Sunday, June 23, 2019

HANYOYIN SACE ZUCIYAR BUDURWA

  1. Kasan cuwar mu na ‘yan adam a doran ƙasa, Allah ya halicce mu ne don mu bauta masa kuma shi ne ya sanya soyayya da sha’awa a tsakaninmu. Saboda haka samarin da suke ƙoƙarin ganin mallakan zuciyar ‘ya mace ko kuma samun zuciyarta ba tare da wata mishkila ba, ga wasu hanyoyin guda takwas da ake bi don sace zuciyar budurwa. 
  2.  TSARI: Duk wata ‘ya mace tana son ta ga namiji mai tsari, ba wai tsari irin na magana ba. Abin da nake nufi da haka shi ne, namiji ya kasance yana da tsarin rayuwa mai kyau, ba mutum ya zama shashasha maras kan gado ba. 
  3.  KYAU DA KWALLIYA: Wasu matan suna son mutum mai kyau da kwalliya ba irin su wancan nanka ba, sau da yawa za ka ga mata suna soyayya da saurayi saboda tsabar kyau da Allah ya ba shi, da kuma iya kwalliya kamar ɗawisu.   KALAMAI: Yana da kyau namiji ya zama ya iya kalaman da za su janyo hankalin duk wata ‘ya mace, rashin iya kalami kan janyo rashin masoyi. Maimakon haka sai ka zama tamkar ɗan bora a soyayya. Dole ne ka kasance ka iya kalaman da zaka birge budurwa.
  4. KIRKI DA KULAWA: Namiji yakan tafiyar da zuciyar ya mace dalilin kasancewa mai kulawa da kirki. Misali duk bayan wani lokaci ko sa’ar da ba ta fi rana ɗaya ba, ko kwana biyu a ce kana zuwa ganin ta ko kuma kana kiran ta, idan ya yi yawa ne a ce kun haɗu sau uku. Musamman ma a irin wanan lokacin da wayar hannu ta zama ruwan dare. Wani lokacin idan haɗuwa ta yi ƙaranci sai ka kirata a waya. Amma fa ka sani yawan zuwa gun mace ko masoyiyarka ce wani zubin nasa gundura. Ma’ana za ta ji duk ta gaji da ganin ka, musamman idan ya zama soyayyar taku ba ta yi ƙarfi ba. 
  5.  KAR KA RIƘA YAWAN YI MATA MAGANA GABAN ƘAWAYE: Ka guji yawan kula yarinya cikin sahun ƙawayenta ko kuma cikin jama’a. Hakan zai karama kima, sannan da nesan ta kanka ga barin wulakanci. Wata kila lokacin da ka je mata cikin jama’a ko ƙawayen ta, ta ji tana son ka. To amma watakila a lokacin shigar da ka yi bai yi mata ba. Hakan zai sa ta guje ka, wanda yin haka a soyayya wulakanci ne ga masoyi. Mafi kyawu shi ne ka jira ta keɓance ko kuma ta koma gida. Idan ba haka ba, to sai dai idan sun kai koda su biyar ne, to kuma ya zama dole ku kasance ku biyar koda sauran ba sa san ‘yan matan. Saboda su kasance masu ɗauke masu hankali a lokacin da kuke hira kuma suma sauran ‘yan matan yin haka zai nuna cewa wadda kake so ba ta fita daban a cikin su ba. Duk abin da sauran ƙawayenta suka ce a kanka da shi za ta yi amfani. 
  6.  BARKWANCI: Idan ka kasance mai raha ga masoyiyarka to nan da nan za ka sace zuciyarta. Misali ka riƙa ce mata a duk lokacin da ka zo hira da ita, amincin so gareki ya tauraruwan zuciyata, ɗaya tamkar da goma cikin sahun mataye, a do da kyau siffarki ce, murmushinki ke sanya zukata fara’a. gimbiya adon ‘yan mata. Da sauran su. Kana mai ambaton haka cikin murmushi da shauƙi irin na soyaya kuma dole ne hirarku ta kasance mai amfani ba ka yi ta zuba ba, har sai ka gundure ta. Yawan magana ba shi da tasiri a soyayya muddin ba magana ne masu ɗauke hankali da san ji ko rashin gundura ba.   KUƊI DA KULAWA: Mata suna son samun saurayi mai tashen kudi da kulawa cikin bukatunsu a koyaushe. Idan ta samu wanda ya haɗa waɗannan abubuwa kuma ya tafiyar da su yadda ya kamata, to abu ne mai sauƙi ya sace zuciyar budurwa. Akwai mazan da suke roƙon ‘yan matansu kuɗi; wannan ba soyayya ba ce, sai a kira shi a kwaɗayi. 
  7.  KYAUTATAWA: Sai dai kuma duk da na yi bayani kan cewa kwaɗayi bashi da kyau a soyayya, hakan ba shi yake nuna ba za ka kyautatawa masoyiyarka ba. Hasali ma idan kai haka, to za ka ƙara ƙarfin shaƙuwa ne tsakanin ku da juna. Sai dai idan za a yi kyautaa duba me masoyiya take da buƙata a daidai wannan lokaci. Misali, kar ka kawo mata hoda a lokacin da take buƙatar turare, atamfa, yayin da ita kuma leshi take so. Sanin haƙiƙanin abin da budurwa ke so, ko da ku fara soyayya da ita, ko ba ku fara ba, yana taimakawa ƙwarai wajen sace zuciyarta. Samfurin Kalaman Soyayya Masoyiyata,
  • ina son ki fiye da yadda kike so na.
  • Ina son kasancewa tare da ke domin kina farantawa zuciyata.
  • Kallon ki kaɗai kan sanya in samu kuzari, duk wata kasala da lalaci in ji ta gushe.
  • Ke ce farin cikina. Ina nan riƙe da amanar soyayyarki har ƙarshen rayuwata.
  • Na saka a raina ba zan taɓa mantawa da ke ba.
  • Sonki tamkar wani fure ne da idanuwana suke ƙawatu wa da kallonsa, hanci ya ji daddaɗan ƙamshi, ruhi kuma ya samu nutsuwa.
  • Idan rayuwa ba za ta yiwu ba tare da ruwa da iska ba, haka ni ma ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba.
  • Jin daɗi da walwala ba za su taɓa samuwa a tattare da ni ba matuƙar babu soyayyarki a cikin zuciyata.
  • Kin zama tauraruwa da ke haska ilahirin bishiyoyi da furannin da suke lambun zuciyata.
Read More»

