TARKON MUTUWA 1
Complete book
typing habibullah kbr
Post AA Misau
BOOK ONE
A wani zamani can baya mai tsawo da ya shude a lokacin da ake yin kashin dankali wato Babba a sama, Kanana a kasa. Ma'ana mai karfi, basarake da attajirai suke cin karan su ba babbaka.
A wannan lokaci zalunci ya yawaita, sam babu adalci, doka bata aiki sai akan talaka, mara karfi da makaskanci.
A daidai wannan zamani ne akayi wata nahiya wacce ta shahara a duniya a harkokin kasuwanci, Karfin mulki da yawan al'umma. Kasar da tafi dukkannin kasashen dake nahiyar daukaka itace Bindal.
Duk wani dan kasuwa dake mu'amala acikin birnin Bindal indai yana son ya tsira da mutincinsa da kuma dukiyarsa to dole yakasan ce dole ribar da ya samu a kullum ya rabata gida uku.
Kaso daya shine naka kaso biyu kuma sai ya kaiwa sarki Shamssal.
Sarki Shamsal ya kasance gawurtaccen jarumi mashahurin mayaki wanda babu kamarsa a nahiyar gaba daya domin a tarihin jarumtakarsa ba'a taba kai shi kasa ba a filin daga kuma ba'a taba yi masa rauni ba a yaki ko a gasar jarumtaka.
Yana iya shafe sa'a goma sha biyu yana yaki ba tare da gaji ba kuma yana iya yin tafiyar kwana bakwai a kasa cikin yin gudu ba tare da ya tsaya ko don ya huta ba sai dai kawai ya daga battar ruwa yasha yana cikin gudun.
Kai idon Sarki Shamsal yayi wani abun jarumtaka sai kaga kamar ba mutum bane ba shi, aljanine komai yawan rundunar mayaka yana iya tarwatsa su ya kashe na kashewa, MASU GUDU SU GUDU don tsira da rayuwar su.
A bangaren zalin ci kuwa masu hasashe sun tabbatar da cewa babu wani Sarki a nahiyar kaf wanda yafi Sarki Shamsal domin shi 'yan uwan sama sarakai cin zalinsu yake yi bare talaka.
Idan ya kyallara ido yaga wani Sarki da kyakykyawar mata sai dai kawai ya aika masa sakon ya kawota da kansa, Idan Sarkin yaki kawo ta zai iya rasa ransa ko mulkinsa don haka yana rawar jiki zai kai ta .
Batun haraji a kan talakwa babu inda aka tsanantashi sama da birnin Bidal ko yaya talaka ya yi laifi yanzunnan sai a zaneshi ko kuma a kai shi kurkuku a yanke masa shekara biyu ko fi,
A ta kaice dai in ban da Sarki Shamsal da fadawansa da kuma ya yan baran darsa da masu yi masa biyayya babu mai kwanciyar hankali a cikin birnin BINDAL.
A can karshen birnin Bindal a bangaren kudu a kwai wani makeri wanda ake kira da suna Satyan
Makeri satyan tsoho ne tukuf domin shekarun sa sunkai dari da biyar kuma tun baifi shekara tara ba a duniya ya kware a harkar kira kuma ya shahara domin gadon sana'ar yayi yana shekara taran mahaifinsa ya rasu kuma yaci gaba da aiwatar da aikin mahaifin nasa Hatta makaman yakin gidan Sarki Shamsal a makerar Satyan ake kerasu ba a taba samun wani sabani ba tsakaninsa da gidan Sarki Shamsal bai taba ganin tsoho satyan ba haka shima tsoho satyan bai taba ganin saba
A karkashin tsoho satyan akwai yara ma'aikata kimanin su saba'in da daya kuma duk suna samun abin da suke rayuwarsu a karkashinsaAlbarkacin kayan yakin da yake kerawa masarautar ne yasa ba' tsananta masa haraji ba,
kuma tun a zamanin mahaifin Sarki Shamsal hakaabin yake wakekana.
Tshoho satyan yana matar aure guda daya wacce itama girma ya kamata domin shekarunta sun kai
saba'in.
