Sunday, February 24, 2019

GANDUJE YA DAUKO HANYAR CIKAWA BUHARI ALKAWARI

GANDUJE YA DAUKO HANYAR CIKAWA BUHARI ALKAWARI 

WASU DAGA CIKIN SAKAMAKON ZABEN SHUGABAN KASA DAGA JIHAR KANO, WADANDA JAMI'AN ZABE NA KANANAN HUKUMOMI SUKA SANAR DA BAKINSU...

1.. Presidential Result Tofa L.G Kano State.

A.P.C 37,732
PDP 19,984

2.. Presidential Result for Ajingi L.G Kano State.

A.P.C 21,384
PDP 5,275

3.. Presidential Result for Albasu L.G Kano State.

A.P.C 26,475
PDP 10,285

4.. Presidential Result in Garun Malam L.G Kano State.

A.P.C 23,810
PDP 13,003 

5.. Presidential Result in Madobi L.G Kano State.

A.P.C 26,110
PDP 13,113

6.. Presidential Result in Gwale L.G Kano State.

A.P.C 50,332
PDP 25,844

7.. Presidential Result in Fagge L.G Kano State.

A.P.C 27,020
PDP 20,405

Wasu daga cikin ingantattun sakamakon da aka sanar kenan, a gidan Rediyon jihar kano, inda suke saka Baturen zabe na kowacce karamar hukuma yake bayani da bakinsa....
Read More»

Thursday, February 21, 2019

Assalin Hausawa

Asalin Hausawa abu ne da aka sha kuma ake kan tambaya a kullum, sai dai abin takaici har yanzu ba a sami wata cikakkiyar amsa mai gamsarwa ba. Kafin mu yi nisa ya kamata mu san ko su wane ne Hausawa. Hausawa dai su ne mutane wadanda harshensu shi ne Hausa sannan dukkan al’adunsu na Hausa ne. Haka kuma addinin musulunci ya yi cikakken tasiri a kansu.
Mutane dabam-daban sun yi bincike sosai a kan ilmin harsuna da abubuwan da aka kattaba da kuma zantukan baka. Ta hanyar irin wannan bincike ne aka gane cewa wadansu harsuna suna da kama da juna ainun, wanda ya haifar da kara zurfafa nazarce-nazarce. Sakamakon haka ne kuwa aka karkasa harsunan Afrika ta yadda kowane kaso ya kunshi harsuna wadanda bisa dukan alamu tushensu guda. Ma’ana a asali su wadannan harsuna harshe ne guda daya wanda wasu dalilai irin su bambancin wurin zama, sanadin kaurace-kaurace da yake-yake da dai wadansu dalilai suka sanya ya karkasu ya kasance harsuna iri-iri a halin yanzu.
Akwai dangunan harsuna da dama a cikin Afrika. Misali akwai dangin Bantu a can wajen tsakiyar Afrika wadanda tushensu duka daga wani tsohon harshe ne wai shi Bantu; akwai kuma dangin Kwa wanda ya kunshi Yarabanci da Ibo da Nupanci da dai sauransu. Ita kuwa Hausa tana cikin harsunan iyalin Cadi. Ko da yake shi wannan harshe babu shi a yanzu, wannan suna na Cadi suna ne kawai da masana ilmin harsuna suka kirkiro. Dalili kuwa shi ne yawancin iyalin wannan harshe ana samunsu a farfajiyar tafkin Cadi. To saboda rashin sanin ainihin sunansa sai aka kira shi da sunan Cadi. Harsunan iyalan Cadi suna da yawa. Akwai Angas da Bacama da Bade da Bolanci da Bura da Hausa da Kanakuru da Karekare da Mandara da Margi da Miya da Ngizim da Tera da dai sauransu. A sakamakon kamanni da wadannan harsuna suke yi da juna ya sanya aka danganta su ga tushe guda.
A bisa wannan dan bayani muna iya cewa Hausawa da harshensu sun fito ne daga cibiya daya da sauran harsunan iyalin Cadi. Wannan kuwa zai ba mu damar cewa mutanen da suka zama Hausawa sun fito ne daga Gabas ko arewa maso gabas da wurin da suke a yanzu
Daga nan sai mu duba abubuwan da aka kattaba. A nan an samu mutane dabam-daban sun yi rubuce-rubuce a kan asalin Hausawa da harshensu. A wani littafi da ya wallafa a kan Daular Usmaniyya, Johnston ya bayyana cewa a tsakanin shekarar 1050 zuwa 1100 ta Miladiyya wadansu, Berbers, (Buzaye) sun ratso sahara suka zauna cikin Tukururu kuma suka yi auratayya da su. Wai a sanadin wannan cudanya ne aka sami Hausa da harshen Hausa.
Shi ma wani marubucin dangane da tarihin Hausawa da harshensu, M.G. Smith, yana da ra’ayi kusan iri daya da na Johnston. Wato ya amince da cewa akwai kaura da ta auku daga gabas zuwa kasar Tukururu, wanda ya yi sanadin samuwar Hausawa da harshensu. Ya kare da cewa wannan kaura ta auku ne wajajen shekarar 1350 ta Miladiyya.
Shi kuwa Abdullahi Smith nuna rashin amincewarsa ya yi da wannan bayani da aka yi dangane da asalin Hausawa da harshensu. Musamman ma cewa wai nan da shekara dubu da suka wuce babu Hausawa. Shi yana ganin cewa kasa rarrabewa tsakanin asalin Hausawa da harshensu da kuma asalin daular mulkin da suka kafa shi ne dalilin rashin fahimtar. Haka kuma bai amince ba da cewa Hausawa sun samu a sakamakon auratayya tsakanin Berbers (Buzaye?) da kuma Tukururu da suka taras a wurin. Hasali ma ra’ayinsa ya fi karkata ga cewa Hausa tana da alaka da harsunan iyalin Cadi, har hakan ma kuwa yana ganin cewa sun raba hanya shekaru dubbai da suka wuce.Ya kuma kara da cewa mai yiwuwa da can akwai dangantaka tsakanin harshen Berber da na Cadi, wato tun kafin Sahara ta zamo hamada.
Babu shakka ba abu ne mai karbuwa ba a ce nan da shekaru 950 da suka wuce babu Hausawa da harshensu, musamman idan aka dubi tarihin garuruwan Hausa da jerin sarakunan da suka mulke su. Misali an ce tun karshen karni na 9 na Miladiyya wadansu maharba suka zo suka zauna a duwatsun da ke kewaye da sararin da ake kira Kano yanzu. Idan haka ne wannan ya nuna cewa akwai Hausawa a wannan wuri fiye da shekaru 1,000 da suka wuce.
Read More»

