Tuesday, June 18, 2019

Home WASU DALILAI DA KE SA NAMIJI YA QARA AURE
..

WASU DALILAI DA KE SA NAMIJI YA QARA AURE...

Dalilan suna da yawa amma dai ga wasu daga cikinsu zan lissafo kamar haka :-

-Akwai namijin da har ga Allah bai son qara aure yafi son zama da mace daya... To amma idan aka yi rashin sa'a ya auro wacce sai daga baya ya fahimci ba irin ta yake son zama da ita ba... Ko wacce bata haihuwa, ko mai lalura,to sai ya fara tunanin qara aure idan mai hankali ne kenan amma idan ba mai tunani bane sai ya saki matar ya auro wata...

-Akwai namijin da dama shi tun fil'azal burinsu shine ya auri mace fiye da daya... Kuma irin wadannan mazan duk irin kirki da tarbiyyar matar da suka aura a farko hakan ba zai hanasu qara aure ba dole sai sun qara din...

-Akwai mazajen da su kuma tsakani da Allah suke qara auren saboda raya sunnah kuma saboda suna da halin rike matan...

-Akwai wasu mazan wanda ba zasu iya zama da mace daya ba dole sai fiye da daya domin halittar ce haka kuma suna da cikakkiiya lafiya...

-Akwai wasu mazan masu qara aure kawai saboda naga abokaina su wane da wane sun qara aure amma ba wai dan yana da ra'ayi ba...

-Akwai wasu mazan wadanda suke qara aure saboda bin umarnin iyayensu... Watakila sun fahimci matarshi ta farko bata da tarbiya ko basu jituwa da ita saboda haka sai su samu wata a cikin dangi su ce lallai sai d'ansu ya qara aure da ita...

-Akwai mazan da basu da niyar qarin aure amma dalilin wata budurwa ko wata bazawara ta lik'e musu tun suna tirjewa har qarshe matan suyi nasara akan su...

Dalilan suna da yawa gaskiya kaima ko kema zaku iya kawo naku domin mu ji kuma mu qaru...

A wurin musulmi qarin aure ba zunubi bane ba kuma laifi bane... To amma tsakani da Allah akwai wasu mazan wadanda qarin aure bai zama cilas a garesu ba amma saboda karanbani sai su dage dole sai sun yi... Watakila kuma basu da hali ko dama ko lafiyar yin hakan kuma yin haka kamar ka shiga hakkin matanka ne da kai kanka gaba daya...

An ce namiji ya qara aure ne idan har yana da hali kuma zai yi adalci...Amma maganar gaskiya a wannan zamanin kowa yana qara aure ne domin wani muradi na karan kan shi ba wai dan Allah ko dacewa ba...

ALLAH YA BAMU IKON YIN ADALCI
1 comment:
Write comments

Follow Admin On Twitter naimismo1
Join Our Newsletter