Tuesday, June 18, 2019

WASU DALILAI DA KE SA NAMIJI YA QARA AURE


WASU DALILAI DA KE SA NAMIJI YA QARA AURE...

Dalilan suna da yawa amma dai ga wasu daga cikinsu zan lissafo kamar haka :-

-Akwai namijin da har ga Allah bai son qara aure yafi son zama da mace daya... To amma idan aka yi rashin sa'a ya auro wacce sai daga baya ya fahimci ba irin ta yake son zama da ita ba... Ko wacce bata haihuwa, ko mai lalura,to sai ya fara tunanin qara aure idan mai hankali ne kenan amma idan ba mai tunani bane sai ya saki matar ya auro wata...

-Akwai namijin da dama shi tun fil'azal burinsu shine ya auri mace fiye da daya... Kuma irin wadannan mazan duk irin kirki da tarbiyyar matar da suka aura a farko hakan ba zai hanasu qara aure ba dole sai sun qara din...

-Akwai mazajen da su kuma tsakani da Allah suke qara auren saboda raya sunnah kuma saboda suna da halin rike matan...

-Akwai wasu mazan wanda ba zasu iya zama da mace daya ba dole sai fiye da daya domin halittar ce haka kuma suna da cikakkiiya lafiya...

-Akwai wasu mazan masu qara aure kawai saboda naga abokaina su wane da wane sun qara aure amma ba wai dan yana da ra'ayi ba...

-Akwai wasu mazan wadanda suke qara aure saboda bin umarnin iyayensu... Watakila sun fahimci matarshi ta farko bata da tarbiya ko basu jituwa da ita saboda haka sai su samu wata a cikin dangi su ce lallai sai d'ansu ya qara aure da ita...

-Akwai mazan da basu da niyar qarin aure amma dalilin wata budurwa ko wata bazawara ta lik'e musu tun suna tirjewa har qarshe matan suyi nasara akan su...

Dalilan suna da yawa gaskiya kaima ko kema zaku iya kawo naku domin mu ji kuma mu qaru...

A wurin musulmi qarin aure ba zunubi bane ba kuma laifi bane... To amma tsakani da Allah akwai wasu mazan wadanda qarin aure bai zama cilas a garesu ba amma saboda karanbani sai su dage dole sai sun yi... Watakila kuma basu da hali ko dama ko lafiyar yin hakan kuma yin haka kamar ka shiga hakkin matanka ne da kai kanka gaba daya...

An ce namiji ya qara aure ne idan har yana da hali kuma zai yi adalci...Amma maganar gaskiya a wannan zamanin kowa yana qara aure ne domin wani muradi na karan kan shi ba wai dan Allah ko dacewa ba...

ALLAH YA BAMU IKON YIN ADALCI
Read More»

Monday, June 17, 2019

LABARIN WANI MUTUM DA YA BUGI MATAR SA

LABARIN WANI MUTUM DA YA BUGI MATAR SA.

Ya kasance cikin tsananin fushi bisa abinda ta aikata a gare shi na ba daidai ba a ranar, daga ƙarshe ya kasa haƙuri har sai da ya duke ta duka mai tsanani.

 Bayan ta gama 'yan koke koken ta ne ta tashi zumbur kamar mai shirin miyar da martani, cikin fushi ya tambaye ta, ina za ki tafi?

Kuma me za ki yi?

 Ta kalle shi a wulaƙance sannan ta ce, zuwa zan yi in kai ƙarar ka.

Ta yaya za ki fita daga gidan nan alhali duk ƙofofi da tagogi suna rufe?

Ya faɗi hakan tare yin dariyar mugunta, ta dube shi cikin murmushi sannan ta ce, ai waya zan buga.

Ta yaya za ki buga waya bayan wayoyin ki duk suna tare da ni?

Ya ba ta amsa.

Koh kula shi ba ta yi ba, kai tsaye ta wuce banɗaki (bathroom) sai ya zaci koh za ta fita ta taga (window) ne don haka ya yi sauri ya zagaya koh zai ga fitan ta domin ya dakatar da ita.

Ya ɗauki dogon lokaci yana tsaye amma bai ga yunƙurin fitowar ta ba, nan ya yanke shawarar komawa cikin gidan.

 Bayan shigowar sa ne ya tarar ta fito faca faca da ruwa, bisa ga dukkan alama alwala ta yi.

Ya dube ta cikin mamaki sannan ya ce, wai me kike shirin aikatawa ne?

