Tuesday, January 29, 2019

RIGAKAFIN-POLIO DA QALUBALENSA.
#RIGAKAFIN-POLIO DA QALUBALENSA.
Rigakafin polio haqiqa yana da matuqar muhimmanci, domin samar da garkuwa jiki a tsakanin mutane, musamman yara kananu.
Ilimin lafiya da cututtuka ya tabbatarda Wanzuwar kwayoyin cutar dake kawo wannan cuta(polio virus), bugu da kari kuma rigakafin bincike ya tabbatarda Ansami Gagarumar nasara kauda kaso mai yawa na wannan cuta.
#MEYAKE KAWO CECE-KUCE DA RIGINGIMU TSAKANI MA'AIKATAN POLIO DA MUTANEN GARI?
1.Na farko shine rashin neman izinin Iyaye yayinda za'a yi wa 'yayansu, A gaskiya yanada daga cikin Manya-Manyan Dokokin Aikin likitanci neman izinin (CONSENT) Mara lafiya ko me neman kulawa (client) kafin Ayi masa magani ko wani abu dake da tasiri ga lafiyarsa.
Jami'an Polio masu bi gida-gida basa Lura da wannan Doka, sukan tare yara akan hanya batare da sani ko izini na iyayensuba suyi masu Allura ko digon baki na polio..
Hakan zai iya haifar da matsaloli kamar haka:-
1.Fadace- fadace tsakanin jami'an da mutunen unguwa.
2.Zai sa mutane Sudinga Kyamatar riga kafin su dinga zargin ko akwai wata Qullalliya a qasa.
3.Akwai wasu yara da ba'a baiwa Allurar ko digon baki, wadanda Garkuwar jikinsu bata da kwari (immunosuppressed) ko kuma jikinsu bai karbar rigakafi (Allergy), ko kuma yaran da akabaiwa a Qasa da wata biyu baya, da kuma yara marasa lafiya (za'a jira su warke).
Idan aka tare yaro a waje aka diga saboda wannan dalili yazama WAJIBI neman izinin iyaye kafi ayiwa 'ya'yansu.
#HANYOYIN MAGANCE WANNAN MATSALA:
1.Asamarwa ko wanne yaro kati daya Qunshi kowanne nau'i na Allurar rigakafi, kamar yadda W.H.O ta tsara, wanda za'a dinga cikewa duk lokacinda akayi.
2. A daina bin gida-gida, asamar da cibiya guda daya akowacce unguwa ta rigakafi ko asibiti mafi kusa.
3. A dinga nema izinin iyaye kafin kowanne rigakafi. (CONSENT).
4.A daina tirsasawa Al'umma, acigab da wayarda kan mutane.
Tirsasawa mutane yin rigakafi yasabawa kudin tsarin mulki da tsarin aikin likitanci.
#Umar sa'ad
Level 300 student nurse.
School of nursing kano
Read More»

MAI SABAWA IYAYE KA KUKA DA KANKA
MAI SABAWA IYAYE KA KUKA DA KANKA
Duk wanda yaga matsala tayi masa yawa ya bincika alakarsa da iyayansa.
Duk wanda yaga baya samun Nasara a duk abinda yasa gaba ya duba alaka da iyayansa .
Duk wanda baya jin dadin rayuwar sa, ya bincika yadda yake zaune da iyayansa
Duk wanda yaga makiya suna rinjaye a kansa, ya tintibi zaman sa da Iyayansa.
