Saturday, December 7, 2019

Fateema Habeeb 21



Fateema Habeeb  21



                    na
Jamilu el hussain zazzau



           dedicated to
     Amina baba kaduna




kallo copper kadija ta watso ma habib, tace masu suna habib ku nawa ne a ss 3? kadan habib ya dago kai yace muna da yawa,

nadan lokaci kadan tai tunani sannan ta numfasa ta kalli principal, tace sir ina ganin ya dace duk wani students mai suna habib a ss3 ya kamata akira shi domin tabbatar da wanda yay wannan rubutun acikin su, domin a tunani na wani na iya rabewa da sunan habib ya aikata hakan,

kadan principal ya numfasa yace bamu ki shawarar da kizo da ita ba, to amma muddin bamu sami wani ba dole shi zai amsa wannan laifin, tabbas kuma hukumar makaranta zata hukunta shi,

dago kai habib yayi yace na yarda, numfashi principal yaja sannan ya kalli displine yace kuje duk ss3 daga A har zuwa C duk wani student mai suna habib ku taho min dashi,

displine yace ok sir, kai tsaye su kama hanya su nufi ss3A, suna shiga students duk su mike su gasshe su, tambaya suyi mutun nawa ne masu suna habib acikin class din nan? ace mutum daya, suce ina shike ya fito, da sauri habib musa ya fito, suka tasa keyar shi su nufi ss3B,

nan dama habib ne kawai mai suna a class din, nan suka fito su nufi ss3C, suna zuwa su sami masu suna habib guda biyu a can, kai tsaye su taso keyar su zuwa office din principal,

suna shigowa duk asa su sukasa guiwar su akasa, muzurai displine yay musu yace kai acikin ku waye ne yaje cikin toilet yay rubutun batanci ga copper?

duk shiru su kayi, wannan ya kalli wannan, wannan ya kalli wannan, tsawa displine ya daka musu yace koba daku nake magana ba? da sauri kowa yace bashi bane, kai displine ya girgida ya kalli kadija yace copper dama na fada miki babu wanda zaiyi rubutun nan face wannan shaidanin yaron,

kallon su yayi yace ku tashi ku koma class, har sun mike zasu fita kadija tace ku dakata, chalk ta dauka taba kowa daga cikin su tace ga black bord nan, inason kowannen ku ya rubuta min malama fatima azzaluma,

amsa su kayi sufara rubutawa daya bayan daya, ana zuwa kan wanda yay rubutun hannunsa yafara rawa, yayi kokarin canza hand write amma ya gagara, ganin yadda ya daburce tace ma sauran ku kukoma gefe kai rubuta mugani,

yana gama rubutawa ta kalli habib tace kaima tashi ka rubuta, mikewa habib yayi ya amsa chalk ya rubuta, kadan tai numfashi sannan tai murmushi, teachers kowa ya zuba mata ido,

kallon yaron nan tayi, tace wannan shi yay wannan rubutun, idan kunaso ku tabbatar kuje ku sake duba wancen rubutun da kyau zaku fahimci abinda nake fada muku,

atare wasu daga cikin su suka koma toilet su duba wancen rubutun, suna dawowa suka sake duba wannan da kyau suce tabbas rubutun shine, a fusace displine ya kalli yaron yafara mishi barazana sai gashi yaron amsa laifin sa cewa shi yayi, kadija tace to kun gani ko? dama tsoron da naji Kennan kada aje a hukunta habib akan laifin da bashi ya aikata ba,

numfashi principal yaja ya kalli Habeeb yace Allah ya kwace ka tashi ka wuce class, yace ma sauran kuma ku wuce, tsawa ya dakawa yaron da yay rubutun yace kai menene cikakken sunan ka? yace Habeeb garba,





from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp  08104550703
Read More»

Fateema Habeeb 20



Fateema Habeeb  20



                    na
Jamilu el hussain zazzau



           dedicated to
      Amina baba kaduna




kai tsaye ya koma office din principal ya shaida mishi yadda su kayi da fatima, principal yace to shikenan tunda ta yafe komai ya wuce, saide kaja mishi kunni saboda kujewa faruwar haka nan gaba, malam sani yace insha Allahu, nan sukai sallama ya fito ya dauki mashin dinsa ya nufi gida,

murja ya iske zaune a dokin kofa rike da kofin kunu a hannu tana jiran dawowar shi, sallama yayi, ta amsa tace megida ka dawo? yace eh, kadan ya dan gusa kusa da ita ya samu guri ya zauna,

labarin duk abubuwan dasu faru ya kwashe ya bata, cike da mamaki ta girgida kai tace kai amma gaskiya habib be kyauta ba, amma duk da haka hukuncin da suka masa yayi tsauri da yawa,

wurgo mata kallo yayi yace to ai maganin sa Kennan, tashi ki miko min sakon nan nazo na wuce kasuwan nan, tace to megida,

1:30pm a tashi daga school, habib na shigowa gida ko zama beyi ba murja ta rufe shi da fada, wawan banza dama soyayya muka tura ka kayi a school din?

banda rashin hankali irin naka duk yara matan dake school din babu wacce tai maka sai malamar ka, ga yaran makota nan duk baka ga wacce kakeso ba har saida kaje ka jawo ma kanka fitina, duk fadan da murja take mishi shiru yayi baice komai ba harta gaji ta daina,


A bangaren kadija kuwa suna komawa lodge kallo ta watso ma fatima, tace a gaskiya kawa banji dadin abinda kiyi ma taohon nan ba, yatsine fuska tayi gami da kada kai tace dansa yaja masa,

kadija tace naji amma koba komai ai ya haifeki, fatima tace yadai haife shi amma bani ya haifa ba, kinga kadija barina taka miki birki naga akan wannan al amarin kina son ki rikayi min shishshigi, gaskiya idan baki bari ba zamu sami matsala, numfashi kadija taja tace to shikenan Allah ya baki hakuri,