 Zan kai ƙarar ka ne a inda rufe ƙofofi, tagogi da ƙwace waya ta ba za su taɓa zama katanga tsakani na da shi ba, zan kai ƙarar ka ne gurin Allah.

 Nan take ya ji nadama ya lullube shi.

Ta fara sallar ta ba tare da ta kula shi ba, yayin da ta kai ga rukunin sujjada sai ta tsawaita, abinda ya tayar masa da hankali matuƙa kenan.

Haka ta ci gaba da tsawaitawa cikin sujjada har ta idar da sallar.

 Ta ɗaga hannaye sama za ta fara addu'a kenan ya yi laraf ya cafe hannayen ta, nan ya fara kuka yana ba ta haƙuri yana cewa, wallahi sharrin shaiɗan ne.

Dubi yanda ki ka tsawaita cikin sujjada kina addu'a a kai na, wannan bai ishe ki ba har sai kin sake yin wata addu'ar?

 Ta kalle shi cikin tausayawa sannan ta ce, a kan menene za ka dakatar da mace daga yiwa mijin ta addu'a?

Ka sani ya kai miji na, ina yin addu'a ne da kyakyawar zuciya gare ka, ina roƙon Allah ya raba ka da wannan shaiɗani da ya ke tunzura ka har ka ke ƙoƙarin watsa gidan ka alhali ba ka sani ba, ina roƙon Allah ne ya kawar da duk wani saɓani tsakanin mu sannan ya kawo zaman lafiya mai ɗorewa tsakani na da kai masoyi na.

Nan ya ƙara sautin kukan sa, ya faɗi gurfane a gaban ta yana roƙon gafarar ta, daga yau babu dalili da zai sa in sake ɗora hannaye na a jikin ki da cutarwa, wallahi na yi alƙawari masoyiya ta, ki gafarce ni don Allah, hakan ba zai sake faruwa ba Inn shaa Allah.

Ta dube shi a natse sannan ta rungume shi ta na mai cewa, wallahi ba ni da kamar ka masoyi na, ka shaida na yafe maka kuma ina roƙon gafarar ka bisa kuskure na, Inn shaa Allahu ba zan sake ba.

Haka suka kasance rungume da juna tare da ɗora nadama cikin zukatan su bisa kuskure da kowannen su ya aikata. Duk wanda ya yi rashin masoyin gaskiya haƙiƙa ya yi hasara babba, Allah ka bar mu da masoyan mu.

Tambaya :

1. Wane darasi ku ka ɗauka cikin labarin?

2. Sannan me ya fi burge ku cikin labarin?

Tushe : ﺭﻭﺍﺋﻊ ﺍﻟﺸﻌﺮ ﻭﺍﻷﺩﺏ ﺍﻟﻌﺮﺑﻲ
Read More»

ABIN DA YAKE KASHE MATANMU NA HAUSA KENAN

ABIN DA YAKE KASHE MATANMU NA HAUSA KENAN...

Na dade ina irin wannan nazarin game da rayuwar matan qasar hausa akan menene dalilin da yasa suke saurin tsufa da zaren an yi musu aure sun je gidan miji...

Zaka ga yarinya qarama wacce aka haifeta a gabanka da zaren ta isa aure an kaita d'akin miji shekara daya kawai zuwa biyu bayan ta haihu idan ka ganta abin zai baka tsoro da mamaki domin zaka ganta duk ta tsufa ta yank'wane kamar wata Anty...

Abin da yake bani mamaki shine kafin 'yan matan suyi aure sun iya kama jikinsu da daukar wanka da kwalliya... Watakila wannan shine dalilin da yasa samari suka yi mata chah a lokacin tana gidansu... Amma da zaren ta shiga d'akin miji shikenan wannan kama jikin da wannan wankan da kwalliya duka sun zama tarihi... Musamman idan ta samu juna biyu ko kuma ta haihu a wannan lokacin wata matar ko abincin da ta dafa wani namijin mai tsantsami ba zai iya ci ba balle har yayi hira ko hada shimfida da ita ba... Kuma a irin wannan yanayin ba kowane namiji bane zai iya zama da irin wadannan matan ba dole sai dai cikin biyu ayi daya ko dai ya saketa ko kuma ya qaro aure...

Da yawa matanmu haka suke basu damu da ado da gyaran jikinsu ba kamar yadda suke a lokacin suna 'yan mata... Dalilin kenan da yasa mazajensu ke gudunsu suna bin' yan matan waje ko karuwai... Domin matansu basu yi musu irin wannan kwalliyar da suke gani a wajen 'yan matan waje...

Kullum zaka tarar da mace da d'aurin kirji kai a chukurkud'e ya tsufa ba kitso ba sarta... Yadda take a hargitse haka 'ya'yanta da d'akinta da gidanta suke babu kulawa... Idan mijin yayi magana domin ta gyara sai tace:-

"Kawai dai Baban Auwal ka gaji da ni ne duk shi yasa kake ta yimin irin wannan tsangwamar... To ya kake son nayi ni inji ce da zanyi ta aiki ba na gajiya? Jiya fa nayi wanka kuma na share d'akin nan sannan nayi wa yaran nan wanka"...

Babu yadda mijin ya iya dole sai dai yayi hakuri ya daina gayyato abokansa gidan dan kada su fahimci matsalar matarsa ko kuma ya fara tunanin sakinta ko qara aure...