Wednesday, February 13, 2019

DA WANNE YATSA ZAN YI ZABE?

DA WANNE YATSA ZAN YI ZABE?

A cikin satin nan, wasu sakonni na ta yawo a kafafen sadarwa musamman facebook da Whatsapp cewa kar a yi zabe da babban dan yatsa (Thumb) sai dai yatsa dan manuni (Index Finger). Hakan ya janyi cece-ku-ce tsakanin al-ummma inda wasu ke ganin ko wata makarkashiya aka shirya don murde zaben.

Gaskiyar Magana ita ce, takardar zaben na dauke da jam’iyyu kusan saba’in (70) ko ma fiye da haka. Hakan ne ya sa aka matse dan sararin da masu zabe za su dangwala kuri’unsu. Kowa ya san cewa idan inkin ya taba sararin wata jam’iyya daban toh fa kuri’arka ta lalace (Invalid), ba za a kirga da ita ba.  Sanin cewa babban dan yatsa na da fadi shiyasa aka ba da shawarar yin amfani da dan manuni wajen dangwalawar don kar inkin ya shiga sararin wata jam’iyyar daban da wanda ka so dangwalawa.

Haka kuma in an zo dangwala inkin daidai kan yatsan za a saka ba fuskar yatsar ba don gudun kar a yi abinda bahaushe ke cewa ‘An gudu ba a tsira ba’.

Abinda dai ake so shine ka kiyaye kar inkin ya taba sararin wata jam’iyyar kawai! In har za ka kiyaye hakan toh babu matsala akan duk yatsan da ka yi amfani da shi tunda da hannu ake kirga kuri’un ba da kwamfiyuta ba.

Allah Ya sa a yi zabe lafiya.  

