<<<<<BA A DARIYA>>>>
Wata mata ce tanason ta gwada mijinta; Taga
inhar suka
rabu yaya zaiyi?... Saita dauki takarda tayi
rubutu kaman
haka; "mijina gaskiya bana sonka yanzu jinake na
tsaneka
bana bukatar kallon fuskanka gara na kalli
fuskan goggon
biri da na kalli fuskan ka, bana burin jin
muryanka
gara na saurayi wakar shata da naji muryanka,
dan haka
nayi tafiyata ka auro wata"....... Sai ta ajiye
akan kujeran da
yake
falon sannan takoma bayan kujeran ta buya...
Mijinta yana zuwa yasamu bakowa a falon yana
kokarin zai
kirata sai yaga takarda akan kujera, sai
yadauka yakaranta...
Nan take ya fashe da dariya
sannan ya dauko wayansa yasa akunnensa
yafara cewa, ''Hello masoyiyata abunda muka
dade muna
addu'ar shi yau
yazo. Yanzu nadawo daga wajen aiki na samu
wannan
lalatacciyar matan nawa tabar gidana kinga
sati mai zuwa kawai sai adaura mana aure... Sai
ya fashe da
dariya
yace kijirani yanzu ina zuwa zamu tafi hotel
muci abinci.....''
Bayan yagama maganganunsa sai yajuya
bayan takardar yayi
rubutu sannan ya bude durowa ya canja riga
ya fita yana
waka wannan baitin....
''SOYYAYYA SO MAI SONKA... ZO
MUJE MUJEJEJE MUJE MUJE...." Haka ya fita
yana wakarsa fuskansa cike da
annuri.
Fitarsa keda wuya matar tafito
tana ta kuka tadauki takardan dan ganin
meya rubuta....
Sai taga yarubuta.....;Kidaina boye-boye Kifito
dan nariga na
ganki abayan kujera, kidafamun ruwan tea
yunwa nakeji,
naje insayo biredi.
Wai a Cikinsu wa akafi razanawa?
1=Matar....?? 2=Mijin.....??











No comments:
Write comments