Allah ya albarkacesu da 'ya 'ya biyu kacal a duniy,
mace da namiji macen itace babba kuma shekarun ta sun kai ashirin da biyar,
Ana kiranta da suna Sadirat.
Sadirat kyakykyawa dai dai gwargwado mai kyan siffa ta taso da farin jini sosai a wajen samari
amma saboda itace kadai ke taimakon mahaifiyarta a ayyukan gida bata son ta yi aure har sai kaninta Hatyan yayi saboda
Matarshi za ta zauna a gidan ta rinka tai makon mahaifiyarsu,
ita kuwa dauketa za ai akaita wani gida.
Tsakanin sadirat da hatyan bambancin shekaru Hudu ne wato a yanzu Hatyan yana da shekaru Ashirin da daya kacal a duniya.
Allah daya gari bambam , ko kadan Hatyan bai gaji harkar kira ba.
Tunda ya taso da kuruciyarsa babu abinda yake so sama da harkar farauta don haka kusan kullum da koyaushe yana cikin daji,
Tun safe idan ya fita farauta baya dawowa sai rana ta fadi.
Wani ikon Allah kuma sai ya zamana cewa yana da nasibi matuka a harkar domin bai taba fita farauta ya dawo ba wani abu ba sai anganshi ya kamo babbar dabba ko wani babban tsuntsu,
Tun Hatyan na da shekara tara a duniya aka gane cewa sadauki ne domin tun a sannan yake iya gumurzu da manyan dabbobin daji kuma ya kashesu da hannunsa,
Wannan baiwa da Allah ya bashine tasa shi kansa Sarkin farauta na Birnin ya jashi a jikinsa
ya kaunace shi ainun hakannema ya rinka taimaka masa da yansim kan daji dana tsafi domin samun tsari.
A kullum abin da Sarkin mafarautar ke nunawa Hatyan shine lallai ya boye jarumtakarsa kada mutanen gari su sani saboda al'adar Sarki Shamsal itace dayaji ance wani sadauki ya taso a birnin sa saiya tura a sirrance a kasheshi .
Bakomai ne ya janyo hakan ba face bokayaensa sun gaya mashi cewa duk ranar da aka sami gagarumin sadauki mai irin baiwarsa ta jarumtaka da juriyar yaki da gudu a birnin to shine zai
karbi mulkinsa.
Bisa wannan dalilin ne duk dabbar da Hatyan ya farauto da hannunsa a daji ,
Sai ya boyeta a cikin buhu ya kaita gidan sarkin farauta,
shine zai siyar masa da dabbar ya bashi kudinsa don kada agane cewa shine ya kaso dabbar.
Duk sa'adda Hatyan ya shigaa daji farauta baya yarda wani ya ganshi a lokacin da yake gumurzu da manyan dabbobi.
A boye hatyan yake baiwa kansa horon gudu dan sarrafa makami,
Tun yana da shekara goma sha daya idan ya ksa tsere da dabba komai karfin gudunta sa ya kure mata gudu ya rafketa,
Hatyan na iya shafe kwana ashirin yana gudu a daji ba tare da ya tsaya din hutawa ba kocin abinci sai dai kawai yasha ruwa,
Wato dai Hatyan har yafi Sarki Shamsal juriya awajen yin gudu,
Abin da Sarki Shamsal yafi Hatyan kawai shine karfin damtse gami da kwarewar yaki da sanin makama amma kuma hatyan ya fishi zafin nama,
A duniya babu abinda Hatyan ke so da tsananin kauna sama da yayarsa Sadirat domin ko kadan bayason yaga damuwarta kuma ko kuda bayason yaga ya sauka ajikinta da niufin ya taba lafiyarta,
Duk saurayin ko wani dan iskan da ya kuskura ya taba jikin Sadirat da hannunsa to ai ya kai masa ziyarar dare ya sare masa hannu ya maisheshi masaki,
