Thursday, May 23, 2019

Home SIFFOFIN MAYAUDARA
..
SIFFOFIN MAYAUDARA
kamar yadda nai muku alkawari cewa zan kawo muku siffofin mayaudara a wancan darasin namu na YAUDARA A FAGEN SOYAYYA gashi Allah ya bani dama na cika saboda haka kusha karatu lafiya
via jamilu pambegua zaria
Yar uwa ki sani samari mayaudara sunfi samari na kirki shiga rai, sunfisu iya nuna so da qauna gareki, sukan kwantar da kai agareki komai wulaqanchi, gasu da masifar naci tun kina qin kulasu har sai sun jawo hankalinki, wannan dalilin yasa gane saurayi mayaudari abune mai wuya, domin abune dake cikin zuciya sai kinbi wasu matakai kafin ki ganesu.
DABARUN DA SAMARI SU KEBI DOMIN YAUDARAR YAN MATA
da farko su kanyi target din budurwar dasu keso, imma dan kyanta, ko hallitarta ko kimarta ko dan wani dalili nasu, ko kuma saboda fasiqanchi
su kanyi nazari akan halayenta kamar aqidarta, metafi so, wato idan ita ustaziyace sukan yi shigar ustazai suzo gunta idan suga dama sukan riqe littafi kamar sun fito daga islamiyya koki gansu da riyad salihin kamar wanda yafito daga masallaci wajen karatu
idan ke sayyada ce sukanyi miki shigar sayyadi suzo miki fira, idan suga dama sai su riqo wani qasida ko diwani su tasho dashi a hannunsu, kosu saka hoton shehu a wuyarsu,
idan kuma ke ma'abociyar karanta littafin soyayyane saisu zo miki da sababbin littattafan soyayya sabon fitowa, ko suzo miki da novel idan sun fahimci cewa ke meson karantawa ne
idan kuma ke yar holewa ce, to anan kuma da shigar holewa zasu zo miki
idan kuma ke mai siffar tausayi ne tofa anan zai miki da siffar cewa zai taimaka miki ne, domin har makaranta zaice zai saki
kullum aikin mayaudari bin ra'ayinki, bai son ya sa6a miki gasu da dadin baki, su kanyi ma mace kuka kosu durqusa mata dazarar sun miki laifi ga saurin bada haquri, mayaudara sun iya kalaman soyayya mai kwantar da hankali, ga kuma saurin rantsuwa wanda ko saurayin kirki baiyin irinsu
WADANNAN SIFFOFIN DANA LISSAFO ASAMA SIFFOFIN SAMARI MAYAUDARA NE AMMA SUNFI YIN AMFANI DA WANNAN SIFFAR WAJEN YAUDARAR YAN MATA YAN QASA DA SHEKARA ASHIRIN
sakamon yan matan a wannan lokacin su nada naqasu sosai na rashin wayewa akan soyayya, domin daidai wannan lokacin babu abinda suka sani saide soyayya wasu ma har bijirewa iyayensu su kanyi akan saurayi mussaman wanda ake ce musu sabon balaga, ko nace kwaila don anfi ganesu ahaka,
IDAN SAMARI ZASU YAUDARI MANYAN YAN MATA SU KAN YAUDARE SUNE DA KUDI KODA MANYAN MOTOCI DOMIN SU MANYAN MATA BASU DA WANI BURI FIYYE DASU GA SAURAYIN SU YANADA MOTA, KUDI, GIDA, MUSSAMAN YAN MATAN DASU HAURA SHEKARA 20 A DUNIYA
idan saurayi yaga dama zai iya aro mota yazo gurinki, gashi shifa arowa yayi amma zaice miki tashi ce kuma har miki alqawarin cewa zai siya miki kema, daga qarshe idan ya lalata ki shikenan saiya gudu ya barki da abin kunya, ke baki hau mota ba amma an hau ki
wasu mayaudaran ko har kayan nagani inaso sukan kawo gidan ku duk da siffar yaudara, wasu kuwa har dukiyar aure suna kawowa, wasu suturo iyayensu amma dazarar sun 6ata miki tarbiya sai su gudu suce su bazasu auri yar iska ba, bayan su suka lalata ki
wasu samarin na yaudarar yan mata ta hanyar abokai ko qawa, domin sa miki kwaya acikin lemo ko wani abinsha domin dai asamu a tsallaka ki
DALILIN DA YASA SAMARI KE YAUDARA
* rashin tsoron Allah
* wasu kuma daukar fansa wato idan wata ta yaudaresu sai suce sai sun rama akan wata,
* wasu samarin kuma sha'awar zinace kawai burinsu sunyi fasiqanci da yarinya
YADDA ZAKIYI MAGANIN SAMARI MAYAUDARA
* kada ki ta6a yadda ki zurfafa son saurayi acikin zuciyarki ko waye shi kuma kome ya kawo gidanku
* ki kasance me yawan roqon Allah saboda neman kariya ga sharrinsu
* kada ki yaudari wani don kema sai an rama
* sannan abu na farko shine istikara, misali idan saurayi yazo gurinki farkon zuwa kice ya baki kwana biyu kiyi shawara, idan kiyi istikara akan shi idan bana kirki bane bazai qara zuwa ba, Allah zai watsa masa aniyar shi can,
sannan kada ki yarda kiyi alaqa na soyayya da wani batare da sanin iyayenki ba, sannan tun kafin ai nisa kece masa ya turo nashi iyayen su nema mishi izinin nemanki
kada wai don yakawo kudin aure gidanku ki saki jiki dashi, shedan na iya zigashi ya lalataki
dazarar kinga canji na rashin amincewa game da saurayinki toki gaggawan tsage masa gaskiya, kar ki mishi da wasa saboda karya raina miki wayau,
yar uwa wani namijin shege ne acikin minti goma 10 zai iya zubar miki da tarbiyar da iyayen ki suka shekara ashirin 20 suna gina miki ita,
namiji mugune ya lalataki kuma 6ata miki record dinki ya lalata miki tarbiya ya tozarta miki zuriya, ya 6ata miki suna, tare da watsa ma iyayenki qasa a ido ya jefa miki tunani, sannan ya barki da abin duniya, daga qarshe ya gudu ya barki yaje ya nemi wata
samari mayaudara abokan juna ne domin ko ina zaki gansu tare idan wannan ya kwashe ki saiya ba wancan labari domin shima yazo ya diba saboda haka mata sai a kiyaye
75 na samari yanzu saide kawai nace Allah ya shirye mu domin babu alkairi da muke tunkarar yan mata dashi, face qoqarin kwanciya dasu domin samun damar kwace musu quruciyarsu
YA ALLAH KABA MATAN KWARAI MIJI NAGARI MAI TSORONKA WANDA ZAI RIQESU AMANA DA KYAKKYAWAR KULAWA
bari na tsaya anan na huta idan mun hadu a darasi na gaba sai mu cigaba, domin inason na kawo muku siffofin da ake gane mayaudara mata suma domin mazaje su gujesu
Idan kina buqatar karanta kala kalan HAUSA NOVEL masu dadi da sanya nishadi tare da debe kewa tun daga kan marubuta mata har izuwa na maza dake fadin arewacin qasar nan zaki iya samin su a group dinmu mai suna £ JAMEEL NOVELs £ domin samur damar shiga group din sai ku turo da lambar waya ta --» 08104550703 mu kuma dan mun gani zamuyi add dinku
Daga naku har kullum jameel el hussain ahamad pambeguwa zaria kaduna state nigeria 08104550703

Posted by #NAIMISMO1
No comments:
Write comments

Follow Admin On Twitter naimismo1
Join Our Newsletter