©Almu Dakata
Read More»

Tuesday, February 5, 2019

*DAURE KA/KI KARANTA WAYANNAN NASIHOHI 35 zasu taimake ka/ki wurin samun ingantacciyar rayuwa*

*DAURE KA/KI KARANTA WAYANNAN NASIHOHI 35 zasu taimake ka/ki wurin samun ingantacciyar rayuwa*
______________________________________
1- ka fara yininka da sallar asubahi da azkar domin samun rabo da tsira.

2- ka zarce da istgfari har sai shaidan ya debe
tsammanin samun rabo a jikinka.

3-kar ka daina addu'a dumin itace igiyar tsira

4-ka tuna cewa mala'iku suna rubuta maganganunka.

5-kyawun yatsu shine ka rika qidaya TASBIH dasu.

6- idan ka shiga damuwa da qunci kace" la ila ha illallah".

7- ka sayi addu'ar talakawa da soyayyan marayu da kudadenka.

8-doguwar sujada 1 wanda aka yita saboda tsoron ALLAH yafi maka bene da aka gina na zinari.

9- ka tauna magana kafin kafadeta domin tana iya zama ajalinka.

10- ka guji addu'ar wanda aka zalunta da hawayen wanda aka hana.

11- kafin ka karanta jaridu da mujallu mai zai hana.kafara karanta alqur'ani.

12- ka zama dalilin gyaruwan iyalanka.

13- ka tilastawa ranka wurin bin dokokin Allah ,
domin ita rai tana umarni ne da sabon Allah.

14- kafin tsufar iyayanka ka daure ka samu yardarsu.

15-tsoffin tufafinka sababbi ne a wurin talakawa.

16- kar kayi fushi , domin rayuwa kadan ce ba kamar yadda kake tsammani ba.

17- tare dakai akwai wanda yafi kowa qarfi yafi kowa wadata, shine Allah.

18- kar ka rufe qofar tuba saboda sabon Allah.
19- sallah itace mafi alkhairin abun da zata taimakeka akan musibu da wahalhalu.

20- ka nisanci munanan zato, zaka huta kuma zaka hutar.

21- dalilin kowane damuwa juyawa Allah bayane, ka juyo zuwa gareshi mana.

22-kayi sallah irin wacce kakeso a shigar dakai qabari tare da ita.

23- idan kaji wanda yake gulma , kace dashi: yaji tsoron Allah.

24-ka dawwamar da kanka wurin karanta suratul MULK domin tana tseratarwa.

25- wanda aka hana( yayi hasara) shine wanda aka hanawa sallar dake cike da tsoron Allah , da idon dake zubar da hawaye.

26- kar ka cutar da bayin Allah nagari wadanda suka shagaltu da bautar Allah.

27- ka sanya soyayyar ka duka zuwa ga Allah da manzonsa.

28- ka yafewa wanda yayi gulmarka, domin ya baka kyautar kyakyawan aikinsa ne.

29- Sallah da ambaton Allah da karatun alqur'ani alqawurane masu nauyi akan qirjinka.

30- duk wanda ya tuna da zafin wuta zai iya hakuri akan sabon Allah .

31- indai ana dare gari yana wayewa, to watarana sai labari tsanani zai zama sauqi.

32- ka nisanci ANCE-KACE ( jita-jita) domin kai game da ayyuka kamar dutsene.

33- kayi sallah da tsoron Allah , domin duk abun da zakayi bayan sallar bai kai sallah ba.

34- ka sanya alqur'ani daf dakai , domin karanta aya daya acikinsa yafimaka duniya da abun dake cikinta.

35- rayuwa akwai dadi, mafi dadin rayuwa shine kaganka da iimaninka.
________________________________
ALLAH Yasa Mudace!
____________________________
*TEMAKA KA YADA DOMIN ANFANIN ALUMMA*
Read More»