Bisa wannan daliline maza ke tsoron latsa Sadirat,
Wa dan dama suke sonta da aure tsoron zuwa wurinta suke
Lokacin da tsoho Satyan yaga cewa ko kadan dansa baya sha'awar harkar kira sai farauta sai hankalin sa ya dugunzuma ainun saboda tunanin cewa ranar da ya mutu babu wanda zai gajeshi sai dai yaransa shikenan sana'ar tabar gidan,
<<<<< K .A .H >>>>
A kan hakane ya dinga matsawa Hatyan yana son yayi masa dole akan yabar farauta,
Koda ganin haka sai Hatyan yaje ya sanar da sarkin farauta halin da ake ciki,
Da jin hakan sai sarkin farauta ya ta so da kansa yazo gidan Satyan dama can sun kasance abokan juna sai dai shi sarkin mafarauta shekarunsa basu fi tamanin da biyar ba,
Lokacin da sarkin mafarauta da Satyan suka kadaita a cikin turaka kuma suka gaisa sai ya dube shi yace,
"Ya kai abokina kayi sani cewa kowane da yana da irin baiwarsa,
Dan ka Allah bai yishi makeriba, mafaraucine,
Masu magana sunce ranar wanka ba'a boyen cibi to yau zan sanarda kai wani babban sirri a kan danka wanda baka taba saninsaba,
Zidane kd..
A halin yanzu duk fadin garinnan in banda Sarkibabu wani jarumi wanda yafi Hatyan sadaukanta ka,
karfin gudu da juriyar wahala a daji.
Ka sani cewa tun yana da shekara tara yake iya fada da manyan dabbobin daji ya kashesu ya kawo gawarsu ya kawosu gidana a boye ba tare da kowa ya sani ba,
Nine nake sayar masa da abubuwan da ya farauto ,
A yanzu haka ya tara kudade masu dumbin yawan da sun wuce dinare dubu dari biyar amma tsoro yake ji yazo ya sanar dakai ,
Kasani nayi bin cike acikin halarar tsafina na gano cewa wannan yaro naka nan gaba sai ya zama babban mutum a kasar nan don haka idan har sarki ya sami labarin jarumtarsa kashe shi zaiyi,
Babban abinda yafi daga mini hankali shine zafin zuciyar Hatyan.
Ina tsoron ranar da wani abu zai hada shi da gidan Sarauta ,
In dai aka tabashi bazai hakura ba tunda kana ganin abin da yakewa samarin da suke kawowa "yar uwarsa Sadirat wargi,
A yanzu haka ya janyo kowa tsoranta yake ji a garin nan,
Ka tuna cewa Sarki Shamsal yanada azzalumin "Da" yarima Zainur wanda shima shekarunsa basufi na Hatyan ba kuma yana da muguwar al'ada ta yiwa "yan mata fyade,
A garin nan yarima Zainur yayi wa "yan mata sama da guda dari fyade kuma ko magana iyayen "yan matan sukayi sai a kashesu,
Mahaifin sane ya daure masa gindin ya yi duk abin da ya gadama saboda yana sonsa fiye da komai a duniya,
Ina tsoron ranar da yarima Zainur zai yi arba da Sadirat,
na tabbatar da cewa bazai kyale taba idan kuwa ya taba ta sai Hatyan ya yi masa mummunan hukun ci."
Sa adda sarkin mafarauta yazo nan a jawabin sa sai tsoho Satyan ya ji hankalinsa ya Dugunzuma ainun fiye da ko yaushe,
Da ga can sai ya dago kai ya dubi sarkin mafarauta yace
"Ya kai abokina kayi sani cewa dangane da batun Sadirat bani da wata fargaba saboda kullum ta na gida bata zuwa ko ina saboda koyaushe itace keyin ayyukan gida kaga kenan babu yadda za 'ayi ta hadu da yarima Zainur tun da babu abin da zai kawoshi nan.