2 weeks da faruwar haka, wani student yaje har toilet din malamai ya rubuta copper fatima ke jahila ce, kuma azzaluma mara tunani, jaka ma tafiki hankali, nine habib daga ss 3,

11:00pm na ranar copper yusif ya dauki buta ya nufi toilet din domin ya zaga, ya gama lalurar sa zai fito yaci karo da wannan rubutun, da sauri ya nufi staff ya sanar da duk malaman dake ciki,

gaba yayi duk suka biyo shi abaya, suna zuwa kowa ya ganema idonsa, kafin kace wani abu har ansami wani daga cikin su yaje ya sanar da principal, cikin bacin rai principal yace kuje ku duba ku gani idan yaron yazo school ku taho dashi,

kusan malamai biyar su nufi class din su habib kowa rike da bulala a hannu, suna shiga class din cikin uban kowa ya duri ruwa, displine yace ina habib sani?

mikewa habib yayi yace sir gani nan, yace fito dan ubanka, tashi guda hantarsa ta kada cikin kyarmar jiki ya fito, kai tsaye su tasa keyar shi zuwa office din principal, dai dai lokacin kadija na cikin wani class tana lesson taga an wuce dashi, da sauri ta fito ta bisu abaya,

suna shiga principal ya watso mishi kallo yace sa guiwar ka akasa, da sauri habib yay biyayya yay kasa, cikin bacin rai yace mishi wato kai saboda iskanci har cikin toilet dinmu kaje ka rubuta kalaman batanci ga copper dun tace bata sonka ko?

fuska cike da kwalla habib yace sir wallahi bani bane, principal yace oh bazaka fadi gaskiya ba Kennan? yace sir na rantse maka banma san anyi ba, principal yace to shikenan tunda bazaka fadi gaskiya ba barina sa abaka kashi,  shiru habib yayi idanuwan sa duk su cika da kwalla,

murmushi displine yayi yace yaro kenan, tun ban fara cin ubanka ba harka fara kuka, tsawa ya daka mishi yace tashi muje, kadija tace kunga ku dakata, yana da kyau ku tabbatar cewa shiya aikata kafin ku hukunta shi, displine yace to mun baki dama ya kike so ayi?



from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp  08104550703
Read More»

Fateema Habeeb 19


Fateema Habeeb  19



                    na
Jamilu el hussain zazzau



     
            dedicated to
       Amina baba kaduna





suna cikin magana sai ga malam sani ya shigo, kallo ya watso musu yace lafiya kuwa? rigar habib ta daga mishi tace megida kalli jikin yaron nan sai kace wanda yay sata,

nadan lokaci kadan malam sani yay shiru, sannan yace to kin tambaye shi abinda yayi akai mishi hakan? eh mana, ya fadamin tuk akan fashin makarantar da yayine kwana ki shine har yanzu cin zalin bai ishesu ba,

paper din habib ya mika mishi, malam sani ya amsa ya karanta, sannan ya dago kai ya kalli murja yace cewa suyi suna bukatar ganina, kinga idan naje koma menene zasu min bayani ai, tace to shikenan Allah ya kaimu, yace amin,

waje habib ya samu ya baje a tabarma, da sauri murja ta dora mishi ruwan zafi domin ya gasa jikin shi, sannan taje ta kawo mishi abinci da ruwan sha, ranar babu inda habib ya fita,

washe gari da safe habib ya tashi yay shirin school, yana gama karyawa malam sani yace to dauko jakar ka muwuce, kan mashin ya dauki habib sunufi school din,

suna isa ya kafe mashin din, sannan ya tasa keyar habib zuwa office din principal, malam sani na shigowa principal ya nuna mishi kujera yace ga wuri nan zauna,

bayan sun gaisa yace naga yaro da sako shine na biyo baya, numfasawa principal yayi yace malam sani yaron ka ya tabka babban kuskure, amshi wannan takardan ka karanta kaga abinda ke ciki,

amsa malam sani yayi ya karanta tsaf, cike da mamaki ya kalli habib yace kai ka rubuta wannan? ba gardama habib yace eh, shiru malam sani yayi sannan ya girgida kai yace lallai yaro ka girma, sannan ya kalli principal yace malam buhari dan Allah kuyi hakuri,

girgida kai principal yayi yace malam sani ai bani zan yanke hukunci akan wannan al amarin ba, hukumar makaranta da ita wacce akayi wa laifin su suke da hurumin yafe masa, abin ya batawa malam sani rai sosai, cikin zafin rai ya fito daga office din principal ya nufi staff,

yana shiga ya samu wani teacher yace mishi nine mahaifin yaron nan da yayiwa malamar shi wasika jiya, nazo ne domin na roketa tayi hakuri, teacher din yace tana can tana koyarwa saide kadan jira ta dawo tukun,

malam sani yace ba damuwa, waje ya samu ya zauna, zuwa can sai gata ta shigo ita da kadija, nuna mishi ita teacher din yayi yace yauwa baba  gatacan ta dawo, itace mai bakin hijabin can,

da sauri malam sani yaje ya sameta yace malama barka da fitowa, kallo ta watso mishi tace old man meke faruwa? tana fahimtar cewa mahaifin habib ne saita juya harshenta na nufanci ganin cewa yana jin turanci, saboda batason ta saurare shi, domin batason ta yafema habib ita burinta kawai a kore shi daga school din,

ganin haka yasa malam sani ya juya zuwa gurin teachers din dake cikin staff din yace dan Allah kusa mana baki ko zata hakura,

tana jin ya fadi haka taja tsaki ta fita daga cikin staff din, ganin haka yasa kadija tabita  da sauri tace haba kawa meyasa kike irin wannan, ya kamata ki dawo cikin hankalin ki, wannan abinda kiyi sam bai dace ba,

cikin fushi fatima ta kalli kadija tace dakata min malama, me kike nufi dana dawo cikin hankalina? ok kina nufin yanzu bani da hankali kenan,

suna cikin haka malam sani ya kariso wajen ya kalli fatima, yace yarinya ki dubi tsufana da yadda nake rokon ki kiyi hakuri kuskure ne insha Allahu hakan bazai kuma faruwa ba,

waigowa fatima tayi ta nuna malam sani da yatsa tace naji na hakura,  amma kaja masa kunni ya tabbar hakan bai kuma faruwa ba,

malam sani yace nagode yarinya Allah ya miki albarka, juyawa yayi zuwa cikin staff yay sallama da sauran malaman sannan ya fito,





from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp  08104550703
Read More»

