Monday, December 10, 2018

Home RAYUWAR AURE
..
Bincike ne na musamman aka gudanar akan manyan abubuwan da suka shafi mata iyayen gida, wanda ake matukar bukatar irin shi musamman a dai dai irin wannan lokaci, an gabatar da shine a wara bita da aka yiwa mata zalla. Allah ya sakawa mawallafiyar wannan rubutu da alkhairi, malamata; Malama A’isha Ahmad Bello (Nuriyyah).
Ya ‘yan uwa bayan sallama irinta addinin Musulunci tare da fatan alkhairi, da yardar Allah SWT za ayi taqaitaccen bayani darasin ‘idaaratul Manzil’ ko ‘Home Management’ ko ‘Gudanar Da Harkokin Gida’, wanda ya qunshi abubuwa kamar haka:
1. Girki
2. Abinci
3. Tsafta
4. Zamantakewa
5. Kiwon Lafiya
Da fatan Allah SWT yayi mana jagora ya kuma sakwa malamanmu da alkhairi akan kokari da kuma jajircewa da suke yi wurin ganin sun fahimtar da al’umma ingatacciyar aqida ta Tauhidi da kuma doramu akan Sunnar Manzo SAW; da kuma wayar mana da kai akan lamarin rayuwa wanda ta hakan addininmu zai qara qarfafa da kuma samun karbuwa.
Gudanar Da Harkokin Gida
#Darasi Na 1
#Girki
Abinci ya zama dole a rayuwa, kulawa da shi yana gyara zamantakewa, rashin kulwa da shi kuma yana bata zamantakewa, dadin dadawa kuma Allah da ya haliccmu ya umarcemu da muci daga abubuwa masu dadi, Manzon Allah SAW ya tarbiyyantar damu a wurare da dama akan cin abinci, misalin hakan shine fadin Allah SWT:
“Yaku wadanda sukai imani kuci daga abubuwa masu dadi na abinda muka azurtaku dashi” (Baqara: 172)
Saboda haka ina fatan wannan taqaitaccen jawabi da zan gabatar zai zamarwa Uwargida ‘ci a hankali’ ko ‘ci ki qoshi kuma baki na marmari’ ko ‘hana mai gida fita’.
1. Iya Girki: Anan ana nufin iya sarrafa duk abinda ya sawwaqa zuwa abu mai dadi, da sanin da wanne za’a qare, da sanin irin tsawon lokacin da kowanne irin abinci ya kamata ya dauka. Misali dahuwar wake da shinkafa, ko dafa shinkafa da doya da dai sauransu.
2. Iya can-canza nau’ikan abinci: Hakan yana taimakawa wajen gujewa ginsa ko qosawa idan anan can-canza abinci daga wannan kalar zuwa wancan. Sannan zanso mutane su gane cewa ba wai sai an dafa abincin gidan sarki ba, duk abinda Allah ya hore dashi za ayi amfani.
3. Kula da yin abinci mai kyau, kuma mai tsafta: Abin misali anan shine mai gida Allah ya hore masa ya kawo shinkafa baqa kuma yace yana son ayi masa tuwon shinkafa, kinga idan tuwo ne sai ki jiqa ta tunda wuri, hakan zai taimaka wurin sanyawa shinkafar tayi haske wanda zaifi bada sha’awar aci. Kwanukan cin abincin suma su zamo a tsaftace, hakan zai taimaka wajen jawo hankalin mai cin abincin, wannan kuwa zai kasance anyi da wurwuri ba sai lokacin da za’a ci abincin za’a wanke ba.
4. Rashin bata gida: Ya kamata uwargida ta kula sosai yayin da take girki kada ta bata gidan ko rumfar girkin ko kuma kayan da take aiki dasu a lokacin girkin. Duk sanda take aiki akan wani abu wanda yake buqatar a zubar da shara daga gareshi to sai tara sharar waje daya, sannan kuma ta debe ta da zarar ta gama da wannan abin ba wai sai ta gama girkin gaba daya ba kafin ta fara gyaran gida. Hakan nan ya kamata uwargida ta kula da jikinta wajen yin girkin, ba dole ne sai jiki ya baci ba don ana girki, matan arewa sun kasance suna zama cikin datti wai saboda su suna girki kuma wannan ba dai dai bane. Dole uwargida ta tabbatar tayi amfani da duk wani abu da zai rage mata sauqin aiki a lokacin da take yin girki (kamar su wuqa mai kaifi, tsumman goge-goge, qyallen sauke tukunya, abin kwashe shara dss).
5. Kulawa da lafiyar jiki lokacin girki: Ana son uwargida tayi taka-tsantsan a lokacin yin girki wajen kula da lafiyar jikinta daga wuqa, wuta, abu mai nauyi da duk wani abu dai zai iya kawo barazana ga lafiyarta.
6. Kulawa da yara da sauran mutanen gida yayin girki: Yakamata uwargida ta kula da zirga-zirgar yara da sauran mutanen gida yayin da take aikin girki, kada ta dinga ajiye abubuwa a ko ina inda yara zasu iya wasa dashi ko kuma a inda manya zasu iyayin tuntube dashi ko su taka.
7. Gama girki akan lokaci: Yakamata uwargida ta kula da lokaci wajen kammala abinci, domin yunwa bala’ice, gama girki da wuri yana daya daga cikin abubuwan da suke jan hankalin mai gida yaso abincin kuma ya qara masa qarfin gwiwar kawo cefane mai dadi, musamman tunda akwai kwanuka masu riqe zafi yanzu (flasks).
8. Gujewa barnatar da abinci da kuma dafa isashshen abin shima abin kulawa ne.