Abin da zai baka mamaki shine irin wadannan qazamen matan idan suka tashi fita unguwa wallahi idan ka gansu ba zaka iya ganesu ba... Wanka suke dauka ayi kitso da k'unshi da gyaran jiki kamar zata gasar kyawawa... Har qananen 'ya' yansu sun ganesu da zaren sun yi kwalliya to unguwa za'a tafi sai ka ga yaran sun fara binsu suna yi musu kuka dan kada iyayen su tafi su barsu a gida...

Idan kuma aka yi rashin sa'a mazajen suka gaji suka sakesu idan suka fara zawarci sai kuma kaga sun fara wanka da kwalliya... Wasu mazajen kuma zasu daukesu a rashin sani sai anyi auren kuma hali ya bayyana a sake sakinsu... To haka za'ayi tayi har ma qarshe su rasa wanda zai auresu...

Wallahi mata wannan shine babbar matsalarku shi yasa kuke tsufa tun da qananen shekarunku... Kuma shi yasa mazajenku ke gudunku ko aurenku ya mutu... Ku lura da kyau ku ga yadda turawa, larabawa, indiyawa da qabilunmu wadanda muke zaune qasa daya ku gani haka suke yi?

To dan Allah mata a daure a dinga wanka da kwalliya da tsafta domin ba kowane namiji bane zai iya zama da qazamar mace irin wannan ba... Kamar yadda kuke gyara jikinku kafin aure dan samari su gani su yaba haka yakamata ku gyara jikinku a gidajen mazajenku domin aurenku yayi lasting kuma ku zauna lafiya ... Jikin mata ba irin na maza bane dole sai da gyarawa...
Read More»

Saturday, June 15, 2019

YADDA ZAKA DUBA BALANCE 38GB DATA DINKA

YADDA ZAKA DUBA BALANCE 38GB DINKA

Kamar yadda post yagaba akan Data wanda kamfanin mtn suke bayar wa gaabiyan su nayi Alkawari a baya kan yadda zaka duna data zai biyo bayan

Post din yadda zakan samu datan to Alkawari ya chika insha Allahu ga mai bukata sai ya natsu Domin.samun yadda zai duba datar da aka bashi

Ta mtn Data Roaming bawani dagon bayani kawai zaka sake shiga Dail pad din ka ne kawai sai ka danna
*559*24#

Naku har kullum naimismo1

Kusan che tare da mu don samun Post masu Alaka damn wanan mun gode
Read More»

MTN 38GB DATA KYAUTA A LAYIN KA NA MTN

MTN 38GB DATA KYAUTA




Kamar yadda muka sani Akullum mukan kawo Abubuwan chigana a wanan dandali namu to yau ma Allah yasake dawo dani Akan wani Sabon package
Mai suna mtn Data Roaming




Wanan wani tsari ne da yake baiwa dukkan customer na
Mtn damar samun data kyauta batere da ka biya ko sisi ba kamar yadda aka saba a baya idan zaka samu data sai ka biya kudi wani naira dari wani dari biyu har Abu da ya sawwaka to yau nazo muku da wata sabuwa batare da kosisin kaba zakasamu data kawai

Ba sai na ja kuda dogon zangon labarai ba ba wani wahala ko zagaye kawai kashiga Dial pad din wayar ka ka danna *131*5*7*1# ku kasan che damu domin samu yadda ake Duba data balance din na ku har kullum NAIMISMO1 Muhuta lapiya
Read More»

Sunday, June 2, 2019

* 'YA MACE KYAUTAR ALLAH 3 *

👩🏻'Ya *Mace* Kyautar Allah🌸👩🏻

A true life *love* story

By *Ashmaad*

3.....

Kallon juna sukai snnan maryam tace "saiki ki kkri nxt class dinshi kixo dawuri sabida course din mutuminnan naada wahala, tana fadin hka ta miqe tashi muje masallaci muyi sallah mutafi gda, masallaci suka shiga sukai sallah suna idar wa ta dauki wayanta sabida tunda take sallah taji yna vibrating, missed call din Sadiya tagani saita dubi maryam tana cewa " kinga drivern mu yaxo saimun hadu gobe, har ta wece sae ta kuma dawowa" what tym Muke da lectures Cox bbu tym table a gurina" 8:30am ki kkri kixo dae da wuri don matar itama da xarar tashiga to bbu wanda xai shiga, godiya tae Mata sukai sallama, tana fita sukaci Karo da jiddah "dallah mallama kixo mutafi tuntuni muke jiranki sallah kamar kina hadawa tun daga subhi,  harararta afeefah tayi tai wucewarta ta shige motar,

Basu fita daga motar ba har sae da drivern ya ijye motar a parking space snnan suka fita, afeefah ce karshen fita koda ta fito saita nemi su jiddah tarasa wanda suna fitowa da sauri sukai cikin gida, ta6e baki tae tana tafiyarta a hankali kamar wadda kwae ya fashe mawa, tana stepping qafarta cikin gidan taji an fuxgota da sauri ta juya tana fadin yaya adnaan me kuma nae? "kewae yaushe xaki wayo?  Sisters dinki kowacce saida ta gaidaani kafin suka shiga gida, amma kina ganina kika dauke Kai wlh saina saisai ta maki tunani a cikin gidannan, tuni hawayen dake idonta suka soma bin kuncinta daidai lokacin Aliyu yashigo da sauri ya rungumeta "Adnaan! Adnaan!! Adnaan!!! Kaji na kiraka sau uku, wlh idan baka fita harkar afeefah ba ranka xae baaci, Akan wani dalili xaka tasata gaba tuntuni na lura kap cikin yarn gdannan kafi sa mata ido matsawar ka cigaba da takurata wlh ranka baxai kyauba" am telling  u this, shikam mamakin duniya duk suka isheshi ya rasa dalilin dayasa Aliyu ke haka bbu dama yaji anamata fada, Amma idan shi yatashi mata bbu mai cewa don me

