Thursday, January 23, 2020

Fateema Habeeb 25

Fateema Habeeb  25



                   na
Jamilu el hussain zazzau



             dedicated to
       Amina baba kaduna



ALLAH KA JIKAN MAHAIFINA, ALLAH KA GAFARTA MISHI, YA ALLAH KA KAI HASKE KABARINSA, ALLAH KASA MUTUWA HUTUCE AGARESHI DA SAURAN MUSULMI BAKI DAYA




Waje kowannen su ya samu ya zauna, principal ya dago kai gami da kallon su rike da biro a hannusa yace to ina jinku meke faruwa ne? bargon lullubar fatima copper yusif ya amsa ya mikawa principal yace sir kalli yadda yaron nan yaje har lodge dinmu yay ma fatima rubutu a jikin mayafin kwanciyar ta,

amsar bargon principal yayi, tsaf ya karanta abinda ke ciki abin ya bashi mamaki, kai ya dago ya bisu da kallo daya bayan daya, sannan yace kuna da tabbacin cewa shiya rubuta?

budar bakin copper kadija tace of course sir, domin yayi irin hakan sau da yawa ni nake kare shi, kawai gajiya nayi shiyasa nake ganin ya kamata nabari a hukunta shi ko zai gane kuskuren sa,

na dan lokaci kadan principal yay shiru, sannan ya dago kai ya kalle su yace ba damuwa ku tashi kuje, hukumar makaranta zatai zama a kanshi, atare su hada baki suce thanks u sir, sannan suka fito daga office din su wuce staff,

principal na kammala abinda ya keyi ya fito, kanshi tsaye ya nufi staff ya kira sajan sunufi class din su habib, suna shiga students duk su mike, yace kar ku damu ku zauna, ina habib sani? hannu habib ya daga yace sir ganinan,

harara sajan ya jefo masa yace stupid come out, kai tsaye habib ya kama hanya ya fito, yana zuwa gabansu sajan ya zabga mishi mari yace wawan banza wuce muje, a gaba su tasa keyar habib zuwa office din principal,

suna shiga su saka shi ya zube akasa, kafin kace wani abu sajan yafara sauke mishi dorina ajiki, kallo principal ya watso mishi yace kyale shi haka, sannan ya kalli habib ya nuna masa mayafin fatima yace meyasa kai wannan rubutun?

dago kai habib yayi ya kalli rubutun, sannan ya sunkuyar dakai kasa, tsawa principal ya daka mishi yace ba dakai nakeyi ba, baza kai magana ba? kadan habib ya dago kai yace sorry sir, ran principal abace yace sorry for what? yace please sajan ci min uban yaron nan, ji kake tas, tas, ganin jikinsa yayi laushi yace barshi haka,

kallo principal ya watso ma habib cikin bacin rai yace idiot go back to your class, sannan ka jira hukuncin da hukumar makaranta zata yanke akan ka, tashi habib yayi cikin tsamin jiki yanufi class din su,

yana fita principal ya kalli sajan yace jeka kiramin vice da admin master kace kome su keyi su bari suzo akwai al amari na ujila, sajan yace ok sir, da sauri sajan yaje ya sanar dasu, cikin hanzari kowannen su ya kamo hanya yazo,

kallo vice ya watso ma principal gami da cewa sir lafiya kuwa? a tsanake principal ya basu labarin duk abubuwan da habib yay ma fatima, nanfa su shiga cancel meeting, daga karshe duk bakin su yazo daya, suka yanke shawarar cewa kawai a kore shi daga school din,




from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp  08104550703
Read More»

Fateema Habeeb 24

Fateema Habeeb  24

                    na
Jamilu el hussain zazzau

           dedicated to
     Amina baba kaduna

3 weeks letter,

A kullum soyayyar fatima sake bijirowa habib keyi acikin zuciyar sa, zaune yake watarana a cikin gida yana tunanin ta, kawai zuciyar shi ta rada mishi cewa ya tashi ya tafi lodge din su domin yay tozali da ita ko zuciyar ta sami saukin tunanin da takeyi,

tashi yayi ya debi ruwa ya  shiga bandaki, yana fitowa sami lotion mai kamshi ya shafa, sannan ya canza kaya kai tsaye ya nufi lodge din, ko tsoro babu cikin zuciyar habib kai tsaye yasa kai ya shiga ciki,

yana shiga ya iske duk basa nan dakunan su akulle duk sun shiga cikin gari, yana duba igiyar shanyar dake ciki ya iske kayan fatima tayi wanki, maka ya dauka a jikin wani window ya rubuta, zanyi alfaharin kasancewa tare dake har karshen rayuwa ta, yana gama rubutun ajikin mayafin ta ya mayar da makan ya fito yay tafiyar sa,