Fateema Habeeb 18

Fateema Habeeb  18



                    na
Jamilu el hussain zazzau




              dedicated to
        Amina baba kaduna




misalin karfe goma na safe lokacin kowani students na class, kai tsaye fatima ta fito daga  staff ta nufi office din principal,

permission ta dauka, principal yace yes shigo, fuskanta a sake ta shigo ta samu waje ta zauna, kallo principal ya watso mata yace copper meke faruwa?

hannu tasa a jaka ta dauko wannan wasikar ta mika mishi, principal ya amsa ya karanta, yana gama karantawa ya dago kai ya kalle ta yace copper waye yay miki wannan wasikar?

tace sir wani student ne, kuma na waye shi, yace idan kin ganshi zaki iya nuna shi? tace yes sir, yace ok tashi muje, kai tsaye su zame staff principal ya kwaso teachers sama da goma kowanne rike da bulala a hannu sunufi class din su habib,

suna shiga class din students kowa ya mike, tashi guda cikin kowa ya duri ruwa, cikin zafin rai principal yace waye habib sani? mikewa habib yayi yace gani sir, yace come out, a tsorace habib ya kama hanya ya fito, tsawa principal ya daka mishi yace kai da waye kuje copper's lodge jiya?

waigawa habib yayi ya kalli abdurrahaman yaga sai famar kyarma ya keyi idanuwan sa duk sun ciko kamar zeyi kuka, yace sir bezo ba, principal yace ok wuce muje, agaba su tasa shi zuwa staff, suna zuwa habib yasa guiwar sa akasa,

kallo principal ya watso mishi yace waya rubuta wannan wasikar? habib yace nine, yana fadin haka principal ya wanka mishi mari yace idiot,

kallon teachers din nan yayi yace ku bashi kashi, ji kake tas tas tas duka kawai tako ina, ko kuka habib ya kasayi sai ninshi kawai, ganin jikin sa yayi laushi principal yace ku barshi haka, ya kalle shi yace toya kana kan bakar ka koka saki?

dago kai habib yayi yace sir har yanzu ina sonta, principal yace ashe be dakuba ku cigaba, tas tas su cigaba da tsulan shi, principal yace ku dakata, kallo principal ya sake watso mishi yace toya ka janye ko kuwa?

kai habib ya dago ya kalli fatima yace I love u, jin haka yasa finance ya kalli principal yace sir ina ganin bayin kansa bane, ba mamaki akwai abinda ke damun sa, yana da kyau koda iyayen shine a bincika aji ko yana da tabin hankali, principal yace ok bari mu gwada yin hakan mugani,

kallon habib yayi yace tashi muje, kai tsaye ya tasa shi agaba zuwa office din sa, paper ya samu yay rubutu yace amshi wannan ka wuce gida yanzu ka kaima mahaifin ka,

amsar paper din habib yayi ya fito, jikin wata bishiya ya samu ya zauna yana huta gajiyar dukan da yasha, ana tashi school habib yabi ayarin students sunufi gida,

tafiya su keyi class mate din shi kowa na fadin albarkacin bakin sa, wannan yace gaskiya habib kayi rashin hankali, wannan yace gaskiya baka kyauta ma kanka ba, murmushi habib yayi yace bazaku gane bane, Ishaq din class din su yay dariya yace aikai daka gane gashinan an baka sakamakon ganewar, haka su cigaba da tafiya har suka isa gida,

habib na shiga gida murja ta ganshi a yamutse kamar wanda ya fito daga prison, matsowa kusa dashi tayi taga rigarsa har tana yagewa tsabar duka,

daga rigar  tayi taga bayansa yayi rudu rudu ga shaidar bulala, har tana hawaye tace Habeeb waya maka irin wannan hukuncin,

numfashi yaja yace umma su nada yawa, tace to laifin me kayi haka? ko dai tun akan wannan maganar ta kwana kine?




from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp  08104550703
Read More»

Saturday, November 30, 2019

Fateema Habeeb 17

Fateema Habeeb  17



                     na
Jamilu el hussain zazzau



     
             dedicated to
       Amina baba kaduna




malama nima banyi kaina bane, domin tun ranar dana ganta zuciya ta ta kamu da sonta, tun a wancan lokacin nai kokarin kawar da soyayyar da karfi amma abin yafi karfi na, domin a sanadiyar afkawa soyayyar ta har matsala na samu da iyayena, baya ga nan na samu matsala da malamai na, na kuma amshi horo da azabtarwa iri daban daban,

saboda haka tunda na riga na furta na gummace na mutu akan na janye abinda ke zuciya ta, tace oh yanzu habib kana nufin bazama ka janye wannan maganar bama kenan? yace wallahi malama bazan iya ba, idan na janye mutuwa zanyi, saboda haka na dauki damarar jure duk wata wahala da zata biyo bayan yin hakan,

jin wadan nan jerin kalaman daga bakin habib yasa jikin copper kadija yay sanyi, tashi guda tausayin shi ya kamata, tace kabari zan sameta a tsanake na fahimtar da ita duk yadda muyi zan sanar dakai, yace nagode saida safe, tace Allah ya kaimu,  kai tsaye habib ya kama hanyar gida, ita kuma ta koma cikin lodge din,

copper kadija na shiga kai tsaye taje daki ta iske fatima, kusa da ita ta samu waje ta zauna agefen katifa, tace kawa inason muyi magana akan habib, fatima tace umhum ina jinki, kallo kadija ta watso mata tace a zahirin gaskiya bazan boye miki ba yaron nan ya kamu  tsananin soyayyar ki, game da labarin irin halin daya shiga akan soyayyar ki yasa jikina yayi sanyi sosai, tabbas na tausaya mishi,