Tana shiga daki ta nufi bathroom tae wanka, kaya mara nauyi tasaka jikinta ganin yamma tayi dakin ma'mi tashiga ta gaidata "ya makarantar afeefah? Cewar ma'mi,... Hmm!!  Ai ma'mi yaukam ban samu lecture din safe ba, ina xuwa na tarar da lecturer a cikin lecture hall din duk a tunanina shima mutumin bai bari a shiga idan ya shiga ashe shi baya Koro, ma'mi tace to baki samu wasu sun nuna miki ba?  Nasamu handout din nai photocopy cikin ikon Allah sai muka hadu da lecturen ya  koya mana har muka gane "masha Allah" gobe ma kya kara Komawa baccin asbah, don ya koya maku yau bashi xaisa nxt tym ma ya koya makuba, gara kudinga hakura da baccin asbah a'ah tou

Washe gari  da wuri suka shirya don basu jira yin breakfst da yan gida ba, har ta nufi kofar Aliyu saita tuna Jan kunnen daya mata akan tashinshi bacci Sai tajuya tama su ma'mi sallama suka fita, duk da irin sammakon da tayi saida ta tararda lecturer din harta shiga, duk da tasan baxata barta ta shiga ba kuma koda tashigan ma sai ta korota hakan baisa taqi shiga ba, bin ta da kallo lecturer tayi har ta xauna snn a nutse tace "Get out" mikewa Afeefah tayi lkci daya hawaye ya cika idonta ta fice da sauri daga class din, karkashin wani bishiya ta samu ta xauna ta dinga hawaye, ta kusa minti goma a gun tana kuka ta ji murya a gefenta ta juya da sauri tana kallonsa, wani matashin saurayi ne da baxae wuce shekaru ashirin da shidda ba, da damuwa yace "me ya faru kike kuka" share hawayenta ta shiga yi da sauri ta mike ta bar wajen kmr munafuka, ta fara tafiya da sauri da sauri don ma kar ya biyota wae, sae da ta dan yi tafiya me nisa snn ta soma waige waige ko xata ga ya biyota, karo ta kusan ci da mutum ta koma baya a tsorace, a dan fusace yace "watch were yhu re goin" shiru tayi tana kallonsa shi ma kallonta ya tsaya yi, "me yasa baki shiga lecture ba?" Tambayar da yyi mata knn, ta sunkuyar da kai ta gaishesa da ladabi ganin lecturansu na jiya ne, bae amsa ba ya kuma jefo mata tambayar da yyi mata, lkci daya hawaye ya soma cika idonta tace "matar ta Kore ni" strictly yace "wat did I tell yhu yesterday?" Kmr xata yi kuka tace "wllh da wuri na xo fa" hawaye ne ya shiga sin
Read More»

* 'YA MACE KYAUTAR ALLAH 4 *

👩🏻 'ya *Mace* kyautar Allah🌸👩🏻
  A true life *love* story

   By Ashmaad
 
4..... 

"Why are yhu late yau ma? ina ne gidan ku?" Tambayoyin da ya jefo mata knn suna cikin tafiya, A hnkli tace "jan bulo" ya juya yana kallonta yace "nan nn jan bulo shine baki xuwa da wuri" shiru tayi bata ce komae ba, ya ci gaba da tafiya yace "me kuke da next ynxu?" Ta ce "ni bani da timetable" ya juya ya kalleta yace "to tafi class ki duba" ta gyada masa kai snn ta nufi lecture Hall dinsu, bakin hall din suka hadu da Maryam, da damuwa Maryam tace "yau ma baki xo da wuri ba" Afeefah kmr xata yi kuka tace "kuma fa wllh da wuri na tashi" Maryam tace "to ki dae dinga daurewa seven xuwa seven thirty ki shigo sch, kinsan wasu lectures basu da mutunci" Afeefah tace "to" Maryam tace "muje kiyi photo copyn handout" bin ta Afeefah tayi suka nufi wani shigo suka gama photo copyn, Maryam ta shiga gwada mata abinda aka koya masu, sha daya saura minti goma Maryam tace "kin ga tashi mu je cafeteria yunwa nake ji, kinsan bana breakfast kafin in fito" Cafeteria suka nufa Maryam tayi masu orderin jollof rice da nama plate biyu sae soft drink, Afeefah tace "ynxu cikin mutanen nn xa mu ci abinci, ni dae kunya nake ji" Maryam tayi dariya tace "lallai, hala baki yi boarding bne" Afeefah tace "kallon mu fa xa ayi" Maryam tace "kin ji ki wa xae kalle ki, kowa na ta cikinsa" Da kyar Afeefah ta ta ci abincin tana duka kai wae ita kunya, Maryam sae dariya take tace "Xa ki daina ne yarinya"
   
Sae da suka yi sllhn Azahar snn suka shiga next lecture dinsu, ssae ta maida hnkli a lecture din har suka gama wajajen uku da rabi, Maryam tace su jira ayi la'asar snn su tafi, a masallaci suka hadu da su Sadiya da Jiddah, Afeefah tayi introducin yayyin nata wa kawarta Maryam, suka gaisa. Karfe hudu da minti goma drivern gidansu ya xo, Afeefah ta tilasta Maryam su je a rage mata hanya tunda hanyar daya ne, da kyar ta yrda shi ma sae da su jiddah suka sa baki, sun kusa inda motarsu ke Parke driver na jiransu ta hango lecturan su, da alama shi ma gida xae wuce, rasa sunan da xata kirasa da shi tayi don bae ganta ba, can tace "Sir" juyawa yyi suna hada ido ta sakar masa murmushi hade da daga masa hannu tace "sae gobe" murmushi yyi shi ma ya gyada mata kai, snn ya karasa gun motarsa ya shiga, su ma suka shiga ta su motar suka bar makarantar, a hanya Maryam tace gun nn xata sauka, drivern yyi parkin ta fita snn tayi ma yayyin Afeefah sallama, Afeefah ta daga mata hannu snn drivern ya ja motar suka nufi gida.
 