6:00pm na yamma fatima su dawo daga cikin gari, suna shiga lodge ta kwashe shanyanta ta shiga dasu daki, bayan sun gama abinci kowa taje tai sallah, sannan su dawo kan abincin suna ci suna fira, zuwa karfe goma su fito atare sukai brush sannan su koma daki su kwanta,

misalin karfe sha biyu na dare a kawo nepa, fatima na farkawa ta gansu acikin haske sun manta basu kashe kwan dakinsu ba,

tana zame mayafin kwanciyar a jikin ta taga wannan rubutun, da sauri ta saki mayafin ta tsandara ihu, a firgice kadija ta farka tana tambayar ta lafiya kuwa?

karar kwan kwasa kofa suji, cikin faduwar gaba kadija tace waye? copper yusif yace mune ihu muji me yake faruwa ne? kai tsaye ta taso ta bude musu kofar su shigo,

watso mata kallo suyi gaba daya suna tambayar ta lafiya kike zabga irin wannan ihun acikin daren nan, bargon ta nuna musu tace ku duba mayafin kwanciya ta kuga rubutun dake ciki,  copper yusif ya tsuguna ya dauka gami da karantawa ya gani,

sannan ya kalle su yace yanzu kunga dare ne, saboda haka abinda nake so daku kowa ya koma daki ya kwanta, idan Allah ya kaimu gobe saimu shiga da bargon school mu nunawa principal, suce ok ba damuwa, kai tsaye kowa ya koma daki ya kwanta,

washe gari da safe bayan sun shirya, copper's sama da biyar su jera tare da fatima zuwa cikin school, suna shiga school din kai tsaye su zame zuwa office din principal,

permission su dauka, yace yes ku shigo, ganin su da yawa yasa principal ya dago kai yace lafiya kuwa? kadan kadija ta saki fuska tace lafiya qalau sir,

from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp   08104550703
Read More»

Fateema Habeeb 23

Fateema Habeeb  23

                   na
Jamilu el hussain zazzau

            dedicated to
      Amina baba kaduna

2 days da faruwar hakan har habib ya mance duk nasihar da copper kadija tai mishi, kai tsaye ya kama hanya ya nufi har copper's lodge rike da chalk a hannun sa, yana zuwa ya sami dai dai kofar shiga ya rubuta, u are d only on my heart fatima, yana gama rubutawa yasa kai yay tafiyar shi,

da yawan copper's sun  wuce hankali su baije kan rubutun ba, 5:30pm kadija da fatima su dawo daga cikin gari, suna isowa bakin lodge sukai ido biyu da wannan rubutun, rai abace fatima ta kalli kadija tace kin gani ko? yaron nan idan bansa anci ubanshi ba bazai fita harka taba, da sauri ta shiga ciki taje kiran copper yusif,

ganin haka yasa kadija tai sauri ta samo dosta ta share rubutun, suna fitowa copper yusif ya kalli fatima yace ina rubutun yake? wurgo ma kadija kallo tayi tace wato share wa kikayi ko? kadan kadija ta saki numfashi tace kunga mu shiga daga ciki kawai, ku manta komai ya wuce,

kai fatima ta girgida gami da cizon libs tace zan kama meyin hakan koma wanene, atare su koma cikin lodge din,

washe gari da safe duk suka shirya sanye da kayar bautar kasa a jikin su, domin ranar zasu tafi taro local government secretaria, tafiya su keyi suna dibar fira abin su kadija ta tuna ta mance wani abu a daki,

kallon fatima tayi tace kawa nayi mantuwa, rike min bag dina ki wuce barina koma na dauko, fatima tace ok, da sauri kadija ta kama hanya ta koma lodge, tafiya fatima ta cigaba dayi tana isa cikin school taga jikin wani bangon class an rubuta copper fatima u are d only person I always seeing on my dream,

tana gama karantawa ta girgida kai tace ji dan iska harda nan ma, da sauri ta karisa staff domin ta samo evidence, teachers guda biyu ta kira su kamo hanya tare,

kafin su kariso har kadija ta iso wajen, tana gani ta share rubutun sannan ta cigaba da tafiya, a hanya ta hadu dasu tace lafiya kuwa, ina za kuje haka?

kallo fatima ta wurgo mata tace kema zo muje ki gani ma idon ki, suna karisawa su iske a share rubutun, kallo su watso mata suce ina rubutun yake? shiru tayi jikin ta yay sanyi tace kuyi hakuri ina ganin wani ya goge, amma ba komai koma waye kiyin hakan asirinsa zai tonu, atare su kama hanya su koma cikin school,