Sabawa iyaye yana jawo dukkan matsala a rayuwa
1 Sa iyaye kuka, saboda bakin ciki
2 Yiwa iyaye tsawa, ko hantara ko tsaki ko gunguni
3 Kosawa da iyaye da gajiya da su ko tsanarsu
4 Daurewa iyaye fuska ko sha musu kunu
5 Yiwa iyaye kallon raini da hadarin kaji
6 Yiwa iyaye tsiwa, da daga murya akan su
7 Kushe iyaye, da daukar su gidadawa.
8 Kauda kai, idan iyaye suna magana .
9 Fifita mata akan iyaye
10 Fifita Abokai akan iyaye
11 Jawowa iyaye matsaloli da rigingimu
12 Gulmar iyaye
13 Zagin iyaye ko jawo musu zagi
14 Damun kiyaye da kade kade da wake wake
15 Rashin shawara da iyaye
16 Kauracewa iyaye
17 Tsagalgalewa iyaye da rashin kunya
18 Iyaye su dinka tsoran dan su
19 Kin amfani da sunan iyaye
20 Dukkan iyaye da gajiya da su
21 Fatan mutuwar su
22 Yi musu gori dan kayi wani abu.
23 Boyewa iyaye samu, ko wadata,
24 yiwa iyaye karya
25 Karyata iyaye
26 Yiwa iyaye sata,
27 YI musu gori
28 YI musu musu,
29 Rashin yi musu addua
30 Barin iyaye cikin kunci da wahala.
Allah kasa mu gama da iyayanmu lafiya, kayi musu rahma kamar yadda suka yi mana tarbiyya tun muna Yara.
Dangirman Allah katurawa group 3 shiyakenuni daka sanarda wani abunda yan uwa abunda kasani. DUNIYA MAKARANTA
Duk wanda yaga matsala tayi masa yawa ya bincika alakarsa da iyayansa.
Duk wanda yaga baya samun Nasara a duk abinda yasa gaba ya duba alaka da iyayansa .
Duk wanda baya jin dadin rayuwar sa, ya bincika yadda yake zaune da iyayansa
Duk wanda yaga makiya suna rinjaye a kansa, ya tintibi zaman sa da Iyayansa.
Sabawa iyaye yana jawo dukkan matsala a rayuwa
1 Sa iyaye kuka, saboda bakin ciki
2 Yiwa iyaye tsawa, ko hantara ko tsaki ko gunguni
3 Kosawa da iyaye da gajiya da su ko tsanarsu
4 Daurewa iyaye fuska ko sha musu kunu
5 Yiwa iyaye kallon raini da hadarin kaji
6 Yiwa iyaye tsiwa, da daga murya akan su
7 Kushe iyaye, da daukar su gidadawa.
8 Kauda kai, idan iyaye suna magana .
9 Fifita mata akan iyaye
10 Fifita Abokai akan iyaye
11 Jawowa iyaye matsaloli da rigingimu
12 Gulmar iyaye
13 Zagin iyaye ko jawo musu zagi
14 Damun kiyaye da kade kade da wake wake
15 Rashin shawara da iyaye
16 Kauracewa iyaye
17 Tsagalgalewa iyaye da rashin kunya
18 Iyaye su dinka tsoran dan su
19 Kin amfani da sunan iyaye
20 Dukkan iyaye da gajiya da su
21 Fatan mutuwar su
22 Yi musu gori dan kayi wani abu.
23 Boyewa iyaye samu, ko wadata,
24 yiwa iyaye karya
25 Karyata iyaye
26 Yiwa iyaye sata,
27 YI musu gori
28 YI musu musu,
29 Rashin yi musu addua
30 Barin iyaye cikin kunci da wahala.
Allah kasa mu gama da iyayanmu lafiya, kayi musu rahma kamar yadda suka yi mana tarbiyya tun muna Yara.
Dangirman Allah katurawa group 3 shiyakenuni daka sanarda wani abunda yan uwa abunda kasani. DUNIYA MAKARANTA
Read More»

-NAZARIN WAQAR MAI ZAMANI TA NURA M INUWA
-NAZARIN WAQAR MAI ZAMANI TA NURA M INUWA-
Editing (Shazali A Salisu Duba)
-AMSHI-
Mai Zamani Allah Shine Zamani, Asalin Zance Bawa Bashida Zamani, Hudubar Shedan Itace Muka Kama Yan Zamani.
