Wednesday, January 16, 2019

Home Hukumar Hisbah Ta Fasa Kwalabe Sama Da Dubu Sittin Na Giya A Kano
..
Hukumar Hisbah Ta Fasa Kwalabe Sama Da Dubu Sittin Na Giya A Kano

Daga Anas Saminu Ja'en

Mai girma shugaban ƙaramar hukumar Gwale Hon. Dakta Khalid Ishak Ɗiso da jama'ar sa tare da haɗin gwiwar hukumar Hisba ƙarƙashin jagorancin shugaban ta na ƙaramar hukumar Gwale Yahaya Bala Sabon Sara, suka jagoranci farfasa kwalaban Giya waɗanda aka kama a lokacin da aka shigo dasu cikin jama'a ake ƙoƙarin sayarwa wanda kimanin ta ya kai dubu sittin (60000).

Kowa ya san a jihar Kano dai ana amfani da dokar shari'ar Musulunci wanda ta hana shigowa ko shan kayan barasa, a lokacin da shugaban ƙaramar hukumar ke jawabi ya ce ma'aikatan Hisba kuma za su ƙara ƙoƙari tare da yaƙi da duk wani mai ta'ammali da kayan maye ba giya ba kawai wajen ganin an bi wannan doka a faɗin jihar a wannan shekarar da aka shiga.

Taron fasa giyar ya samu halartar manyan mutane wanda suka haɗar da wakilin gwamna da wakilin hakimin da mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Hon. Ado Gambo Ja'en, sakataran ƙaramar hukuma Hon. Abdullahi Sarki tare da manyan Malam addinin Musulunci ƴan takarkarun majalissun tarayya dana jihar na ƙaramar hakumar Hon. Abdullahi Lawan Kenken da Hon. Usman Zubairu da sauran masu faɗa aji daga ciki da wajan ƙaramar hukumar Gwale da kuma dubban al'ummar gari, kuma an gudanar da wannan fasa giyar a hauren yara kusa da helkwatar ƴan sanda ta ɗaya wato Zone 1 dake jihar Kano.
No comments:
Write comments

Follow Admin On Twitter naimismo1
Join Our Newsletter