Dukkan Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Halittu, tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad tareda iyalansa da wadanda suka bi tafarkinsa har izuwa tashin Alkiyama.
Yauma gamu munda dawo muku da cigaban karantunmu na Gudanar Da Harkokin Gida (zama na biyu), wanda da yardar Allah zai kunshi darussa guda biyar kamar haka:
1. Ingantacciyar lafiya tana samuwane ta hanyar ingataccen abinci.
2. Zaman aure zaman Ibada ne ba zaman kwatar 'yanciba.
3. Mallakar miji watau (matakai).
4. Kishi kumallon mata.
5. Rainon yara.
Da yardar Allah za'a daukesu daya bayan daya aji bayani akansu.
Gudanar Da Harkokin Gida (Zama Na Biyu)

#Ana Samun Igantacciyar Lafiyane Ta Hanyar Ingantaccen Abinci
Tabbas kulawa da abinci ya zama dole kuma sanin hakan dolene da lafiyayyen abinci ga lafiyayyen mutum dolene ya hada manyan sinadirai na gina jiki kamar haka: -
1. Protein : Wannan sinadarin gina jiki anfi samunsane a jikin dabbobi ko tsuntsaye kamar su nama, kifi, nono, madara, kwai, ko ta hanyar tsiro ko shuka kamar dankali domin wadannan suna taimakawa wajen gina gababuwa da karfafasu.
2. Carbohydrate : Wadannan ana samunsu ta hanayar shinkafa, alkama, Masara da dai sauransu. Suna Haifar da karfi da lafiya da kuma haifar da zufa watau cuta zai dinga fita ta zufa.
3. Fat/Oil: Watau duk wani abinci mai maiko suma suna da nasu anfanin a jiki, kamar manja, mangyada da dai sauransu.
4. Vitamin/Minerals & Salt: Ana samunsu ta hanyar kayan marmari, ganyayyaki wasu sai an dafa wasu kuma ba sai an dafaba. Koda yake a wata sa'in kowani mutum yana da abinda ya dace dashi musamman idan aka samu lalura na ciwo, wannan kuma sai mutum yabi shawarar likita, amma idan ba haka ba ana bukatar canzawa saboda kowanne ya dinga aikinsa a inda ya kama.
Kuma kamar yadda bukatuwa ta banbanta ta fuskar girma, yara sune mafi bukatuwa akan wanda ya manyanta saboda haka sai mu gyara, don zakaga munci nama uku-hudu koma fiye da haka amma yara sai a ficincina musu. Haka kuma lokacin samartaka akwai bukatar hakan don samun karfin gabbai da dai sauransu.
Hakan yana nufin a duk lokacin da za’a dafa abinci sai a kula da irin abubuwan da za’a sa a ciki da kuma irin abincin shi kansa. Idan da hali anaso a qalla aci kowanne nau’i wadannan sinadarai a kowacce rana.