* Taqakama Da Kudi Mai Yi Baya Dorewa (Mai Zamani)
*Shiko Mai Qarya Zance Bai Gamsarwa Mai (Zamanii)
* Daukakar Zamani Tauraro Haskawa (Mai Zamani)
* Baiwa A Ciki Allah Ne Mai Bayarwa Yan Zamani
~
* Ita Dai Dama Sai Da Ita Aka Damawa (Mai Zamani)
* Inta Sufce Dawuya Tai Dawowa (Mai Zamani)
* Zo Shuka Iri Mai Kyau Dan Kai Girbewa (Mai Zamani)
* Kada Kai 'Barna Gyaranta Ya Zamma Wuya, Kana Gani
~
* Mai Furen Juji Baya Sha'awar Tsinka (Mai Zamani)
* Ruwan Bazara Mai Kama Da Yawan Malka (Mai Zamani)
* Matsayi Ka Bukata Allahu Ya Doraka (Mai Zamani)
* Shi In Yaima Ba Mai Iya Kar6ewa Da Magani
~
* Ganga Da Zuga Su Kunne Suka Hurewa (Mai Zamani)
* Zari Da Zalama Suka Jawo Shakewa (Mai Zamani)
* Samu Da Wadata Kansu Zakai Holewa (Mai Zamani)
* Don Tuwon Gobe Aka Wanke Tukunya, Buri Adani
~
* A Wurin Magana Da 'Da Tsaftace Harshenka (Mai Zamani)
* Zaima Wahala Iya Gane Masoyinka (Mai Zamani)
* Dan Wanni Abun, Idanu Basa Nunenka (Mai Zamani)
* Girman Kai Kar Da Kayarda Yazo Yanada Maka Rawani
~
* Jita-jita Ashe Batada Dadin Yadawa (Mai Zamani)
* Wani Yayi Amai Karshe Yai Lashewa (Mai Zamani)
* In Sunyi Yabonka Yi Shiru Ba Kushewa (Mai Zamani)
* In Sun Jefo Kunnenka Ka Toshe Daina Martani...
-Mai Zamani Allah Shi Ne Zamaniii, Asalin Zance Bawa Bashida Zamaniii, Hudubar Shedan Itace Muka Kama Yan Zamani-
Jinjina Ga Wannan Fasihin Mawaki Wato (NURA M INUWA) Tabbas Wannan Waqar Tana Dauke Da Saqo Mai Kyau Qwarai Da Gaske Idan Mukayi Duba Da Irin Zantukan Da Yayi Amfani Da Su Masu Dauke Da Tauhidi, Ya Yarda Cewa Allah Shine Yake Da Iko Akan Komai Domin Shine Yake Ni'imtawa Bawansa Ni'imarsa A Lokacin Da Yaso Kuma Ga Wanda Yaso.
Babu Shakka Na Jinjina Masa Tare Da Yabawa Qwarai Da Gaske, Allah Yakara Basira Da Ilimi Mai Amfani
29-01-2019
Read More»
Sunday, January 27, 2019

Hattara dai Matasa!!!!
Hattara dai Matasa!!!!!!
Akwai rayuwa bayan zabe. Kar ka bari harkar siyasa ta hada ka rigima da wani. Kayi siyasa mai tsafta cikin mutunci da girmama juna. Ka girmama ra'ayin wanin ka shima ya girmama naka.
Ta'addanci da bangar siyasa bata dace da duk mutum mai hankali ba, kar ka bari wani dan siyasa yayi amfani da kai wajen tayar da tarzoma a cikin al'umma. Kar kayi zaton 'yan siyasa suna amfani da kai ne don ci gaban kasar ka, suna amfani da kai ne su mulke ka don jin dadin rayuwar su.
Sako daga:
Kungiyar Matasa Masu Rajin kare hakkin Matasa da Al'umma. ( MMA)
Posted by NAIMISMO1
Read More»
Saturday, January 19, 2019

Me Yakamata Nayi Kafin Ranar Jarrabawar Jamb?
Me Yakamata Nayi Kafin Ranar Jarrabawar Jamb?
AMFANIN YIN JAMB A COMPUTER
Samun Sakamako cikin kankanin lokaci.
Magance matsalar rashin samun cikakken sakamako,
Magance satar jarabawa.
ME KUMA YA KAMATA NAYI KAFIN RANAR JARABAWA?
1. Ka tabbatar Registration Slip din ka yana hannun ka sannan kayi kwafi din sakamar guda biyu a hannunka.
2. Ka tabbatar kayi gwajin jarabawar a na’ura mai kwakwalwa musamman idan baka da kwarewa akan Computer.
3. Ka ziyarci cibiyar da aka tura ka domin zana jarabawa ka tabbatar da yankin da take yanda ranar jarabawa zaka iya kai kanka kai tsaye ba tare da kwatance ba don gudin makara.
4. Ka tabbatar da Rana da kwanan wata da aka saka zaka yi jarabawar da lambar kujerar da zaka zauna.
4. Ka tabbatar da lokacin da safe ne ko da yamma kuma karfe nawa ne? mafi kyau ka kasance a inda za kayi jarabawa awa daya kafin lokacin jarabawar domin tantacewa.
Zamu cigaba.
Basheer Sharfadi
Social Media Strategists.
January 2019.