Da daddare suna xaune falo suna kallo da Mami, Abba ya shigo gidan, duk suka yi masa sannu da xuwa, hnklinsa duk na kan Afeefah da ta hade rae, ya karaso falon yace "ya aka yi dota, me aka maki" cikin shagwaba tace "ba kai ne ba baka tambayeni ya karatu ba" dariya yyi yace "to ae bacci kike kafin in dawo, in xa ki tafi kuma baki shigowa sallamata" Mami ta tabe baki, Adnaan ya mike ya bar falon, su Sumayya kam dariya suka soma yi, Abba yace to tashi mu je ki gaya min ya karatun, ta mike da sauri ta bi bayansa suka nufi sama xuwa falonsa.    Karfe goma saura Afeefah ta fito daga falon Abba, dakin Aliyu ta nufa, ta samesa xaune yana danna laptop, ta hade rae tace "yayanmu baka tambayeni ko am enjoying my new sch ba" ba tare da ya kalleta ba yace "OK, Afeefah are yhu enjoying ur new sch" shiru tayi tana kallonsa kmr xata yi kuka, ya dago kai yace "ko ba shknn ba" juyawa tayi xata fita yyi dariya yace "srry little sis, xo ki ban lbrin experience din ki a higher institution" dawowa tayi ta xauna ta shiga basa lbrin abubuwan da suka dinga faruwa tun daga ranan da ta fara Bayero, kwata kwata hnklinsa bae kanta kawae yana amsa mata ne, hkn yasa tace "wayyo yayana ba ji kke ba" ya dago da sauri yace "ohh ina ji mana sis" tace "tohm, a day 15 xa mu tashi ko?" Kai ya gyada mata duk da bae sani ba, nn ta shiga basa lbrin lattin da tayi da tsoron shiga aji da tayi da kuma abinda lecturan yace mata da ya fito, ssae ya mai da hnkli a nn, har ta kai karshen lbrin a day 16 wato yau knn, yyi shiru yana kallonta sae washe hakora take tana jiran jin comment dinsa, ya girgix
Read More»