Ko batun kayan yakin gidan Sarki akwai wakilin kayan wanda shi kadai yake zuwa ya karba,
Ni yanzu kawai damuwata akan Hatyan ce , Me zai hana ka dauke mini shi daga garin nan ka turashi can wani garin wajen irin abokan sana'ar ka yayi rayuwarsa acan,
Ni na tsufa tawa ta kare mahaifiyarsu ma girma ya soma kama ta,
Abinda muke buri kawai shine muga auren wadannan yara kafin ajalinmu,
Ga shi su biyun sun shaku da junansu basa san rabuwa idan har ma za"a dauke Hatyan daga garin nan sai dai a hadasu tare ,
ni ina gani wannan ce kadai hanyar da zamubi mu tserar da rayuwar Hatyan data "yar uwarsa daga sharrin Sarki da Dansa,
Saboda haka a yau idan Hatyan ya dawo daga farauta ka taho dashi mu zauna gaba daya tare da mahaifiyar su mu sanar da su hukuncin da muka yanke,
'Yan kudin da Hatyan ya tara sun ishesu su fara sabuwar rayuwa a wani wurin amma babban shawarata itace subar wannan nahiya gaba daya."
Lokacin da tsoho Satyan yazo nan a jawabinsa sai sarkin mafarauta yaji ya kamu da tsananin tausayinsa har kwalla ta zubo masa ya sunkui da kansa kas yace,
"In da matsalar take shine tayaya kake tsammanin cewa Hatyan da "yar uwarsa Sadirat zasu iya barinku kaida mahaifiyarsu su tafi can wata nahiyar su zauna alhali kuna raye baku mutuba?
Ko da wannan tambaya sai hankalin Satyan ya dugunzima ainun, nan take hawaye ya zubo masa yace,
"Rabuwarmu da su a wannan lokaci itace tafi alheri a tsakaninmu,
idan kuma suka ki su tafi to nan gaba zasu yi tafiyar doke a yayin da babu mu din,"
Cikin rashin fahimta Sarkin mafarauta yace " Nifa bangabe me kake nufi ba"
Satyan yace, " Ba na so ka fahimta din amma dai lallai ka tilasta Hatyan ya dauke "Yar uwarsa su bar nahiyar nan gaba daya kuma su manta damu,
Idan da rabon zamu sake ganawa, zamu gana anan gaba, Ni da mahaifiyar tasu za muyi jiranku idan Hatyan ya dawo daga farauta."
Koda gama fadin hakan sai Satyan ya mike tsaye ya kuma kama hannayen sarkin mafarauta ya tsaheshi tsaye suka kurawa juna idanu sannan yace, nagode abokina , nagode da wannan shawara da kazo mini da ita da kuma wannan sirii na dana daka baiyana mini ,
Tabbas kai masoyine na kwarai bazan taba mancewa da kaiba, Allah ya bar zumunci namu wanda dama tun iyaye da kakanni yake gidan makera da gidan mafarauta mun zama tamkar jini daya,
Kayi iya sani cewa iba ji ajikina cewar bazan dade ba ajalina na kusa dan haka nabar maka amanar iyalina ,
ka yi iya kokarin ka wajen karesu da basu shawarwari na gari,"
Lokacin da Makeri Satyan yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubowa sarkin mafarauta ya rungumoshi yana mai cewa ,
Na rantse da girman iyayena zan rike wannan amana taka hannu biyu har zuwa kashen rayuwata,
Sai da suka dan jima kadan kankame da juna sanu zubar da hawaye sannan Sarkin mafarauta ya janye jikin sa daga jikin na Satyan yayi masa Sallama ya tafi.......Har su yarima Zainur sun hau kan dawakansu zasu tafi kenan sai ga Sadirat ta fito daga cikin gida dauke da ruwan sha acikin tamulan da kofi bisa wani faranti zata kawowa Satyan,
Dama kullum wannan lokaci sai ta kawo masa ruwan sha saboda tu'ammali da yake da wuta a makera
A wannan lokaci Sadirat na sanye da wata matsatstsiyar riga wacce ta bayyana dukkan surar jikinta
Ko da yarima Zainur ya kyallara ido yaga Sadirat sai ya dimauce ya kama hadiyar miyau kamar maijin kishirwa ya dade yana neman inda zai jika makogwaronsa sai yayi katari da rafi,
Nan fa yarima Zainur ya kasa sakarwa dokinsa linzami ya tafi, ya kurawa Sadirat idanu kawai
Ita kuwa Sadirat koda taga ya kura mata idonu sai yayi sauri ta sunkui da kanta kas ta wuce izuwa wajen Satyan ta kai masa ruwan ta zuba masa a kofi kamar yadda ta saba yi masa domin yasha amma sai taga shima ya kasa shan ruwan,
Hannunsa dake rike da kofin sai karkarwa yake kuma sai kallon yarima yake kawai.
