Friday, December 28, 2018

Home IDAN 'DANKA KO 'YARKA SUN KAI SHEKARUN FARKO NA TASHEN BALAGA, TO KA LURA DA WANNAN:
..
IDAN 'DANKA KO 'YARKA SUN KAI SHEKARUN FARKO NA TASHEN BALAGA, TO KA LURA DA WANNAN:
------------------------------------^------------------------------------

1. Duk lokacin da yaro ko yarinya suka kai matakin tashen balaga wato "early adolescence", musamman daga shekara 11, 12 zuwa 13... 18... To wannan shi ne lokaci mafi hatsari ga yara da iyayensu.

2. A lokacin ne yaro yake samun zama na gari ko na banza, me amfanar da al'umma ko me cutar da su.

3. Yaro ya fi tasirantuwa da abokansa ko kawayenta fiye da malamansa ko mahaifansa.

4. Yaro yana jin shima daidai yake da kowa a duniya, kuma zai iya yin komai kamar yadda kowa yake yi, haka ita ma yariyar.

5. A lokacin ne yaro yake neman 'yanci daga ikon mahaifansa akansa. Yana son dakinsa daban, wajen kwanciyarsa da ban, abinci, kayan sakawa da aski sai wanda ransa yake so.

6. A lokacin ne yake jin karfinsa ya kawo, kuma zai iya ja da kowa.

7. A lokacin yaro komai yana yin sa ne gaga-gaga, ba kan gado babu nutsuwa, kuma ba wanda ya isa ya hana shi (a tinaninsa), idan kuma iyaye ba su bi hanyar da ta dace ba, to za su sha wahala da shi/ita.
-------------------------
-------------------------

MAFITA:
1. Iyaye su ja yaronsu a jiki, kuma su yi amfani da hikima wajen yi masa gyara da tarbiyyarsa.

2. Kar su nuna masa karfi ko iko, domin zai iya baudare musu, a karshe ya haifar musu da hawan jini.

3. A kula sosai da su waye abokansa, ko kawayenta. A hada shi da na gari, a raba shi da na banza.

4. A samar masa da aikin yi, wajen nuna masa yadda zai dogara da kansa (koda kuwa dan masu kudi ne ahi).

5. A tsara masa ayyukan da zai ke yi a kullun tun daga safe zuwa rana, i.e. makaranta, bacci, cin abinci, ziyara, hutu, da sauransu.

6. Iyaye su zama abokan 'yayansu wajen bincikar matsalolin 'yayan, da magance musu ita.

7. Ka da a hana yaro wani abu, face sai a maye masa gurbinsa da wani, idan ba haka ba, to zai yi wanda aka hana shi muni.

8. Kar ayi amfani da karfi, da duka, da tsattsauran hukunci wajen ladabtar da shi, har sai idan abu ya ta'azzara, sai a je da shi guidance and counseling domin neman shawarwari.

9. Ake tunatar da su ayoyin alqur'ani da hadisan Manzo s.a.w. da sukai magana akan biyayyar iyaye.

10. Sannan ake hadawa da addu'ar nema musu shiriya da nagarta a wajen Allah s.w.t.
Wallahu a'alam.


No comments:
Write comments

Follow Admin On Twitter naimismo1
Join Our Newsletter