DA WANNE YATSA ZAN YI ZABE?
A cikin satin nan, wasu sakonni na ta yawo a kafafen sadarwa musamman facebook da Whatsapp cewa kar a yi zabe da babban dan yatsa (Thumb) sai dai yatsa dan manuni (Index Finger). Hakan ya janyi cece-ku-ce tsakanin al-ummma inda wasu ke ganin ko wata makarkashiya aka shirya don murde zaben.
Gaskiyar Magana ita ce, takardar zaben na dauke da jam’iyyu kusan saba’in (70) ko ma fiye da haka. Hakan ne ya sa aka matse dan sararin da masu zabe za su dangwala kuri’unsu. Kowa ya san cewa idan inkin ya taba sararin wata jam’iyya daban toh fa kuri’arka ta lalace (Invalid), ba za a kirga da ita ba. Sanin cewa babban dan yatsa na da fadi shiyasa aka ba da shawarar yin amfani da dan manuni wajen dangwalawar don kar inkin ya shiga sararin wata jam’iyyar daban da wanda ka so dangwalawa.
Haka kuma in an zo dangwala inkin daidai kan yatsan za a saka ba fuskar yatsar ba don gudun kar a yi abinda bahaushe ke cewa ‘An gudu ba a tsira ba’.
Abinda dai ake so shine ka kiyaye kar inkin ya taba sararin wata jam’iyyar kawai! In har za ka kiyaye hakan toh babu matsala akan duk yatsan da ka yi amfani da shi tunda da hannu ake kirga kuri’un ba da kwamfiyuta ba.
Allah Ya sa a yi zabe lafiya.
©Almu Dakata











No comments:
Write comments