Abinda ake nufi da zamantakewa shine mace ta zama mata ta gari, mutuniyar kirki wacce duk al’umma suka shaideta da mutuntaka a zamanta na aure. Kula da Maigida, yara, iyayen miji da kuma malamanta da ma sauran mutane baki daya.
Daga cikin abubuwan da zasu taimakawa mace ta zama ta gari sun hada da :
1. Bin dokokin aure
2. Bayar da haqqoqin aure
3. Kyakykyawar mu’amala da miji, ‘ya’ya, iyayen miji, dangin miji da sauran jama’a, mu sani duk wanda ya auri mace to fa ya aureta ne harda danginta, kamar yadda itama ta aure shi ne harda danginsa.
4. Haquri da yawan yafiya tare da kawar da ido akan wadansu abubuwa.
5. Neman shawara daga mutanen kirki, masu hangen nesa da nutsuwa da kuma aiki da shawarar da aka bata.
6. Baiwa Maigida shawara a kebance, ma’ana ba a cikin jama’a ba, kinga ko da bai karbi shawarar ba abin ba zai zamo matsala ba.
7. Rashin saurin fushi da kuma qoqarin kawar da fushi, kamar yadda yake a maganar Mazon Allah S.A.W : Idan kayi fushi idan kana tsaye to ka zauna, idan kuma a zaune kake sai ka kwanta, kuma kayi alwala.
8. Baiwa Maigida cikakken saurare, ki zama mai kyakykyawan saurare.
9. Sallamawa ga shawararsa matuqar bai sabawa Allah da Manzonsa ba, da kuma rashin jayayya da shi, sabanin wasu da qawayensu ne kadai keyi musu jagora da zuga.
10. Kiran Maigida da suna mai dadi ko kuma sunan da yafi so (kamar su sweety, darling, honey, angona, maigidana, nawan, my only one, Sahibina, sirrin zuciyata, hasken idona dss), kamar yadda Manzon Allah S.A.W yake kiran Nana A’isha da Ayish !
11. Yiwa Maigida kyautar bazata, kamar tufafi, abinci, abinsha, ‘greeting card’, turare da kuma yafiya akan laifi mafi girma wanda yake zaton za’ai tashin hankali akai.
12. Ki zama kina kiyaye harshe, tare da lura da abinda zaki fada, domin Manzon Allah S.A.W yace harshe zai jefa mutane a cikin wuta.
13. Yiwa Maigida uziri a inda ya gaza da nuna masa godiya ga duk abinda yayi ko ya kawo.
14. Qarfafa masa gwiwa wajen qulla zumunci da ‘yan uwansa, kamar iyaye dss.
15. Yawaita hira da shi da irin abinda kika san yafi daukar masa hankali ko kuma yafi so.
16. Yabonsa a gaban iyaye, ‘yan uwa tare da jinjina masa
17. Taimaka masa a gurin girmama iyayensa da naki
18. Kyautata zato a gareshi da kuma rashin dogon bincike a gareshi, kamar bincike a wayarsa (handset) da shiga cikin saqonninsa (messages) dss.
19. Karki fifita abokan miji akan miji, ballantana qawayenki!
20. Ki riqa nunawa Maigida cewa yana da hikima da dabara a cikin al’amuransa.
21. Mantawa da abinda ya wuce don baya jawo komai sai bacin rai
22. Tunawa da shi a cikin addu’a
23. Kulawa da ‘ya’yansa wadanda ba ke kika haifesu ba.
24. Ba da kyauta ta mamaki ga iyayensa ko wadanda suke a matsayinsu
25. Kulawa da wurin kwanciyarsa da kuma koyan salo daban-daban na kwanciyar aure, tare da tausaya masa idan kina al’ada, in har kina da abokiyar zama ki bashi damar ya tafi koda bai nema ba, in kuma ke kadai ce to ki bi hanyoyin da zaki kawar masa da sha’awa wadanda shari’a ta yarda da su.
BY NAIMISMO1











No comments:
Write comments