#Jamb
Read More»
Thursday, January 17, 2019

Ina Son Zanyi Jarrabawar Jamb, Shin Me Yakamata Nayi? Cigaba
Ina Son Zanyi Jarrabawar Jamb, Shin Me Yakamata Nayi?
Cigaba..
*JAMB 2018/2019*
Yanzu kuma yar uwa da dan uwa bara mu kutsa cikin batun Jarabawar Jamb din ta wannan shekara wadda muke magana akan ta.
*INA SON ZAN YI JARABAWAR JAMB SHIN ME YAKAMATA NAYI?*
Dalibin da yake son zana jarabawar jamb a wannan shekara 2018 zai bi matakai kamar haka:
Dalibi ya mallaki email account (wanda yake yin amfani dashi) sannan ya bude Jamb Profile wanda ake budewa a www.jamb.org.ng sannan yayi printing din (jamb profile details) bayanan profile din nasa wanda zasu turo masa ta email din sa.
Zai tafi da copy Jamb Profile din banki sannan ya biya kudin, ka tabbatar ka rike tailer din da ka biya gudun samun bacin rana, bankin zasu baka (Jamb Pin) wasu bankunan sukance ka koma washe gari bayan ka biya, sannan baya ga wannan hanyar ma ana iya biya online idan ka karbi wannan Pin din dashi zaka je cibiyoyin da ake yin jarabawar Jamb din domin suyi maka register anan za’a cike maka courses din da kake son yi, ko wane dalibi sai yayi jarabawar English sai kuma subject guda uku da suka shafi bangaren da yake so yayi karatu akai, daga nan zasu baka takarda mai kunshe da bayanan register din daka yi sannan su baka Plate mai kunshi da bayanai akan jarabawar jamb da kuma bangarorin da ake sa ran yin tambayoyi akai da sauran bayanai, sannan za’a baka littafin da zaka karanta wanda jamb suke bayarwa duk shekara a shekarar da ta gabata an bayar da littafi mai suna INDEPENDENCE wallafar Sarah Ladipo Manyinka.
Daga nan sai ka jira su fara aiko da sakon inda zakayi jarrabawa da lokaci da lambar mazauni wanda a turance ake kiran wannan takarda da (Slip).
Akwai wuraren da Jamb ta amince a bana wanda zakaje kayi register kuma za suyi maka komai da komai.
Daga nan ya rage na dalibi yaje ya koyi yadda ake sarrafa computer wajen yin jarabawar sannan ya dage da karatu da yin addu’ar samun nasara.
Gobe idan Allah ya kaimu zamu tashi akan *Computer Practice Test (Jamb CBT)*
Basheer Sharfadi
Social Media Strategist.
17-01-2019.
#Jamb
Read More»

WASIKA ZUWA GA MATASA MASU AIKATA ISTIMNA'I
WASIKA ZUWA GA MATASA MASU AIKATA ISTIMNA'I
ma'anar ISTIMNA'I shine= fitar da mani ko sha'awa da gangan ta hanyar da bata dace ba.
Matasa Maza da mata, suna neman taimako akan illolin da suke samu a jikunansu sakamakon Istimna'i wato Masturbation. An kawo hujjoji
gamsassu daga Al-Qur'ani da Sunnar Ma'aikin Allah (saw) da fatawoyin Amintattun Malamai duk akan HARAMCIN ISTIMNA'I, Amma duk da haka wasu matasan basu yarda sun dena ba.
Wasu kuwa sunji tsoron ALLAH sun riga sun dena, bubban dalilin da yake janyo musu afkawa cikin
wannan bala'in shine :
1. Kallon Fina-finan batsa.
2. Shiga shafukan internet na batsa.
3. Yin zantukan batsa tsakanin
saurayi da budurwa.
4. Kusantar zina ta hanyar kallo da
shafa, ko zance da dai sauransu.
Wasu kuma suna aikata hakan ne
dan gudun afkawa ZINA, basu san cewa shi d'inma ZINAR bane!!
Idan kun Qi bari domin Allah, to ku dubi irin illolin da yake haifar muku ajikinku mana!!!