A wannan lokacine Sadirat ta tuno da labarin da takeji akan yarima cewar indai yaka mace ya kyasata sai ya yi mata fyade,
Nan itama hankalinta ya dugunzuma ta rasa abin da zatayi,
Lokacin da Zamhas yaga yarima ya dimauce bisa ganin sadirat sai sai ya fara rokonsa akan su tafi ya tuna masa a kan Sarki fa ya gargadeshi kada yayi wani abu daba dai dai ba a wannan gida ,
Duk irin wadannan maganganu na Zamhas sai yarima ya rinka jinsu kamar tatsuniya a cikin kunnensa don haka ko kallonsa bai yi ba barema ya yi aiki da shawarar tasa,
Sadirat ta taso daga gabn mahaifinta Satyan ta zo zata gifta ta gaban yarima domin ta shige cikin gida ,
Kawai sai yarima ya duro daga kan dokinsa ya sha gabanta sannan ya kai hannu ya kamo hannunta ,
Tana waigowa sai ta zabga masa mari,
Cikin tsananin kaduwa dakaru, Zamhas da Satyan suka wangame baki suna mamkin al'amarin,
Ita kuwa Sadirat saita dakawa yarima tsawa tace , "Shin ka zata ni irin 'yan matan da ka saba wulakantawa ne a gari harda zaka taba hannuna,
To ka sani kusantata ba karamin hadari bane agareka sai dai kaje ka nemi wadanda basu da gata ka wulakanta su,
Koda Sadirat tazo nana zancenta sai yarima Zainur ya shafa kumatunsa sannan ya bushe da dariya, lokaci daya kuma sai ya turbune fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa ya dubeta yace,
" Yake wannan 'Yar talakawa kiyi sani cewa ko mahaifina bai taba mari naba.
Babu wani maha luki a garinnan daya taba zagina bare ma ya dokeni amma yau gashi kin mareni a gaban mutane kin muzan ta darajata da mutuncina
<<<<<<<<<<Khaleed>>>>>>>>>>
Toki sani na rantse da Uwata da Ubana yanzu a gaban wannan tsoho naki zan yi miki Fyade kuma na karya wannan hannun naki da ya mareni na sareshi da takobina,
Kafin Sadiray ta yi wani yunkuri guda daya tuni Yarima Zainur yasa hannunsa guda ya maketa a fuska,
Saboda karfin dukan saida ta baje a kasa ta kasa mikewa tsaye ya yin da jini zuba a bakinta,
Ko da ganin abinda ke faruwa sai tsoho Satyan ya mike da sauri domin ya hana Yarima nufinsa ,
Ai kuwa yana zuwa daf dashi sai ya zare wuka ya luma masa a ciki kuma ya doki kirjinsa da karfi ya fadi can baya yana kakarin mutuwa,
Ko da Zamhas yaga abinda ke faruwa sai ya zaburi dokinsa da gudu ya bar sauran dakaru a wajen saboda ya san cewa abinda zai biyo bayan wannan al'amari ba mai kyau bane,
Lokacin da Sadirat ta ga yarima ya cakawa mahaifinta wuka a ciki ya fadi kasa yana kakrin mutuwa sai ta tsandara ihu ta mike zumbur ta ruga gareshi amma sai Yariman ya sake maketa ta zube kasa shi kuma ya kamata da kokawa yana kokarin cire maya tufafi,
