*shawara 1*
Haba maigida ! yanzu in ba ka kwantar wa da Uwargida hankali ba waye zai kwantar mata ?
kana zaman Hira mai shayi abokai.
◾ yan mata
kaji tsoron Allah ka daina aikata wannan dabi'a ka zamo mai walwala da sakin fuska da raha tare da iyalanka.
amma kaje cikin abokanka Ana Washe musu baki ko
yan'mata ,amma ga wacce ya dace ka washewa baki ka rinka saka ta cikin annashuwa.
yawancin mata 80% na yawan hawan jini maza ne
don Allah kubi hanyoyin da zaku zauna da matanku lafiya ka zamo mai ba ta shawara ita ma mai baka shawara. sai a yi ta sha'awa zamantakewar Ku, Ku zama abin koyi a wurin jama'a.
a karshe kuji tsoron Allah kula da matanku , Ku tausaya musu ,sai Allah ya jikan Ku, kuma ya yi musu jagora a dukkan mu'amala.
* shawara ta 2 *
kada ka zagi matarka a gaban ya'yan ka ko yan'uwanka ko a gaban mutane, aikata hakan yakan sa ya'yan cikin damuwa kuma kana zubar mata da mutunci a idon ya'yan ka da yan'uwa ka da sauran al'umma ba laifi ba ne ka yi mata fada amma ba a gaban mutane ba ko ya'yan ka ya kasance idan za Kayi mata fada daga Kai sai ita kuma Kayi shi ta hanyar nasiha ba ka ware baki ba duniya ta ji
musamman ma in tana gidan yawa ko cikin kishiyoyinta wani ma in ya tashin rashin mutuncin sa a gaban akokinsa zai ta hantarar matarsa komai sai masifa da zagi.
shawara ga mata
karki zamo mace mai yawan rokon maigida ko abokan maigida, hakika roko yana debe kima da kwarjini da mutunci na mutum, hakika akwai matan da mazajensu ba sa kirga kudi ko su ba su ajiyar kudi ma nuna musu alama ta suna da da kusin ba sa yi saboda sun San hali, don haka duk mai Neman fada da gindin zama a wajen maigidanki ta daina yawan rokon mutane.
shawara ga mata
kar ki dogara da abin hannun mijinki kice komai sai mai gida yayi miki, hakika a wannan zamanin ki ka ce haka Zaki yi kina tare da wahala don haka ki dogara da Allah ki wadatu da abinda ke hannunki kiyi amfani da shi kar kici ba shi domin shi ba shi musifa ne babban.
ALLAH YA RABA MU DA BASHI
mai gida Inda kasan matarka bata Sana'a Kayi kokarin taimakon ta da abinda zatayi koda bata Sana'a amma wasu mazan basa barin matan Sana'a
kuma basa iya dauke musu duk wata bukatar su irin haka sai kaga mace tana hali Mara kyau.
BABBAN SHAWARA GA MATA
⊂( ̄ ̄)⊃GIRKI SIRRIN MATA⊂( ̄ ̄)⊃
ki zamo mai iya girki da kwarewa wajan hada kayan shaye- shayen karki Bari a miki zarra ta bangaren girke-girke ya zamo mai gida ba shi da tunanin ya ci abinci a wajen ke idan mai gida ya gamsu da abincin Uwargida ko yana kasuwa sai yazo yaci idan kuma aikin yayi masa yawa sai ya turo an karbar masa, amma babu kima aga mijinki yana yawo Neman abinci da safe da yamma ya tura nan ya tura
nan, babu kima in baki iya ba ko baki kware ba sai ki nemi masu koya miki girke-girke kwatowa kanki 'yancin a wajan mai gida ki Sani babu wacce tazo da iyawa kowa koya yake don haka kema sai ki koya domin faranta wa maigida .
SHAWARA GA MATA
ki zamo mace mai riko da addinin musulunci kar ki zamo mai wasa da ibada ki bautawa Allah kamar kina ganinsa ki Sani in kin kasance bakya ganinsa to shi yana ganinki ki maida lamuranki ga Allah karki yi yawan bin BOKA KO MALAM kamar yadda wasu matan suke yi ko bin bokaye da yan bori yin hakan ba zai Kara miki komai ba asara da tabewa..
DON JAWO HANKALI MAIGIDANKI
madarar ruwa.
ayaba.
garin dabino
garin aya.
idan kika sami madara ta ruwa gwangwani daya, sai ki sami ayabarki kamar manya guda biyu ,sai ki yanyanka ta kananan a cikin madara ruwan , wacce kika sami kofinki kika juye, sannan sai ki kawo garin dabinonki cikin karamin cokali sai ki zuba a hadin madararki, sannan sai ki kawo garin ayarki shima sai ki hada ki gauraya shi sai ki shanye.











No comments:
Write comments