kallo fatima ta jefo mata, tace yanzu me kike nufi? numfasawa kadija tayi tace ki taimaka ki ceto rayuwar shi, yatsine fuska fatima tayi tace me kike nufi dana ceto rayuwar shi? kadija tace ina nufin ki amshi soyayyar shi,

rai abace fatima tai girgida kai tace kin raina min hankali, in banda kin raina min wayau ni zaki kalla kice nai soyayya da students dina, wanda na tsere mishi ta kowani fanni,

numfashi kadija taja, sannan ta girgida kai tace wannan ba rainin wayau bane kawai zan iya cewa wani al amari ne daga ubangiji, domin shi Allah yana iya sarrafa al amarin sa takowani fanni kuma a lokacin da yaga dama, idan zaki tuna tarihin mazon Allah (s a w) lokacin da uwar muminai nana kadija ta aure shi aita girme shi sannan ta fishi arziki, saboda haka a tunanina ma yin hakan koyi da sunna ne,

buder bakin fatima tace ai naga kema mace ce, idan da gaske ki keyi kin tausaya mishi kamata yayi ki amince ki aure shi, kai kadija ta dago ta kalle ta, tace kar ki manta tare ya ganmu amma ya zaba cewa ke yake so,

cikin fushi fatima tace to bana son shi, ko ana so dolene? kuma na rantse miki saina sa an hukunta shi, domin ya zame mishi darasi nan gaba, kadija tace ba damuwa Allah ya taimaka, tana fadin haka ta tashi ta fita,

washe gari da sassafe abdurrahaman ya dauki waya yakira habib, habib na dubawa ya daga gami da girgida kai, abdurrahaman yace hello abokina ya akayi ne? numfashi habib yaja yace normal, abdurrahaman yace wai jiyan nan ya kuka kare dasu ne? habib yace abinda kasani miye kuma na tambaya,

murmushi abdurrahaman yayi, yace malam habib kenan yanzu menene mafita? numfashi habib yaja, yace yadda Allah yay damu haka za ayi,

dariya abdurrahaman yayi, yace gaskiya abokina ina baka shawara kada kaje school yau, domin komai na iya faruwa, numfashi habib yaja, yace zanje domin na tabbatar ba kashe ni za suyi ba, abdurrahaman yace babu maganar kisa amma zasu kashe ma fatar jiki,

tsaki habib yaja ya kashe wayar shi ya koma ya cigaba da baccin sa, gari na gama wayewa ya tashi ya shiga wanka, yana fitowa ya shafa mai ya saka uniform, yana gama break fast ya dauki jaka yanufi school,




me karatu ya kake gani zata kaya, domin sanin hakan sai kayi kokari ka nemi cigaban labarin




from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp  08104550703
Read More»

Fateema Habeeb 16

Fateema Habeeb  16



                      na
Jamilu el hussain zazzau



             dedicated to
       Amina baba kaduna




5:00pm habib ya debi ruwa ya shiga wanka, yana fitowa ya shiga daki ya sami versiline dinsa mai kamshi ya shafa, sannan ya sami black trouser da red t shirt ya saka, explorer perfume ya fesa sannan ya sauki takalmi ya saka ya fito, kai tsaye ya nufi gidan su abdurrahaman,

yana zuwa ya iske abdurrahaman zaune a kofar gida yana jiran sa, yace sorry na bata lokaci ko? abdurrahaman yace lallai kam ka kusa makara, murmushi habib yayi yace to musa kai kawai,

tafiya suke suna fira kai tsaye su nufi copper's lodge, a bakin kofa su tsaya su rasa wanda zai shiga yakira musu ita, ana cikin haka sai ga copper yusif ya dawo daga cikin gari, da sauri su taso suzo su gasshe shi, yace wa kuke nema ne? suce copper fatima, yace ok bari nai muku magana da ita, suce thanks sir,

copper yusif na shiga ya iske fatima zaune acikin copper's suna fira, kallon ta yayi yace fati kinyi baki, da sauri ta watso mishi kallo itama, tace baki? murmushi yayi yace students dinki ne, tace oh shine zasu tsaya a waje, copper yusif yace to kila ko kunyar shigowa su keji tashi kije ki shigo dasu,

yunkurawa fatima tayi ta shiga daki ta dauko hijabi ta saka, kai tsaye ta nufi waje, tana fita ta iske su a tsaye, tace oh kune? fuska abdurrahaman ya saki yace wallahi kuwa, bayan sun gaisa tace lafiya ko? kadan abdurrahaman ya sosa kai yace qalau, dama munzo fada miki wani sako ne,

tace ok ina jinku, hannu abdurrahaman yasa cikin aljihun sa ya dauko wannan wasikar daya rubuta ya mika mata, yace ga wannan sakon dake tafe damu yana ciki, 

kallo ta watso mishi tace menene aciki? yace kar ki damu ki bude zaki gani, idan kin karanta habib zaki bama amsa, yana fadin haka ya kalli habib yace abokina minti daya ina zuwa, da sauri ya lallaba yaje jikin wata bishiya ya buya domin yaga abinda zai faru, fatima na budewa taga rubutu kamar haka,

   
         aminci agareki

dafatan kina cikin koshin lafiya kamar yadda nake, a gaskiya fatima tun ranar da Allah yasa nai tozali da kyakkyawar surar ki Allah ya jarabce ni da tsnanin sonki, wannan dalilin yasa nazo domin bayyana miki, ina mai fatan zan sami masauki acikin zuciyar ki, 

        daga masoyinki na har abada habib sani ss3B,

tana gama karantawa ta dago kai ta kalli habib tace waya rubuta wannan wasikar? numfasawa habib yayi yace nine, tun kafin ya rufe baki ta falla mishi mari, tace stupid baka da hankali ne, koka fara shaye shaye ne? idiot ni zaka dubi tsabar idona kace zakai soyayya dani,