9:00am su kama hanya su nufi local government, misalin karfe sha daya su dawo, bayan sun huta kowa ya duba time table ya tafi class din da yake dashi,

class din su habib fatima taje, tana shiga students su mike atare su gasshe ta, tace ku zauna, da sauri class captain ya dauko dosta ya share mata black bord, kai tsaye tafara lesson,

tambaya tayi class yay tsit babu wanda ya sani, hannu habib ya daga, tana gani ta harare shi taki pointing din shi, ta cigaba da lesson dinta, duk tambayar da tayi saiya daga hannu ita kuma taki pointing din shi, domin jikin ta yabata cewa shi yake wannan rubutun,

from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp  08104550703
Read More»

Fateema Habeeb 22




Fateema Habeeb  22

                     na
Jamilu el hussain zazzau

            dedicated to
       Amina baba kaduna

ok meyasa kai wannan rubutun? budar bakin sa yace sir gaskiya banji dadin abinda tasa aima same name dina bane, principal yace ok za kaci ubanka,

kallon teachers din nan yayi yace ku bashi kashi, atare su fara tsulan shi, ji kake tas tas tas tako ina, ganin jikin sa yayi laushi principal yace ku kyale shi haka, kallo ya watso mishi yace stupid tashi ka wuce class gobe ka sake, cikin tsamin jiki takwaran habib ya tashi ya koma class din su,

3 weeks da faruwar wannan al amarin, class teacher din su habib ya aike shi staff ya dauko mishi register, yana shiga staff habib ya iske teachers din dake ciki sai famar dibar fira su keyi, fakar idon su yayi ya karisa kujerar fatima, wani littafi ya gani a saman table dinta da sauri ya bude bangon littafin ya rubutu I love u fatima, yana rubutawa ya mayar da sauri ya aje, kai tsaye yaje ya dauki register din ya fita,

12:pm na rana fatima ta dawo staff, tana shigowa ta iske kadija zaune tana hutawa, kallo ta watso mata kawa baki da class ne? kai kadija ta dago su hada ido tace sai zuwa 12:50pm,

bag fatima ta ajiye sannan ta sami waje ta zauna, tana kallon book dinnan taga alamar kamar an taba, domin habib bai mayar dashi inda ya same shi ba, tana budewa taga wannan rubutun, fuska a daure ta nunawa kadija tace kawa kinga abinda wani dan iska yay min ko,

amsa kadija tayi tace mugani me aka rubuta? tana dubawa tai murmushi tace haba to menene don ance I love u? bafa I hate u aka rubuta ba, kai fatima ta girgida tace lallai ne kawa yanzu na fahimci ko kadan bakya son gaskiya,

numfashi kadija taja, tace bahaka bane kawai dai kin kasa fahimta tane, amma dan Allah mubar maganar nan iya mu biyu basai  kowa ya sani ba, domin kina fada za ace habib ne koda bashi ya aikata ba,

ummm aini nama fiso ace shi dinne a farfasa mishi jiki, domin na tsane shi sosai, hannu kadija ta dora a kafadar ta tace naji, amma dan Allah akan wannan kiyi hakuri idan ki sake gani saiki dau mataki koma me zakiyi bazan hanaki ba, numfasawa fatima tayi tace to shikenan, nan suka bar wannan firar suka shiga wata saugar,

ana gab da tashi school kadija taje har class din su habib ta kira shi, a waje su tsaya, tace kaga habib tambayar ka nake so nayi amma banso kai min karya, fuska a sake yace ba damuwa malama yi tambayar ki naji,

tace kaine kaje har staff kayi wa fatima rubutu a bangon littafin tako? nadan lokaci kadan yay shiru sannan ya dago kai yace hakane nine,

tace haba habib meyasa kai haka, shin taya ma akayi ka shigo har cikin staff babu wanda ya ganka? uncle ne ya aike ni staff na dauko mishi register, ina shiga na iske teachers sai dibar fira su keyi duk hankalin su baya kaina, kawai sai nayi amfani da wannan damar na rubuta,

shiru kadija tayi tana sauraran shi, yana gamawa tace tabbas kayi babban kuskure domin da ace wani ya ganka fa? kai ka sani da yanzu wani labarin ake ba wannan ba, saboda haka ina baka shawara kada ka sake aikata irin wannan kaji,

yace zan kiyaye insha Allahu, tace to shikenan Allah yasa, yace amin malama nagode,

from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp  08104550703
Read More»
Follow Admin On Twitter naimismo1
Join Our Newsletter