Monday, February 4, 2019

KARANTA KAJI YADDA ZAKABAR DUNIYA KOKANASO KO BAKASO

      *MISALI*
Bayan na dauki
wani lokaci mai
tsayi ina kwance
ina bacci sai naji
matata tana ta
tashina daga bacci,
babban abinda ya
bani mamaki shine
yadda na farka
kuma nakemata
magana cewa ME
KIKE BUKATA?
amma ita kwata
kwata batajin
maganar da
nakemata, amma
ahaka tajuya ta
fita, bayan kamar
minti 30 sai ta
dawo takara
tashina na farka
nacemata ME KIKE
BUKATA? amma
ina batasanma
inayiba. Kawai sai
naga ta fita waje
afirgice tana kiran
'yan-Uwana. sai
naga 'yan-Uwana
sunkira likita yazo
gurina yana gwada
jikina, sai nacema
likitan ME KAKE
BUKATA? amma
wani abin mamaki
sai naga likitan
bayajin maganar
da nakeyi, sai naji
likita yana gayama
'yan-Uwana cewa
na" mutu". Sai suka
firgita sukai tayin
koke-koke duk
dacewa
banmutuba, ni dai
bansan dalilin da
yasa basajin
maganataba, wannan
abu yayi matukan
ban mamaki
musamman da naji
'yan-Uwana
sunacewa
"agaggauta ayi
jana'izata", sai naga
sun daukeni
sunkaini dakin da
nake ajiye
motocina, ga shidai
inayimusu magana
amma kwata
kwata basajin
maganar da nakeyi,
sai suka ciremini
tufafina sannan
suka yimini wanka
suka samini
likkafani kuma
suka daukeni suka
kaini masallaci don
ayimini sallah. Na
samu liman na
gayamasa cewa
da raina ban
mutuba, amma sai
naga liman yaki ya
kulani inaji ina gani
sukaimin sallah,
bayan sungama
yimin sallah sai
suka daukeni suka
nufi makabarta
dani inaji ina gani
suka rika kokarin
binneni, bayan
sun sa ni acikin
kabari sai naga
wani daga cikin
'yan-Uwana na
kusa wai har dashi
ake kokarin
binneni, sai
nacemasa NIFA
BAN MUTUBA, dan
haka karda ku
binneni, amma sai
naga ko kulani
baiyiba kamar
baisan inayimasa
maganaba, bayan
sungama zubamini
kasa sai na tuna da
Hadisin MANZON ALLAH (S.A.W)
ya ce "lallai mamaci
yanajin takun
takalman mutane
idan suka juya
zasu fita daga
maqabarta", sai
nima narika jin
takun takalmansu
alokacinda suka
juya suka barni
acikin
kabari, wannan
shine abinda ya
tabbatar mini
cewa AYANZU INA
CIKIN WANI GURI
MAI TSANANIN
DUHU. Bayan haka
sai wasu mazaje 2
masu firgitar da
jama'a sukazo
guna, 1 daga
cikinsu ya tsaya
akusa da kafafuna
1kuma ya tsaya
akusa da kaina
sannan aka
tambayeni WAYE
UBANGIJINKA? sai
na fara tinani
waye Ubngijina?
alhali nasan
Ubangijina dan
haka narika
mamakin yadda
akayi na manta,
haka aka
tambayeni WAYE
ANNABINKA?
nanfa na fara
tunani ANNABINA
ANNABINA
ANNABINA
sannan aka
tambayeni miye
ADDININKA? nanfa
nashiga tunani
addinina addinina
ga shidai nasan
amsoshin amma
abun mamaki shine
yadda na
manta, babu wani
abu da yake
fadomini arai bancin
matata da
shagona da 'yan-Uwana da motata,
har saida naga
ansa wani katon
kulki andakeni
dashi duka mai
tsanani, nanfa na
saki baki na
kwarara ihu!, IHUN
DA YA TAYAR DA
DUKKANNIN
MUTANEN
GIDANMU da
sukeyin bacci, sai
matata ta kira
sunana sannan
tace:MEYASA
KAKEYIN IHU DA
KA'RA IRIN HAKA?
awannan lokacin
ne na gane cewa
mafarki nayi, nanfa
na tsaya inata
haki kawai sai naji
ankira sallar
asubah sai ya
zamana cewa
wannan mafarki
da nayi shine
sanadiyyar
shiriyata, tundaga
wannan ranar
narika dagewa
wajen yima ALLAH
(S.W.T) biyayya.
WANNAN KENAN, gaskiya 'yan-Uuwa Musulmai
muji tsoron ALLAH, domin watarana wannan labari
zai faru akankowa wannan tunatarwace,
muna rokon ALLAH yabamu ikon amsa tanbayoyin
kabari.
YA ALLAH KADAUKI RANMU MUNA MUMINAI

Read More»
Follow Admin On Twitter naimismo1
Join Our Newsletter