da sauri ta koma cikin lodge din ta sanar da sauran copper's abinda ke faruwa, da sauri suka dungumo su fito domin suga wani students ne haka, suna fitowa su iske habib ko motsawa daga wajen da yake tsaye beyi ba,

kallon shi copper yusif yayi yace kai kayi wannan abin? kai habib ya daga yace eh, yusif yace oh dama abinda ya kawo ku kenan? shiru habib yayi yana kallon su kowa na fadan albarkacin bakin sa,

copper yusif yace baku da hankali, amma zakuyi nadamar abinda ku aikata, kusa da habib copper kadija ta matso takira copper yusif tace kunga ku mishi hakuri yanzu, idan ya sake saiku dau mataki,

kai copper yusif ya girgida yace no, bawani hakurin da zatayi dolene ya fuskanci hukunci domin nan gaba ya zame mishi darasi,

can gefe copper kadija taja habib tace mishi meyasa kai haka? hawaye ne suka fara zuba daga idanuwan sa yafara magana cikin rawar murya,




Domin samin littafin daga na daya zuwa inda mu tsaya saika tuntubeni ta wannan number dake kasa,



from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp  08104550703
Read More»

Friday, November 29, 2019

Fateema Habeeb 15

Fateema Habeeb  15



                     na
Jamilu el hussain zazzau


       dedicated to
   Amina baba kaduna



Habeeb na karisawa jikin katuwar bishiyar nan ya hau ya sauko da jakar sa dake gurin, daya bayan daya ya fara kallon hotunan fatima, yana gamawa ya mayar ya aje, duk abinda ya keyi abdurrahaman na makale ajikin wata bishiya yana kallon shi,

habib na mayar da jakar ya kama hanya ya nufi cikin school, ganin yayi nisa abdurrahaman ya fito daga wajen da yake, kai tsaye yaje ya hau bishiyar ya sauko da jakan,

bude wa yayi domin yaga abinda suke ciki, yana budewa yaga pictures din copper fatima ne aciki masu kyau tare da kalaman soyayya, kallon su yafara yi daya bayan daya, a bangaren habib kuwa harya kusa shiga cikin school zuciyar shi ta bashi cewa ya koma wajen jakar nan, kawai ya biye mata kai tsaye ya juyo,

tun daga nesa ya hangi abdurrahaman rike da hotunan nan yana kallo, harya iso wajen abdurrahaman baisan ya dawo ba, kadan habib yaja numfashi yace sannu da aiki,

a tsorace abdurrahaman ya zubar da hotunan ya waigo, yana waigowa yaga ashe habib ne ya dawo, yace oh dama baka wuce ba? habib yace ok dama jira kake na wuce kenan?

kai abdurrahaman ya girgida yace aa, habib yace tome ya kawo ka nan? abdurrahaman yace dama zuwa nayi naga wajen da kake zuwa kana hutawa,

murmushi Habeeb yayi, yace yaro nasan meya kawo ka saboda haka barina ja maka kunni, kada ka sake kaba wani wannan labarin, karfin hali abdurrahaman yayi yace haba ai baka isa ba wallahi, domin ina tashi daga nan gidanku zanje na fadawa maman ka, kaga yanzu shikenan zata san abinda ke damun ka,

cikin bacin rai habib ya kalle shi yace haka kace ko? tabbas saina fada musu, domin babu abinda zai hanani fada, kai habib ya girgida yace jikinka ko zai fada maka,

tsimagiya ya dauko ya tunkaro abdurrahaman da ita, ganin haka yasa abdurrahaman yay dariya yace matsala ta dakai bakasan wasa ba wallahi, jin haka yasa habib ya yar da tsimagiyar ya samu waje ya zauna,

kallon abdurrahaman yayi yace abokina tunda Allah yasa yanzu kasan abinda ke faruwa menene shawara? murmushi abdurrahaman yayi yace shawarar kenan kawai ka fito fili ka fada mata cewa kana sonta koma menene zai faru ya faru,

kai habib ya girgida yace wannan ba shawara bace, ko so kake akara azabtar dani? abdurrahaman yace bazata bari akara azabtar dakai ba muddin ta amince, habib yace to naji, idan kuma bata amince bafa?

kai abdurrahaman ya dago yace kar ka damu ni nasan yadda za ayi ta amince, habib yace ok, toya zamuyi mu tunkare ta?

abdurrahaman yace kaga kabar komai agurina zuwa nan da gobe, murmushi habib yayi yace kai amma gaskiya nayi matukar farinciki da zuwan ka,

tattara hotunan habib yayi ya mayar acikin jakar ya hau bishiyar ya sagale sannan ya sauko su kama hanya su koma cikin makaranta,

washe gari suna zaune a cikin class habib ya kalle shi yace ya maganar mu? abdurrahaman yace ban manta ba ai, amma ba'a school zamu fada mata ba kabari sai an tashi sai muje har copper lodged din mu sameta, habib yace ok Allah ya kaimu,

jim kadan abdurrahaman ya yagi wani fallen paper ya rubuta duk wasu bayanai dasu dace su fada mata, yana gamawa ya ninke ya saka a aljihu,

ana tashi school yace ma habib zuwa yamma idan ka shirya saika biyo ta gidanmu mu wuce, Habeeb yace ok ba damuwa sai anjiman,



Hammm me karatu shin ya kake gani, zata iya amince wa kuwa? domin tabbatar da hakan sai kuyi dakon cigaba,



from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp  08104550703
Read More»