A taqaice tsafta kalma ce da take nufin kawar da qzanta ko dauda ko datti da kuma mummunan wari ko kawar da duk wni abinda baya da kyawun gani. Don haka tsafta ta shafi abubuwa kamar haka:


1. Jiki: Idan aka ce tsaftar jiki ana nufin wanke gangar jiki da ruwa da sabulu ko abinda zai tsaya a matsayinsu su wanda zai taimaka wajen kawar da dauda da wari.
Haka kuma akwai wata hanya da mace zata kawar da dauda daga jikinta ba tare da amfani da ruwa da sabulu ba, wannan hanyar ko ana kiranta da Dukhan wato hayaqi, ana amfani da itacen farar qaya ko magarya.
Yadda ake yin sa kuwa shine mace zata rufe dukkan jikinta da bargo a lokacin da ta tube ta zauna ta ware qafafafunta alhali wannan itacen yana qarqashinta, yana bada hayaqi a hankali, shi itacen za’a dan jikashi da ruwa sannan asa a cikin wuta, dalilin jiqawa shine domin kada ya haifar da zafi sai dai hayaqi. Yana matuqar gyarawa mace jiki da matancinta domin yana mayar da mace yarinya kuma ya ma fi wanka tsaftace jiki. Amma kafin mace ta shiga cikin bargon zata shafe jikinta da KARKAR (wani mai ne da ake hadawa in babu sai a shaf man zaitun)
<Dan Allah idan akwai wacce tasan yadda akeyin wannan hayaqi sosai sai tayi mana qarin bayani dan mu qaru>
GA YADDA AKE HADA KARKAR
Za’a samu bawon lemon zaqi a jiqa ya kwana a ruwa tare da kanunfari sai a zuba a tukunya mai tsafta tare da man simsim (Ridi) ko man zaitun ko man kwakwa ko man gyada tare da wuta mara qarfi yana dahuwa har ya tafasa za’a sauke idan aka karya kanumfari aka ga ya karye to yayi.



2. Baki: Daga cikin tsaftar jiki akwai tsaftace baki, aqalla awanke baki da maganin wanke baki ko aswaki sau biyu ko uku a kullum, kuma dadi akan haka ya kamata mace ta riqa amfani da alawa (sweet) mai dadi mai bada daddadan qamshi a duk lokacin da zata kusanci mijinta.



3. Aski: Anan ana nufin aske wurin da suke tara gashi, kamar hammata, mara da sauransu, wanda dama yana cikin fitra guda biyar da Manzon Allah S.A.W ya fada, aqalla mace ta tabbatar tana yin wannan aski duk bayan kwana arba’in.



4. Qumba (Farce): Shi ma yanke qumba yana daya daga cikin fitra guda biyar wanda shi ma jigo ne sosai a cikin duniyar tsafta. Idan so samu ne ya kamata a qalla a yanke qumba a cikin kowanne sati, amma sai kaga wata farcenta kamar ta gwagwgwan biri.



5. Kaushi: ya kamata uwar gida ta kula da kaushin qafa tabi hanyoyin da zata bi wurin kawar dashi ko magani ko wankewa ko zuwa saloon dss. Wata hanya da mace zata iyayin maganin kaushin qafa shine ta samu ruwan zafi ba sosai ba ta zuba shampoo a ciki sai ta saka qafafauwa a qalla minti goma sai ta goge qafar da dutsen goge qafa sai ta fitar ta shafa mai kamar basilin ko zaitun sai ta sanya qafar a cikin leda kamar minti biyar amma ba wai sai zata tafi unguwa ba

BY NAIMISMO1
No comments:
Write comments

Follow Admin On Twitter naimismo1
Join Our Newsletter