* 'YA MACE KYAUTAR ALLAH 2 *

🌸👩🏻 'Ya *mace* Kyautar Allah'🌸
   
A true life *love* Story
 
By Ashmaad

   2....  Washegari da safe Afeefah da sauran yayyinta suka gama shirin tafiya makaranta don duk Bayero suke, suka sauko kasa gaba daya don yi breakfast, su Sumayya dama bakwae da rabi suke barin gidan, tea kawae Afeefah ta hada, ita a dole fushi take tun kan abinda ya faru jiya, bbu Wanda ya kalli inda take, Adnaan sae watsa mata harara yake ganin bata gaishesa ba ta kuma ki gaishesan, ya gama shan tean sa ya mike don shima yyi shirin xuwa aiki ne da yake Banker ne shi, Kudi ya ciro a aljihunsa dubu biyu ya mika ma jiddah yace "ga wnn ke da sadiya ku kara a kudin break yau" Afeefah ta shiga mitstsika ido murya can kasa tace "ina kwana yaya" harara ya galla mata yace "wnn kuma da wa take" mikewa tayi da sauri tana kkrin boye dariyarta ta kamo hannunsa tace "wllh ni ma sae ka bani yaya" ya fixge hannunsa yace "da'alla" su Sadiya suka dinga dariya ta fashe da kukan karya ta rungumesa tace "ni wllh yaya kana ganinsu ko" murmushi yyi ya ciro duba daya ya mika mata ta washe hakora tace "ngdd yayana" yace "ayi karatu da kyau snn ya fice rike da briefcase dinsa don ya sallami Mami, Abba bae yrda sun sa gyale su fita ba don hka dukkansu da Hijab suke xuwa sch, Afeefah ta nufi dakin Aliyu ganin bata gansa ba tun da ta sauko ta gansa kwance yana bacci har lkcn, ta isa kusa da gadon ta dan yi kara ya bude ido da sauri tace "yayanmu xa mu tafi" harara ya galla mata yace "nace ki daina tashi na idan ina bacci" ta turo baki ta juya ta fice daga dakin, Driver na ajiyesu makaranta duk suka kama hanyar Faculty dinsu, Afeefah da ko sati biyu bata yi da fara Bayero ba taji duk makarantar ya isheta, lecture Hall dinsu ta nufa tayi mmkin ganin har an soma lecture, ta karasa gun kofar shiga lecture hall din ta tsaya kmr munafuka don bata manta me Aunty Safiya tace mata ba wae idan ka xo ka tarar lecturer ya shiga class to kadda ma ka sa ran shiga lecturen ranan don koro ka xae yi, lecturan da baxae wuce shekaru talatin da biyu ba ya daga kai yana kallon ta, ta dauke kai da sauri ya ci gaba da lecturing dinsa, har aka kai karshen lecture din Afeefah na tsaye inda take, ya bada assignment snn ya kwashi takardunsa ya fito ta basa hanya da sauri, yana kallonta yace "me yasa ba ki shiga lecture ba?" Kmr xata yi kuka tace "idan na shiga xa ka Kore ni" Murmushi yyi kawae ya wuce, ta nufi wani karkashin bishiya a sanyaye tana tunanin shknn bata samu lecturen safe ba, wata yarinya ce ta xauna gefenta tace "Baki shigo lecture ba kika tsaya bakin kofa, ae wnn lecturan baya kora da kin shigo" Afeefah tace "haba" yarinyar tace "wllh kuwa, ga handout din da ya bada sae kiyi photo copy, ya sunan ki" Afeefah tace "sunana Afeefah" yarinyar tace "ni sunana Maryam Sadis" Afeefah tayi murmushi tace "nyc name" Maryam ta mike tace mu je kiyi photocopyn," Afeefah ta mike ta bi bayanta suka nufi shagunan da ake photocopy. Karfe uku da minti sha biyar suka fito daga lecturen su na karshe ranan, Maryam tace "mu je mu dan sha drinks kafin lkcn sllh yyi" wani cafeteria suka nufa suka karbi drinks biyu suka xauna suna sha suna hira kmr da can sun saba, Afeefah tace "to dan koya min lecture din da ku ka yi da safe mana idan kin gane" Maryam ta bude handout din tace "nima fa ba wae na gama ganewa ne ssae ba don ni course din wahala yake min, amma bari in maki bayani iya in da na gane" bayani Maryam ta shiga yi mata da farkon handout din kmr ynda lecturen yyi masu, murya suka ji daga gefensu duk suka juya suka juya gaba daya, lecturan course din suka gani xaune shima da drink a gabansa, yana kallon Maryam yace "idan lecturer yyi maku lecture ba ku gane ba, tun a ajin ya kamata kuyi tambaya ya ganar da ku" Maryam tayi murmushi cike da jin kunya bata ce komae ba, Afeefah ma ta sunkuyar da kai, mikewa yyi ya dawo spare kujerar dake kusa da su ya xauna, ya karbi handout din ya shiga masu bayani gaba daya har sae da ya tabbatar sun gane, godiya ssae suka yi masa barin Maryam, ya sakar masu murmushi yace "yhu re all welcm" yana kallon Maryam yace "ya sunanki?" Tace "sunana Maryam," ya gyada ka
Read More»

*'YA MACE KYAUTAR ALLAH 1 *

🌸👩🏻'Ya Mace Kyautar Allah🌸👩🏻

    A true life *love* story.

By  *Aaashmad*

Page 1....

Ban kade kofar da'akayi da karfi ne yasa su saurin juyawa don ganin ko waye hka, *Afeefah* ce ta shigo tana zum6ure zun6ure hawaye cike idonta ba tare da ta bi ta Kansu ba ta nufi hanyar daki da sauri, A fusaace ya daka mata mugun tsawa yace "ke xo nan" a sanyaye ta dawo hawayen da ke cike idonta ya shiga gangarowa fuskarta, *Adnaan* dake xaune gefen babban yayan nasu yyi tsaki yace "kedai gabaki daya rayuwarki ba ki da aikin yi sa na kuka koh? A hka nake ga xa ki qare koda yake ma banga laifin ki ba samun waje kika yi wllh, wawiya kawae" muryar *Ma'mee* su ka ji a falon ashe har ta shigo basu sa ni ba, a fusace take cewa " ke wllh idan baki dinga kama kanki a gidan nn ba sae kin dinga shan mamaki na, hka kawae xa ki sa mutane gaba da kuka a gida, ke yarinya ce ko uwarki ce ta mutu ko uban ki?" Adnaan yace "tambayeta dae Ma'mi, shegantaka kawae don ta ga ba a dukanta, ni da ma xa ki ban izini in saita mata xama a gidan nn" Aliyu kam shiru yyi don kwata kwata bayaso yaji ana wa yar kanwartasa fada shima bada son ranshi yai mata ba, bai ankara ba yaga ma'mee ta daga hannu xata kaiwa Afeefah da ke tsaye gun tana kuka har da shessheka duka, aikam yai xumbur ya miqe yana fadin "ma'mee don Allah kiyi haquri karki daketa kibarni da ita kawai," Adnaan da ransa bae masa ddi ba yace "haba yaya aida ka bari ta kai mata koda daya ne xata maida hankalinta," A tsawa ce Aliyu yace "shut up" ba'shiri kam ya maida sauran maganganunshi ciki yana hararan Afeefah, Aliyu na juyawa yaga babu ma'mee a gurin, janyota yayi ya shiga lallashinta dakyar ya samu ta haqura snn yace ta wuce daki, adnaan kam banda ta6e baki babu abinda yake, miqewa tai tanufi sama tana share hawayenta tashiga dakinta ta kwanta tana maida ajiyar xuciya tana tunanin abinda xata yi ma yayyin nata don rama abinda suka mata taji ddi, bude kofarta da akayi ne yasa ta dago kai don ganin ko waye *jiddah* ce tashigo tana dariya tana fadin "yar lelen yayan mu yau de mun ganku a raana muna labe mun ga duk abinda ya faru, aikam charaf afeefah ta dauka " to sai me? Bai isa yamin fadan bane? kuma ai gwara ni koda munyi fadan a ranar xamu shirya ku fa?, kuma kan ya doke ni ko ya min fada sau daya ku ya maku sau hamsin, xa ki xo kina wani gaya min maganar bnxa sae kace ba ku ku ka ma janyo min ba, kuma wllh sae na rama kmr xata yi kuka ta kare maganar, Daga mata hannu jiddah tai alamar ya isheta "ya isheni haka futsararra dama indai gurin fitsara ne ke gwanace," anyi fitsarar cewar *afeefah* ai ban gayyaceki dakina ba daxa kixo kidinga gaya man magana.A fusace jiddah ta bude qofar tabar dakin, tana fita Afeefah tabi bayanta don ta san inda xa ta, dakin Mami suka nufa gaba daya, Jiddah tace "Mami kina ganin Afeefah daga na mata mgna sae ta kama yi min rashin kunya ko" Mami ta daga kai tana kallon Afeefah, Afeefah ta fashe da kuka tace "Mami wllh su suka fara tsokana na daga mutum yyi min fada a hanya sae su kama min dariya dukansa" Jiddah tace "to Mami tafiya fa take bata kallon hanya saura kadan machine ya bugeta shine wani mutumi ya fara mata fada....." Tsawa Mami ta daka masu tace "duk ku bar min daki na" suka juya suka fita har lkcn Afeefah na hawaye.       
   Afeefah 'ya mace ce ta biyar ga Hajiya Zuwaira snn kaninta uku su ma duk matan, Alhaji Umar mai gidanta dan kasuwa ne da ke xaune Kano da iyalan nasa, mutum ne shi mai rufin Asiri sosae tunda ya wadata 'ya yansa da komae bbu abinda suka rasa na rayuwa, Hajiya Zuwaira da suke ce ma Mami ita ce matarsa ta biyu, bayan  rasuwar Uwargidansa kuma uwar 'ya yansa Maza wato Aliyu da Adnaan, a lkcn Mami na amarya bata fi watanni biyu a gidan ba don da cikin Adnaan ta xo ta sami uwar gidan tasa, Aliyu kuwa na da shekaru biyar a lkcn, tunda ta shigo gidan bata taba samun matsala da matarsa ta farko ba Hajiya fateema har xuwa lkcn da Allah ya karbi ranta bayan ta haifi Faisal da ake ce ma Adnaan da kwana biyu, ssae mutuwar Hajiya fateema ya girgixa Alhaji Umar da amaryarsa Mami, Mami ce ta yi rainon Adnaan da madara har yyi wayo
Read More»