A dai dai wannan lokacine Mahaifiyar Sadirat ta fito daga cikin gida aguje saboda jiyo ihun 'Ya ta da tayi ,
Ko da ta fito sai tai arba da gawar mijinta sannan kuma taga yarima ya danne 'Yar ta suna kokawa,
Nan take jiri ya kwasheta ta fadi sumammiya,
Yariam yaci gaba da kokarin yage rigar Sadirat amma sai ya kasa saboda tana kai masa duka da hannayenta harma ta sami nasarar fasa masa baki ,
Ko da ya shafa lebensa yaga jini sai ya fusata ainu ya gabza mata wawan naushi a fuska take ta baje a wajen sumammiya ,
Duk wannan abu da yake yi dakarunsa da suka rakoshi suna kallonsa amma an rasa wanda zai hanashi,
Makotan makeri Satyan kuwa duk sun firfito daga cikin Gidajensu kowa ya noke a kofar gidansu ya zuba ido kawai yana tausayi da jimami,
Abinka da mara mutunci da kunya a gaban mutane Yarima Zainur ya ynkura da nufin ya afkawa Sadirat ya lalata mata rayuwa kawai sai yaji an daka masa tsawa ,
Ko da ya waigo a fusace domin yaga wanda yayi masa tsawar sai ya ga wani matashi dan saurayi ya falfalo da gudu izuwa kansa yana kuka yana ihu ,
Ba wani bane face Hatyan, Sarkin mafarauta ya biyoshi da gudu yana kwala masa kira amma yaki tsayawa
Ko da dakaru guda Ashirin suka hango Hatyan a guje rike da takobi tsirara ya durfafo yarima sai sukaNan take Boka Daizan ya zuba alkalumansa sa sihiri ya shiga aiki,
Bayan dogon ya yi dan dogon bincike ya dago kai ya dubi Sarki Shamsal a lokacin da ya jike sharkaf da zufa kuma idanunsa suka kada sukayi jajur tamkar an gasa danvu a wuta babu kyan gani ya ce, "Ya shegaba hakika al'amarin wannan yaro da ban tsoro yake, domin akwai sa'a da nasara acikin harkikinsa,
Tabbas idan har ba a gano ba an kashe shi to sai wannan mafarki naka ya tabbata gaske
Abin da na iya gani kawai a cikin bincikena shi ne wannan yaro tuni ya fita gada kasarka tare da 'yar uwarsa domin tafiya ya rinkayi ba dare ba rana,
Kai lokacin da dokin nasa ma ya sare goya yar uwar tasa ya yi ya yi ta gudu da ita har tsawon kwanaki ashirin ba tare da ya tsaya ba , ko sau daya ya huta sai dai yasha ruwa ya mika wa 'yar uwarsa abinci da ruwa taci ta sha yana kan gudun saboda ya san cewa an biyo sawunsu,
Yanzu haka ya shiga wata kasa ce kuma na kasa gano a wane bangarene kasar take
Duk yadda aka yi shi ma wannan yaro ya na sirrin batar da sawun tafiya an ya kuwa bashi da wata alaka da mafarauta?"
