LABARIN WANI MUTUM DA YA BUGI MATAR SA.
Ya kasance cikin tsananin fushi bisa abinda ta aikata a gare shi na ba daidai ba a ranar, daga ƙarshe ya kasa haƙuri har sai da ya duke ta duka mai tsanani.
Bayan ta gama 'yan koke koken ta ne ta tashi zumbur kamar mai shirin miyar da martani, cikin fushi ya tambaye ta, ina za ki tafi?
Kuma me za ki yi?
Ta kalle shi a wulaƙance sannan ta ce, zuwa zan yi in kai ƙarar ka.
Ta yaya za ki fita daga gidan nan alhali duk ƙofofi da tagogi suna rufe?
Ya faɗi hakan tare yin dariyar mugunta, ta dube shi cikin murmushi sannan ta ce, ai waya zan buga.
Ta yaya za ki buga waya bayan wayoyin ki duk suna tare da ni?
Ya ba ta amsa.
Koh kula shi ba ta yi ba, kai tsaye ta wuce banɗaki (bathroom) sai ya zaci koh za ta fita ta taga (window) ne don haka ya yi sauri ya zagaya koh zai ga fitan ta domin ya dakatar da ita.
Ya ɗauki dogon lokaci yana tsaye amma bai ga yunƙurin fitowar ta ba, nan ya yanke shawarar komawa cikin gidan.
Bayan shigowar sa ne ya tarar ta fito faca faca da ruwa, bisa ga dukkan alama alwala ta yi.
Ya dube ta cikin mamaki sannan ya ce, wai me kike shirin aikatawa ne?
Zan kai ƙarar ka ne a inda rufe ƙofofi, tagogi da ƙwace waya ta ba za su taɓa zama katanga tsakani na da shi ba, zan kai ƙarar ka ne gurin Allah.
Nan take ya ji nadama ya lullube shi.
Ta fara sallar ta ba tare da ta kula shi ba, yayin da ta kai ga rukunin sujjada sai ta tsawaita, abinda ya tayar masa da hankali matuƙa kenan.
Haka ta ci gaba da tsawaitawa cikin sujjada har ta idar da sallar.
Ta ɗaga hannaye sama za ta fara addu'a kenan ya yi laraf ya cafe hannayen ta, nan ya fara kuka yana ba ta haƙuri yana cewa, wallahi sharrin shaiɗan ne.
Dubi yanda ki ka tsawaita cikin sujjada kina addu'a a kai na, wannan bai ishe ki ba har sai kin sake yin wata addu'ar?
Ta kalle shi cikin tausayawa sannan ta ce, a kan menene za ka dakatar da mace daga yiwa mijin ta addu'a?
Ka sani ya kai miji na, ina yin addu'a ne da kyakyawar zuciya gare ka, ina roƙon Allah ya raba ka da wannan shaiɗani da ya ke tunzura ka har ka ke ƙoƙarin watsa gidan ka alhali ba ka sani ba, ina roƙon Allah ne ya kawar da duk wani saɓani tsakanin mu sannan ya kawo zaman lafiya mai ɗorewa tsakani na da kai masoyi na.
Nan ya ƙara sautin kukan sa, ya faɗi gurfane a gaban ta yana roƙon gafarar ta, daga yau babu dalili da zai sa in sake ɗora hannaye na a jikin ki da cutarwa, wallahi na yi alƙawari masoyiya ta, ki gafarce ni don Allah, hakan ba zai sake faruwa ba Inn shaa Allah.
Ta dube shi a natse sannan ta rungume shi ta na mai cewa, wallahi ba ni da kamar ka masoyi na, ka shaida na yafe maka kuma ina roƙon gafarar ka bisa kuskure na, Inn shaa Allahu ba zan sake ba.
Haka suka kasance rungume da juna tare da ɗora nadama cikin zukatan su bisa kuskure da kowannen su ya aikata. Duk wanda ya yi rashin masoyin gaskiya haƙiƙa ya yi hasara babba, Allah ka bar mu da masoyan mu.
Tambaya :
1. Wane darasi ku ka ɗauka cikin labarin?
2. Sannan me ya fi burge ku cikin labarin?
Tushe : ﺭﻭﺍﺋﻊ ﺍﻟﺸﻌﺮ ﻭﺍﻷﺩﺏ ﺍﻟﻌﺮﺑﻲ

No comments:
Write comments