Fateema Habeeb 14

Fateema Habeeb  14



                     na
Jamilu el hussain zazzau



             dedicated to
        Amina baba kaduna




Washe gari da sassafe habib ya shiga wanka, yana fitowa yay shirin school, sannan ya fito ya karya, jaka ya dauka zai fita malam sani ya harare shi yace idan kaso kar kaje school din ka wuce wani wajen,

kai tsaye habib ya kama hanya sai school, yana isa ya zame class,

displine na zuwa ya wuce wajen aikin da yasa habib domin ya duba ya gani ko yayi, yana zuwa ya iske habib ya gama aikin tsaf, girgida kai displine yayi yace lallai yaron nan yakai tantiri ace mutum ya gummace yay ta shan duka sai kace jaki, kai tsaye ya wuce office din principal yay mishi bayani cewa sir babu inda banyi da yaron nan ba, amma yaki fadamin wajen da yake zuwa,

principal yace kar ka damu jeka abinka ni nasan yanda zanyi dashi, domin naci uban wanda suka fishi gagara, ana tashi break principal yaje har class din su habib ya taso shi agaba zuwa office din sa,

kallo ya watso mishi yace sa guiwar ka akasa, da sauri habib yasa, yace inason kai min bayanin wajen da kake zuwa baka son zuwa school, domin kaga wannan yawon da kakeyi kanka kake zalunta,

shiru habib yayi yaki magana, tsawa principal ya daka mishi yace ba dakai nake magana ba? yace sir ba inda nake zuwa, murmushi principal yayi yace wato har yanzu baka daku ba kenan tunda kaki bayani,

rai abace principal ya kalle shi yace tashi ka kama kunninka awajen, ba gardama habib ya tashi ya kama, principal yay ta aikin shi har ya manta dashi, zuwa can hawaye suyi ta zubo masa kafafuwan sa sukai tsami ya yanke jiki ya fadi,

jin karar faduwar sa yasa principal ya dago dakai ya kalle shi yace ubanwa ya tashe ka? bulala ya dauko yafara tsula mishi, yana fadin dan ubanaka fadamin ina kake zuwa bakasan zuwa school, ihu kawai habib keyi yana fadin kayi hakuri malam babu gurin da nake zuwa,

jin haka yasa principal yace stupid kawai, tashi ka wuce class, da kyar habib ke tafiya, kai tsaye ya koma class,

bai jima da fita daga office din principal ba sai ga mahaifin sa yazo, bayan sun gaisa principal yay ma malam sani bayanin duk irin punishment din da suyi ma habib amma yaki fada musu wajen da yake zuwa, malam sani yace to ba damuwa ku kyale shi nagode, hannu ya bashi sukai sallama ya kama hanya ya koma,


5:pm malam sani ya dawo daga kasuwa, dai dai lokacin habib na zaune a tsakar gida rike da wani karamin littafi yana karatu, kallo ya watso mishi yace wato kaki musu bayani ko? na sake jin ance baka zuwa kagani nida kaina zan casa ka, shiru habib yayi baice komai ba,

washe gari Habeeb na gama shirya wa zai fita murja tace to habib dan Allah ka mayar da hankali kaji, yace to, tace a dawo lafiya, yana fita kai tsaye ya wuce school,

yana shiga class ya ajiye jakarsa ya fito, kai tsaye yanufi bayan gari wajen daya ajiye hotunan fatima, tun daga nesa abokin shi abdurrahaman ya hange shi, da sauri ya kama hanya ya bishi abaya,

zuwa can habib yaji kamar ana biye dashi, da sauri ya waigo  ya duba, abdurrahaman kuma yay sauri ya boye a jikin bishiya, ganin baiga kowa ba yasa ya cigaba da tafiya, abdurrahaman ya fito ya cigaba da binsa,



from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp  08104550703
Read More»

Wednesday, November 27, 2019

Fateema Habeeb 13


Fateema Habeeb  13



                      na
Jamilu el hussain zazzau




           dedicated to
     Amina baba kaduna




kallon habib principal yayi, yace jeka kiramin malamin dake kira muku rijista, da sauri habib yaje yakira malam ayuba su dawo tare,

kallon malam ayuba principal yayi, yace shin yaron nan na zuwa school? nadan lokaci kadan malam ayuba yay shiru, sannan ya girgida kai yace gaskiya ya kwana biyu bezo ba, jin haka yasa malam sani ya kalli habib cikin bacin rai yace to ina kake zuwa?

shiru habib yayi yaki magana, ganin haka yasa   malam sani yace ma principal malam buhari inason kuba yaron nan kashi har saiya fada muku gurinda yake zuwa, yana fadin haka ransa abace ya tashi ya wuce,

tsawa principal ya dakawa habib, yace idiot sa guiwar ka akasa,

sallama suji, copper yusif ne ya shigo yace sir akwai chalk anan kuwa? principal yace eh akwai, na staff yakare ne? copper yusif yace yes sir, principal yace ok kwasa da yawa katafi dashi, ya diba zai fita principal yace copper idan kaje kace ma displine yazo da sauri inason ganin shi, yace ok sir, yana zuwa ya fadama displine, da sauri displine yabar abinda ya keyi ya kama hanya,

yana shigowa yace gani sir, principal yace ok abinda nakeso dakai kaje da yaron nan kabashi kashi sosai har saiya fada maka gurinda yake zuwa baison zuwa school, displine yace ok sir, kallon habib yayi yace tashi muje,

agaba ya tasa shi zuwa office din shi, suna shiga yace sa guiwar ka akasa  dan ubanka, da sauri habib yay nildown, displine ya kalle shi yace to zaka fadamin ne ko saina sosa maka baya?