Ko da jin wannan tambaya sai 1ki Shamsal ya yi shuru yana tunani har izuwa tsawon 'yan dakiku sannan ya dago kai ya dubi Boka Daizan ya ce mahaifinsa aminin Sarkin mafarautane,
Ko da jin haka sai Bika Daizan ya ce haba shiyasa na kasa ganin komai akan wannan yaron,
Ka yi sani cewa duk garin nan babu wanda yake da karfin sihirin Sarkin Mafarauta ;
NI kaina a wajensa nayi karatun tsadi amma har na kammala ban san rabin nasa ilimin ba, Daga bayane na shiga duniya naje na nemo wadansu sirrikan amma duk da haka ina shakkar sarkin mafarauta,
Duk inda sarkin mafarauta ya ke to ka tura aje a zo maka dashi amma bari na bincika naga yanda yake din,
Koda gama fadin hakan sai Boka Daizan ya zura hannu cikin aljihunsa ya fiddo madubinsa na tsafi ya ajiye a gaban sarki sannan ya shafi mudubin da hannun sa na hagu,
Maimakon mudubin ya nuna abin da akeso a gani sai ya yi duhu dudun ba a ganin komai,
Ko da ganin haka sai Boka Daizan yace " Ai Sarki mafarauta ya munafunceka tabbas da taimakon sa wannan yaro Hatyan ya sami nasarar guduwa tare da 'yar uwarsa "
koda jin wannan batu sai bakin ciki ya turnuke Sarki Shamsal ya sake kurma wani uban ihu a karo na biyu kamar zai fashe da kuka,
Sai daya shafe kusan dakika dari da ashrin yana huci da numfarfashi tamkar kumrucin maciji sannan ya ce, "Ya kai abin dogaro na ka yi sani cewa zama bai kama niba
Da kaina zan tafi farautar wannan yaro domin na kasheshi tun gabnin lokacin da zai dawo ya riskeni har cikin masarauta ta ya cini da yaki,
Taimakon da nake nema a wajenka guda daya ne , ina son ka bani hadimanka na aljanu kamar su dari biyar wadanda zasu dauki manzan nina su kaisu izuwa dukkan kasashen dake wannan nahiya tamu,
<<<<<<<<<<Khaleed>>>>>>>>>>
Zasu kai wasiku ne gamida hotuna masu dauk da Hatyan da 'yar uwarsa ,
A cikin kowace qasika zan gayawa kowane sarki da ya sa a baza hotunan su Hatyan a birni da kauye duk inda aka gansu a kamasu a tsare a kurkuku,
sannan kuma zan san ya lada mai tsoka na dubban durhami ga duk wanda ya sami nasarar cafkesu,
Ina son a cikin kwanaki uku kacal a gama rarraba wadannan wasiku da hotuna,
Ko da jin wannan batu sai Boka Dazan ya kyalkyale da dariyar mugunta ya ce, " Ya shugabana hakika kazo da shawara mai kyau domin wannan ce kadai hanyar da zaka bi ka hana Hatyan da 'yar uwarsa samun damar fita daga wannan nahiya kuma a cikin kankanin lokaci zasu dawo hannunka,
Tabbas kwakwalwarka tana ja kana da kaifin tunani gami da hangen nesa,
ko da jin wannan zuga sai Sarki Shamsal ya bushe da dariyar farin ciki ya shiga yiwa kansa kirari,
Ba tare da bata lokaci ba sarki ya rura akazo da wani makocin Satyan wanda gidan sa ke daf da na Satyan sannan aka kirawo wani masanin zane
Take makocin ya bayyana kamannin fuskar jarumi Hatyan da fuskar 'Yar uwarsa Sadirat,
Cikin kankanin lokaci mai zanen ya fitar da taswirar tamkar sune a wajen ba zanen su aka yi ba ,
Shi kuma Boka Daizun sai yayi tsafi takardun zanen ta tsara kanta har izuwa kimanin dubu dari ,
Daga nan kuma sai aka tara manzanni aka rarraba musu wasiku da hotunan su Hatyan da yawa aka kirawo aljanu suka kwashe su suka tafi dasu izuwa dukkanin kasashen dake nahiyarSai Hatyan ya kama hannun Sadirat ya jata suka kara gaba amma sai taga ya kan sunkuya kasa ya debi kasa ya shin shina sai kuma taga ya sauya hanya,
Al'amarin da ya yi mutukar bata mamaki kenan ta dubeshi ta ce, "Wai shin mainene ma'anar wannan abu da kake yi ne??"
Hatyan ya ce, "Ina yin haka ne domin na gano inda zamu samu rafi a kusa domin musha ruwa kuma mu yi guzurin sa da yawa.
Ki yi sani cewa ruwa ya fi abinci muhimmanci a rayuwar dan Adam domin zamu iyayin kwanaki bakwai babu abnc amma baza mu iya jure kishirwa ta sama da yini uku ba,"
Ai kuwa kamar tsafi sai Sadirat taga sun iso bakin wata korama mai dauke da ruwa mai kyau garai-garai, ruwan tafiya yake da gudu yana kwaranya izuwa kasan wani dutse.
