Tuesday, December 11, 2018

Home KIWON LAFIYA
..

Ana buqatar mace ta kula da kiwon lafiyar kanta, dana Maigidanta da kuma ‘ya’yanta dai-dai iyawarta. Wannan kulawar kuwa ta shafi duk abubuwan da muka ambata a baya, kamar na babin tsafta dss. Saboda haka Uwargida ta guji yin sakaci akan abinda ya shafi lafiya don yin hakan zai taimaka qwarai wurin habakar arzikin Maigida da kuma samun nutsuwa da kwanciyar hankali.
Abubuwan da za’a kula dasu sun hada da:
1. Yawan tsafta
2. Nisanta da kawar da duk wani abu da zai jiwa yara ciwo
3. Rashin sakaci da kayan wutar lantarki kamar su ‘heater’, ‘electric stove’, dss, ka da asa su a jikin wuta kuma a kwanta bacci ko a fita wajen hira dss.
4. Duk abinda zai kawo hatsari a nisanci ajiyeshi a wajenda yara zasu iya dauka, kamar su ashana, kalanzir, fetur dss.
5. Kulawa da yanayin abinci
6. Gudun shan kowanne irin magani musamma idan ba qwararren likita ne ya rubuta ba
7. Bin dokokin da aka bayar akan magani
8. Qoqarin amfani da maganin kashe qwari kamar su sauro, kyankyaso, quda dss.
9. Lura da yara wajen qoqarin yanke musu farce, aski, kitso, wanke kai dss.
A taqaicen taqaitawa wannan shine ‘dan abinda Allah ya nufa a rubuta, kura-kurai masu dimbin yawa Allah ya gafarta mana ya kuma sa mu dace da bin Sunnah, abinda aka yi dai-dai kuma Allah ya bamu ladan shi amin thumma amin..

BY NAIMISMO1
No comments:
Write comments

Follow Admin On Twitter naimismo1
Join Our Newsletter