kadan habib ya dago kai yace babu inda nake zuwa, dariyar mugunta displine yayi yace yaro kenan, cire riga dan ubanka, a tsorace habib yacire rigar sa domin yasan halin displine din, ya rage daga shi sai singlet,

ko tausayi babu displine yay ta tsala masa dorina yana cewa zaka fadamin ko kuwa? nin shi kawai habib ya keyi yakasa magana, kafin kace wani abu yayi masa rudu rudu da jiki, duk dukan da habib yasha baisa ya fadi komai ba,

ganin haka yasa displine yace yaro idan kasan wata bakasan wata ba, fatanya ya dauka yace tashi muje, tsakiyar rana ya fita dashi ya nuna mishi wani katon fili cinkushe da ciyawa, yace kaga duk girman wajen nan kai zaka nome shi duka idan baka fadamin gurinda kake zuwa ba, ya mika mishi fatanyar yace gashinan fara nizan wuce office idan ka shirya fadamin saika ajiye fatanyar kazo office ka sameni,

dukawa habib yayi ya dau fatanyar ya dukufa noman ciyawa ko hutawa beyi, har lokacin tashi yayi displine bezo ya sallame shi ba, haka students kowa ya shiga wuce wa yana kallon shi, har students kowa ya gama wuce wa gida sai shi kadai ya rage yana ta famar aiki,

zuwa can displine yazo domin ya duba ya gani ko habib yayi aikin da yasa shi, yana zuwa ya taras habib yayi aikin tas  abin ya bashi mamaki, dariya yayi yace yaro kenan, wato kai dan taurin kai ko? ba damuwa, yanzu zaka fadamin ne kokuwa?

shiru habib yayi kamar ba dashi ya keyi ba, dariyar mugunta displine ya saki gami da nunawa habib wani katon fili yace tunda kace kai kangararre ne to yau anan zaka yini, dauki fatanya ka cigaba da aiki,

dukawa habib yayi ya dauki fatanyar ya nufi gurin, murmushi displine yayi yasa kai ya kama hanyar gida, duk a tunanin sa habib zai kira shi ya fada mishi, ko dago kai habib beyi ba ya cigaba da aikin,

duk school kowa ya watse, ya rage sai shi kadai ga yunwa ga gajiyan aiki, ga kuma zafin rana dake damunsa da kuma zafin dukan daya sha, sai misalin karfe biyar na yamma ya gama aikin,

yana gamawa ya dauki rigarsa ya saka yana tafiya da kyar yanufi gida, murja na zaune a inuwa tana hutawa habib ya shigo gida wujiga wujiga, tsabar tausayi har tana hawaye, tace habib bansan lokacin daka fara gagara ba, yanzu kaki fada musu gurinda kake zuwa ka gwammace aita dukan ka kamar jaki ko?

shiru yayi bece komai ba yasami waje ya zauna, kai tsaye murja ta tashi ta dauko mishi abincin sa,

6:00pm malam sani ya dawo daga kasuwa, yana shigowa ya iske habib ya baje  a tabarma yana huta gajiyar horon da yasha, hararan shi yayi yace shasha shan banza mai kunin kashi, mu zuba nida kai muddin kace gagara zakayi ni kuma zan cigaba da basu umarni suna baka kashi, a ranar habib yakasa zuwa ko ina saboda wahalar da yasha,




from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp  08104550703
Read More»

Fateema Habeeb 12



Fateema Habeeb  12



                      na
Jamilu el hussain zazzau



            dedicated to
       Amina baba kaduna




2 weeks letter, habib ya dauke kafa da zuwa school, kullum yay shirin school saiya zame can bayan gari gurinda ya ajiye hotunan fatima, bashi da aikin daya wuce zana hotunan ta da kuma jera baitocin soyayya,

ganin kwana biyu baizo school bane yasa abdurrahaman yaje har gidan su domin ya duba yaga ni ko lafiya yasa be zuwa,

yana shiga gidan ya iske murja zaune tana wanke wanke, sallama yay mata ta amsa,  tace malam abdul yau kaine agidan namu? yace eh umma, aciki ladabi ya gasshe ta, yace dama nazo duba habeeb ne,

da sauri murja ta dago kai ta dube shi dakyau tace wani habib kuma? shida ya wuce school tun  dazu, kai abdurrahaman ya girgida yace umma habib baizo school yau ba, hasalima ya kwana biyu bai zuwa, wannan dalilinne ma yasa nace bari nazo na duba nagani ko bashi da lafiya ne,

jin wadan nan jerin bayanan na abdurrahaman ya batawa murja rai sosai, kallo ta sake watso mishi, tace kaga abdul dan Allah kafada min gaskiyar abinda kasani,

rantsewa abdurrahaman yayi, yace wallahi umma habib yakai kusan sati biyu rabon shi da school, kuma a zahirin gaskiya bansan gurin da yake zuwa ba, murja tace nagode yaro jeka abinka zai dawo gidan zai fada mana gurin da yake zuwa, abdurrahaman yace to sai anjima, kai tsaye ya kama hanya ya koma school,

1:30pm atashi daga school, kai tsaye habib ya kama hanya yabi bayan dalibai yanufi gida kamar wanda yaje school, yana shiga gida ko zama baiyi ba murja ta daka mishi tsawa tace daga ina kake? yace daga school nake, tace rufe min baki makaryaci, dazun nan abokin ka yazo neman ka, yace kusan sati biyu kenan baka zuwa school din, shin ina kake tafiya?

kai habib ya dago yace wallahi karya ya keyi kullum sai naje, tace to shikenan bari mahaifin ka ya shigo na sanar dashi, daki habib ya shiga, tashi guda zufa yafara keto mar yana tunanin abinda zai biyo baya muddin mahaifin shi yasan bai zuwa school,

yamma nayi malam sani ya dawo daga kasuwa, kamar kullum murja taje ta tarbe shi ta kawo mishi ruwa mai sanyi da abinci, bayan ya huta ta kwashe labarin da abdurrahaman ya kawo mata tsaf ta fada mishi, nadan lokaci kadan malam sani yay shiru yana mamaki, sannan ya numfasa yace to shikenan tunda yace karya ne kibari gobe zan tasa keyarsa agaba muje makarantar domin na tabbatar da gaskiyan lamarin, tace to megida Allah ya kaimu, yace amin, sannan suka shiga wata firar,

washe gari da safe habib na gama shiryawa malam sani ya dauke bisa yamaya din shi sai school din, suna shiga yay parking su sauko ya tasa agaba sunufi office din principal, tunda ga waje yay sallama, principal yace yes ku shigo,

suna shigowa malam sani ya bashi hannu su gaisa, principal yace har yanzu wancen matsalar ce batakare ba? kai malam sani ya girgida yace ba ita bace, wannan wata matsalar ce kuma daban,

principal yace to inajinka meke faruwa? tsaf malam sani ya kwashe labarin da murja ta bashi ya fadawa principal, kai principal ya girgida yace babbar magana, barina aika akira for master dinsu muji koya abin yake,




from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp  08104550703
Read More»