Ciki farin cikin fuska suka ruga izuwa bakin koramar suka sa hannayen su ciki suna kwarfo ruwan suna sha.
Daga nan sai Hatyan ya bude jakar gzrnsa ya dauko abinci wanda bai wc loma goma ba suka ci tare suka kora da ruwa,
Gama hakan ke da wuya sai ya cika bututun ruwansu guda biyun da ruwa ya mika mata ta rike ya ce yanzu zan goya ki a bayana zan yi gudu dake na tsawom kwanaki ashirin.
Duk sa'adda kika ji kishirwa ko yunwa ki dauki abincin dake cikin jakarki ki ci kuma kisha ruwan battarki,
Ki sani cewa a tsawon kwana ashirin din nan ba zan tsaya ba domin ki huta ko da kuwa kin gaji da zama a gadon bayana.
A lokacin da Hatyan ya zo nan a zancensa sai Sadirat ta yi masa kallon mahaukaci ta ce "Ni ban taba jin inda bil'Adama ya iya jure gudu ba har na tsawon kwana ashirin ko kuwa kana nufin kan wani aljani zamu hau?? To wai shin kuma idn larura ta kamani fa ta fitsari ko kuma kashi???" (Sai tayi a haka ko ya kuka ce)
Ko da jin wadan na tambayoyi guda biyu sai jarumi Hatyan ya bushe da dariya ya ce," Ai kuwa zan baki mamaki saboda ni tin inada shekara tara a duniya duk sa'adda na shiga daji farauta sai nayi kwana ashirin ina gudu ba ci sai shan ruwa kuma wannan gudu da nake yi tsere nake kasawa da wata shirtacciyar bauna har sai na kure mata gudu na risketa mun fafata kazamin yaki, a karshe dai wuya ce ta ke sawa ta gudu ta barni.
<<<<< Khaleed >>>>>
Gudun kwana ashirin din da na ke yi dai dai yake da tafiyar kwana saba'in da tara akan doki. Wannan karfin gudu nawa baiwa ce zallah , Ina nufin da ita aka haifeni,"
Ko da jin wannan batu sai mamaki ya turnuke Sadirat kuma hankalin ta ya sake kwanciya ta ji ta kara samun nutsuwa ta cewar "Wannan kani nt zai iya krta gada sharrin Azzalumin Sarki Shamsal,
Ba tare da bata wani lokaci ba kuwa sai Hatyan ya rankwafa Sadirat ta hau bayan sa ya goya ta ya daure Sadirat tamau a jikin sa.
Battar ruwan sa kuwa na sakale a cinyarsa ta dama .
Kawai sai ya falfala da azababbebn gdu izuwa cikn dji.
Nan fa Sadirayt ta rinka ganin abu kamar almara domin saboda karfin gudun Hatyan har dan tashi sama yake yi kadan yana shallake gajerun bishiyoyi, 'yan duwatsu da kwazazzabai.
Wani lokacin ma sai taga kamar akan iska ko cikin sararin samaniyaa suke tafiya sbda karfin gd, Sai tari bata sanin sa 'adda barci yake saceta kuma duk sa'adda ta farka da ta ji kishirwa sai ta bude battarta ta kwnkwda ta koma barcinta( DA KYAU )
Abu dai kamr wasa sai da suka shafe kwanaki ashirin cif suna falfala gudu a cikin daji,
Tun tana kirga darare har lissafin ya kwace mata ta manta,
Abin da ya fi daure mata kai shine tun da aka fara wannan tafiya ba gajiya ba kuma bataji fitsari ko kashi ba, Tamkar bata ci da sha.
Abin da take ji kawai shine yunwa da kishirwa kuma suma da zarar ta ji su din sai ta dauko abincin guzrin da battar ruwanta wadan da suke jikinta ta kawar dasu
NANNE KARSHEN LITTAFI NA DAYA
MU HADU A LITTAFI NA 2
NAKU Suleiman zidane kd whatsapp 09064179602










No comments:
Write comments