1. MUTUWAR IDANU.
2. MUTUWAR AL'AURA.
3. CIWON BAYA.
4. BUGAWAR QIRJI.
5. RIKICEWAR TUNANI.
6. YAWAN MANTUWA.
7. KARANCIN 'YA'YAN MANIYYI.
8. SAURIN INZALI.
9. SHAFAR ALJANU, ETC.
Wad'annan 'yan kad'an ne daga cikin Matsalolin da ISTIMNA'I yake haifarwa. kuma duk wanda bai tuba ya dena ba, idan ya mutu a haka zai je ya tarar da hisabi.
DAN GIRMAN ALLAH!! Matasa ku kiyayi zina da duk dangoginta, ku Qaurace ma duk wani abinda zai rinQa motsa muku sha'awa, idan
da hali kuje kuyi aure, idan kuma babu hali, to ku yawaita azumi.
ALLAH YA SAUWAQE.
Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,
DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM WHATSAPP, da sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.
Manzon Allah (s.a.w) yace: "WALLAHI IDAN ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA
DALILINKA, YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAQUMMA"
Wani mutum yazo wajen manzon Allah S. A.W. ya ce: Yah-Manzon-rahma zan tambaye ka rayuwar duniya da ta lahira.
1. Yah Manzon Allah ina son in zama mafi sani a cikin mutane?
AMSA
Sai ya ce "Ka ji tsoron Allah ka bi dokokin Sa."
2. Ina son in zama mafi arziQi a cikin mutane?
AMSA
sai ya ce "Ka zama mai wadatar zuci."
3. Ina son na zama Wanda yafi kowa acikin mutane?
AMSA
Sai ya ce "Ka zama mai amfanarwa."
4. Menene zai kare ni daga wuta?
AMSA
Sai ya ce "Ka zama mai yawan yin Azumi."
5. Ina so in zama mafi adalci a cikin mutane?
AMSA
Sai ya ce "Ka so ma d'an uwanka abin da ka ke soma kanka."
6. Ina son in zama mafi amfanin mutane a wajen Allah?
AMSA
Sai ya ce "Ka yawaita tuna Allah."
7. Ina son imanina ya zama ingantacce?
AMSA.
Sai ya ce "Ka gyara halayen ka."
8. Menene yake huce fushin Allah (S.W.T.)?
AMSA
Sai ya ce "Ba da zakka a boye da kyautata ma 'yan uwa."
9. Wani zunubi yafi muni awajen Allah?
AMSA
Sai ya ce "Mummunar hali shine rowa"
10. Ina so in zama mafi biyayya ga Allah?
AMSA
Sai ya ce "Ka bi umurnin Allah za ka zama mafi rinjaye a wurin Allah."
YA ALLAH Ka sa mu gama da Duniya lafiya.
INA ROQON MAI KARATU dan GIRMAN ALLAH kayi Qokari ka tura wani group d'in domin tunasarwa....
Read More»
Wednesday, January 16, 2019

Hukumar Hisbah Ta Fasa Kwalabe Sama Da Dubu Sittin Na Giya A Kano
Hukumar Hisbah Ta Fasa Kwalabe Sama Da Dubu Sittin Na Giya A Kano
Daga Anas Saminu Ja'en
Mai girma shugaban ƙaramar hukumar Gwale Hon. Dakta Khalid Ishak Ɗiso da jama'ar sa tare da haɗin gwiwar hukumar Hisba ƙarƙashin jagorancin shugaban ta na ƙaramar hukumar Gwale Yahaya Bala Sabon Sara, suka jagoranci farfasa kwalaban Giya waɗanda aka kama a lokacin da aka shigo dasu cikin jama'a ake ƙoƙarin sayarwa wanda kimanin ta ya kai dubu sittin (60000).
Kowa ya san a jihar Kano dai ana amfani da dokar shari'ar Musulunci wanda ta hana shigowa ko shan kayan barasa, a lokacin da shugaban ƙaramar hukumar ke jawabi ya ce ma'aikatan Hisba kuma za su ƙara ƙoƙari tare da yaƙi da duk wani mai ta'ammali da kayan maye ba giya ba kawai wajen ganin an bi wannan doka a faɗin jihar a wannan shekarar da aka shiga.
Taron fasa giyar ya samu halartar manyan mutane wanda suka haɗar da wakilin gwamna da wakilin hakimin da mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Hon. Ado Gambo Ja'en, sakataran ƙaramar hukuma Hon. Abdullahi Sarki tare da manyan Malam addinin Musulunci ƴan takarkarun majalissun tarayya dana jihar na ƙaramar hakumar Hon. Abdullahi Lawan Kenken da Hon. Usman Zubairu da sauran masu faɗa aji daga ciki da wajan ƙaramar hukumar Gwale da kuma dubban al'ummar gari, kuma an gudanar da wannan fasa giyar a hauren yara kusa da helkwatar ƴan sanda ta ɗaya wato Zone 1 dake jihar Kano.
