wanda/muke tare dashi/ita da irin halayensu.
Gaskiya dokin qarfe, idan ka zamo mai gaskiya da halin qwarai to ba ka da tsoron komai a tare dakai!
#Matsala #3
#Mulkin Gida
A duk inda taro ya kai mutum biyu to ya kamata ace akwai shugaba wanda za’a iya cewa shine babba, haka ma a Rayuwar Aure dole a samu jagoran tafiya. Sanin kowa ne cewa a Addini da al’ada miji shine yake da mallakin gida, shi yasa ma ake kiransa da MAIGIDA.
Daga cikin matsalolin da akan samu daga wajen wadansu matan shine wai su baza su bari wani ya dinga nuna iko akansu ba, suna ganin idan suna bin maigida sahu da qafa kamar sun fado, za’a mayar da su kamar bayi! Wannan batu kuwa ba haka yake ba, dole ne mata kuyi haquri da yadda addini da al’ada ta tsara akan cewa maza sune shugabanni a Rayuwar Aure, ta haka ne kawai zaku iya cika haqqoqin auren da suke kanku; har ma ku zamo masu biyayya ga mazan auren naku, sai Allah ya baku lada.
Duk macen da take ganin ba zata iya yiwa namiji biyayya ba saboda tana ganin itama ta waye to lallai kuwa fitina baza ta taba qarewa a gidanta ba, irinsu ne zaka ga ko da Allah ya basu zuriyya to haka suma ‘ya’yan zasu taso irin halin mahaifiyar tasu. Saboda haka ina kira ga MATA IYAYEN GIDA da ku daure kuyi biyayya ga mazan aurenku dan samun ingantacciyar Rayuwar Aure, mu kuma maza muji tsoron Allah kada muyi amfani da wannan dama mu cutar dasu matan auren namu. Allah yasa mu dace baki daya.
BY NAIMISMO1











No comments:
Write comments