KALAMAN SACHE ZUCIYAR BUDURWA A CHIKIN SAUKI

  SIRRIN YADDA AKE SACE ZUCIYAR  BUDURWA  DUK GIRMAN KANTA DA KUMA JAN  AJINTA!!!  Sanin kowa ne jindadin rayuwa  sai mutum ya sami irin Macen da yake so  sannan zai gane a dadi yake ko a  wahala.  Ta yaya zaka shawo kan macen da  kake so ka rayu da ita?  To dakata! Ita dai mace da kake gani, daga  'yar shekara 1 zuwa 100, ma'aunin  tunaninsu daya ne.  Harshenka da kwakwalwarka,  makamai ne masu karfin da har yau mace bata  mallaki garkuwar  kare hare  harensu ba.  Idan kana so ka sace zuciyar  budurwa da kalamai, wadanda zasu  ratsa ta duk jikinta  su sami tabbataccen wajen zama a  zuciyarta ya zamana ba mai fada  mata taji in bakai ba, koda kuwa  iyayenta  ne, to kalmomi ne guda bakwai 7 zaka  kiyaye.  Dasu mace take jin lallai ta sami  masoyi, matukar taji su cikin  bayanan ka  da kake mata. Mace tana so taji wadannan  kalamai ta bakin duk namijin da ya  tsaya a  gabanta  domin neman soyayyarta. Kuma  dayawa daga matan basa gane ya akai ka  iya sace mata tunani da zuciya.  Karkayi kasa a gwiwa, daka ga  mace kana so kai tsaye ka tunkare  ta ba da  wata fargaba ba. Kana zuwa, dama fuskarka a  sake take kamar kaga na gida.


Read More»

YADDA AKE TUNKARAR BUDURWA

Idan kaga 'yar budurwa tana tafiya sai kaga tashiga zuciyarka kuma kanason yi mata magana..
(1)dafa rko dai ka tabbata kaima kahadu ma'ana kadau wanka mai kyau saboda wanka yana daya daga ckn abunda ke sato maka zuciyara mace..sai karka yi mata magana sai ka tabbata tazo dai dai gurin da babu mutane sosai don wata tana da alkunya.
(2)daka karasa gurinta dakaje sai kafara yi mata sallama kamar yanda addininmu yatanadar nasan indai ta cika musulma zata amsamaka kaga kasamo hankalinta kenan.
(3)sai kace ranki yadade kiyi hakuri fah nasan ba mutuncin kyakkyawar mace mai haiba da asali bane tatsaya ta kula namiji a yayin datake tafiya izuwa wani guri,amma kiyi hakuri nima bayin kaina bane wani sashen bangaren jikinane ya uzuramin dole sai nayi hakan tun yayin da idanuwana sukai arba da wannan kyakkyawar surar taki.
(4)kar dai incikaki da surutu nasan kina sauri ne saboda haka nake neman wata alfarma guda 2 zuwa 3 agunki.

Read More»
Follow Admin On Twitter naimismo1
Join Our Newsletter