Read More»

Mecece Jarrabawar Jamb? Da Kuma Tarihinta?
Mecece Jarrabawar Jamb? Da Kuma Tarihinta?
*Gabatarwa:*
Assalamu Alaikum warahmatullahi wa barakatuhu, wannan takardar ce da zata kunshi muhimman bayanai dangane da Jarabawar Jamb tun daga ma’anar ta, tarihin ta, da Sharudanta da kuma yadda ake yinta, me kuma ake bukata idan za’ayi ta? sannan me yasa ake yin ta, da yadda ake samun nasara a jamb din.
Cibiyar Sharfadi.com itace ta shirya wannan takarda domin amfanar daliban da zasu zana jarabawar a wannan karon da wadanda zasu zo nan gaba domin dai ganin an gudu tare an kuma tsira tare.
Cibiyar ta zabi harshen Hausa domin yin rubutun akai domin ‘yan uwan mu hausawa masu karancin kwarewa a yaren turanci su samu damar amfana da ita, kuma an yi takardar ne domin amfanin su, masana sun hadu akan irin yadda harshen uwa yake da matukar tasiri wajen isar da sako don haka muka ga mafi dacewa kuma mafi taimako ga dalibai na yankin da muke ciki shine muyi amfani da harshen hausa domin isar da sakon cikin kankanin lokaci, sai ku biyo mu.
*Sharadi:*
Ba’a yarda wani ko wata tayi amfani da wannan takarda ko tayi kwafi dinta ba tare da iznin marubucin ba.
*Mecece Jarabawar Jamb?*
Jarabawar Jamb Jarabawa ce da dalibai ke yinta domin neman samun gurbin karatu a jimi’o’I da kwalejoji da kuma makarantun kimiya da fasaha wadda wata hukuma da ake kira da JOINT ADDMISSION AND MATRICULATION BORD (JAMB) take shiryawa kuma ake kiran jarabawar da sunan hukumar ana yin ta sau daya (1) a shekara akwai adadin makin da ko wace makaranta take bukatar mai neman shigar ta ya samu.
Jarabawar tana da wasu ka’idoji na sai mutum ya na da sakamakon jarabawar karshe ma’ana ya gama Sakandire ko kuma yana Shekarar karshe wadanda ake kiran su da WAITING RESULT a turance ma’ana wadanda ke zaman tsammanin jiran ganin sakamakon jarabawar su suma ba’a barsu a baya ba sukan zana wannan jarabawar tare da fatan in an dace sai ayi tazarce kai tsaye zuwa makarantun gaba da sakandiren.
*Tarihin Jamb*
A shekarar 1974 lokacin a kasar nan ana da a jami’o’I guda bakwai (7) kuma ko wacce tana tsara yin jarabarwar neman shigarta ne akaran kanta ga daliban dake da sha’awar shiga, sai a cikin shekarar 1976 zamanin mulkin soja na Olusegun Obasanjo aka samu Karin jami’o’I guda shida (6) sannan aka fara tunanin yadda za’a maida yin jarabawar neman shiga makarantun gaba da sakandire bai daya a lokacin ne gwamnati ta kafa wani kwamiti da zai tsara da kuma lura da yadda al’amuran zasu kasance kar-kashin Mr. M. S. Angulu.
An kirkiri hukumar shirya jarabawar Jamb a shekara ta 1978 sannan an yi wa hukumar garanbawul a shekarar 1989 da 1993 duka wadannan lokuta ana yin jarabawar ne a takarda a shekarar 2009 hukumar ta fuskanci matsaloli agame da jarabawar hakan yasa a shekarar 2013 akayi wani kwarya-kwaryar canji na tsarin gudanar da jarabawar inda aka koma amfani da Computer wajen gudanar da ita saboda wasu dalilai da zasu zo a gaba.
Zamu cigaba gobe idan Allah ya kaimu.
Basheer Sharfadi
Social Media Strategists.
16-01-2019.
Email: info@sharfadi.com
Call & WhatsApp: 09035830253
#Jamb #Students
Read More»
Subscribe to:
Comments (Atom)








