Hakika So,
Dafine So,
Gubane So,
Masifane ga wanda Allah Ya jarabe shi.
Hakika So wata Yanace dakan makantar da idanun
massoya gabarin gani. So shine abu mafi girma dake iya sarafa zuciyar ko
wane irin mutum.
So wani haskene dakan haskaka zukatan massoya.
So nagaskiya shine ginshikin dorewar soyayya. So nagaskiya shine kaso mutum don Allah badan wani
abu dake tareda shi ba. So Yakan iya zama linzamin ga duk wanda Ya tsinci
kansa a tarkon sa. So wani marurrine dake yawan azabar tarda zukatan
massoya. So wani tsirone dakan iya tsirowa a zuciyar duk Yaga
dama. So ba ruwansa da kyua,kudi,ilimi,mulki, nasaba ko
cancanta. Babu shakka soyayya itace jin dadin rayuwa ga wanda
yayi dace da itah. Lafizin kauna shine abu mafi girma dayadi sausasa
zukatan massoya. Baza ka sataba sanin menene bakin cikin a ko farin ciki
sai alokacinda kake soyayya. Soyayya tadi komai dadi amma tadi komai azabantarda
zukata. Soyayya itace tushen kafuwar aure da wanzarda
zaman lafiya ga massoya. Soyayya da aka ginata da tubalin gaskiya ba zata taba
rushewa ba. Soyayya itace ginshikin jin dadi amma wani lokaci
takan zama illah.











No comments:
Write comments