Thursday, December 6, 2018

Home MENENE SOYAYYA
..

Wannan tambaya an dad’e ana kaiwa da kawowa a kanta, masana da yawa sun tattauna domin ganin sun samar da ma’anarta domin a gane ta a kuma fahimce ta. Kamar haka:
Soyayya ita ce nuna ‘kauna daga 6angarori biyu na masu ‘kaunar juna (C.N.H.N.).
HARUNA USMAN
 bayyana cewa: ‘Soyayya ita ce ni’ima mafi d’aukaka da Allah Ya ba wa bayinsa. Soyayya ita ce zuciyoyi biyu a dun’kule su cure, su game cikin zuciya d’aya. Haka kuma soyayya ita ce rai biyu cikin jiki d’aya. Soyayya ita ce mutum biyu cikin mutum d’aya. Abin da ake nufi a nan shi ne, idan mutum ya so wani tsananin soyayya sai ya zama cewa koda yaushe cikin tunaninsa yake, ba ya damuwa da kowa sai shi, ba ya son ji da ganin kowa sai shi, wato kenan sun zama mutum d’aya cikin jiki biyu.’
Duk da abubuwan da muka ambata hakan ba zai sanya mu ce mun bayyana ha’ki’kanin ma’anar soyayya ba. Domin ita soyayya ba za a iya siffanta yadda take ba. Sai mutum ya shige ta, sannan zai san ta.BY NAIMISMO1

No comments:
Write comments

Follow Admin On Twitter naimismo1
Join Our Newsletter