Monday, December 24, 2018

Home *😳WATA SABUWAR HANYAR YIWA MATA FYADE,* *👰🏻MATA KUYI HATTARA.😳*
..
Dangane da wani rahoto na yan'sanda, wata ta tsinci kanta a yayin da maza 5 suka yi mata fyade suka yarda ita a tashar mota, koda yake bata iya tunawa da abin da ya faru ba, Dangane da binciken likitoci sunce anyi mata fyadenne akai_akai(layi) kuma dangane da binciken nasu sun gane akwai sinadarin ROHYPNOL a jininta.                   ROHYPNOL_sabuwar hanya ce ta amfani dashi wajen yiwa mata fyade. Hakika wata karamar kwaya ce wadda masu yiwa mata fyade suke amfani da ita a wajen bukukuwa. Ita dai wannan kwaya tanasa hankali ya gushe koda anyiwa mace fyade bazata sami ciki ba. Mummunan labari akan kwayar shine ita illarta bawai na lokaci neba tana zama dundundun a jikin dan adam. Duk wata mace da take shan wannan kwayar bazata dauki cikiba, wannan kwayar ana zaluntar mata ta hanyar saka musu ita cikin abinsha kamar lemo, idan aka sawa mace to a wannan daren bazata iya tunawa da abin daya faruba.       Kwayar ROHYPNOL tana narkewa acikin abinsha da sauri kuma bata da dandano bata chanja launi acikin lemo, shi yasa ganeta  yana da wuya. Ita wannan kwaya ana samunta a makarantun kiwon lafiyar dabbobi da kuma jami'o'in kula da lafiya. Tana da saukin samu kuma a halin yanzu da muke ciki a jami'o'in da muke dasu aqasarnan ta zama ruwan dare, abin mamaki shine akwai ta yanar gizo_gizo masu ilimantar da mutane yadda ake amfani da wannan kwayar.                 Mata kuyi hattara idan kun fita da samarinku karku yarda ku bar abinshanku kan tebur kuje wata sabgar. ko kuma a wajen sha'ani ku sayi naku abinshan, kuma ku tabbatar da cewa abinsha na kwalba ko gwangwani a rufe yake kafin amfani dashi,kar ku ko dan dana abinshan wani.      Akwai rahoto a NIGERIA abinshan mata ana saka mishi ROHYPNOL a wajen biki.         GARGADI ga maza ku sanar da mata dangi da kuma qawayenku, kuma ku tuna cewa kuna da 'yan'uwa mata ko 'ya'yanku.              LABARI mai amfani yana bukatar yadawa, kada ka/ki qi tura wannan sakon. An turo mini da wannan sakon ta harshen turanci ne naga ya kamata na fassara zuwa harshen HAUSA domin yan uwa su qaru dashi. Dan ALLAH ku tura da wannan sakon saboda ni da ku duka mu cechi RAYUWAR matanmu da kuma gaya musu karsu yarda a zalunce su.
No comments:
Write comments

Follow Admin On Twitter naimismo1
Join Our Newsletter