Fateema Habeeb 11

Fateema Habeeb   11




                    na
Jamilu el hussain zazzau




           dedicated to
    Amina baba kaduna




washe gari habib na gama shirin school mahaifin shi ya dauke shi a mashin dinsa suka nufi makarantar,

suna shiga harabar school din ya samu waje ya faka mashin din ajikin wata bishiyar dogon yaro dake harabar school din, kai tsaye ya tasa habib agaba sunufi office din principal,

sallama yayi, principal yace bissimilah ku shigo, suna shigowa malam sani ya mika masa hannu su gaisa, sannan ya samu waje ya zauna, habib kuma na gefe yana tsaye,

duk irin halin da habib ke ciki malam sani ya kwashe ya fadawa principal, kadan principal ya dago kai ya kalli malam sani yace gaskiya yanzu ayyuka sun min yawa, saboda haka bazan iya sauraran wannan case din ba, amma yanzu barina hadaka da class master din su domin ya bincika ma,

kallo principal ya watso ma habib, yace jeka staff ka kira min malamin ajinku, da sauri habib yaje staff yakira malam ayuba su dawo tare,

kallon malam ayuba principal yayi, yace malam ayuba wannan bawan Allah da kake gani mahaifin yaron nanne, yazo yay min bayani cewa yaron shi na cikin damuwa matuka, kuma yana tunanin matsalar  daga nan school take, saboda haka abinda nake so dakai katasa keyar yaron nan kuje ka bincike shi yafada maka abinda ke damun sa,

malam ayuba yace ok sir,   kallon habib yayi yace wuce muje, habib na gaba malam ayuba na biye dashi sutafi class din su,

suna shiga students su mike duk su gasshe shi, yace ku zauna, kallon su yayi ya nuna habib yace kunsan wannan? duk su hada baki suce eh, yace ko akwai abinda ya hadashi da wani acikin ku? class kowa ya girgida kai yace aa,

mikewa monitan class din yayi, yace sir gaskiya akwai abinda ke damun shi kwana biyun nan, domin kullum ya shigo class baya kula kowa saide ya koma gefe yay ta tunani, ko walwala beyi da jama'a, kallo malam ayuba ya wurgo ma habib yace mu koma,

agaba ya taso shi su dawo office din principal, kallon su principal yayi yace ma malam ayuba ya akayi? dalla dalla malam ayuba yay mar bayani, principal ya kalli malam sani yace to megida kadai jiko?

malam sani yace eh naji, principal yace to zaka iya komawa idan ya sanar damu zamu nemeka muyima bayani, malam sani yace to madalla nagode, ya basu hannu su gaisa ya fito daga office din, kai tsaye yaje ya dauki mashin din sa yanufi gida,

mahaifin habib na fita principal yakira displine master yace kaga yaron nan akwai abinda ke damun sa, iyayen sa sunyi sunyi dashi yaki fada musu shine su taso keyar shi zuwa makaranta, muma nan mun tambaye shi yaki fada mana, saboda haka abinda nakeso dakai ka tasa shi agaba kuje saiya fada maka,

displine yace ok sir, fuska ya daure ya dakawa habib tsawa yace wuce muje, kai tsaye ya tasa habib zuwa office din shi, suna zuwa yasa habib yasa guiwar sa akasa shi kuma ya jawo kujerarsa ya zauna, sannan ya dauko wata dorina mai baki biyu ya ajiye kusa dashi,

hararan habib yayi, yace to zakai min bayani ko saina zaneka? dago kai habib yayi, yace sir nifa ba abinda ke damuna, barazana displine yay tama habib amma duk da haka baisa habib ya fadi komai ba, ganin haka yace mishi tashi mu koma,

kai tsaye ya taso shi su dawo office din principal, suna dawowa yace ma principal nima nayi nayi dashi yaki fadamin, kallon habib principal yayi, yace tunda kace babu abinda ke damunka tashi ka wuce class, jaka habib ya dauka kai tsaye ya wuce class din su,

zuwa yamma bayan an tashi daga makaranta principal su hadu da mahaifin habib a kasuwa yay mishi bayanin duk yadda su kayi da habib amma yaki fada musu, malam sani yace nagode ba damuwa, sukai sallama ya wuce,




from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp  08104550703
Read More»

Fateema Habeeb 10

Fateema Habeeb  10



                      na
Jamilu el hussain zazzau



         dedicated to
    Amina baba kaduna




Shiryawa  yayi zai tafi school mahaifiyar shi tace habib, yace na'am umma, tace wai meke damunka ne? kadan ya saki fuska yace bakomai,

tace ya zakece min bakomai bayan yanayin yadda kake harkokin ka duk sun canza, kadan ya sosa keya yace umma zazzabi ne kawai ke damuna 'yan kwanakin nan, tace to naji kana shan magani kuwa? eh ina sha umma, tace to Allah ya baka lafiya, yace amin, kai tsaye ya kama hanya ya wuce school,

Habib gwani ne wajen drawing, idan ya zana maka hotan mutum sai kaga kamar ka kira sunan sa ya amsa, idan hotan muto ya zana kuwa sai tayi kamar ai mata key tai tafiya,

zuwa yamma bayan an tashi daga school habib ya fasa asusun shi, kaf kudin dake ciki ya kwashe ya nufi kasuwa, wasu manyan  drawing books ya siyo gami da kwalin colours da kuma pencil, sannan ya sayi wata jaka ya zuba su aciki kai tsaye yanufi can bayan gari gaba da school din su,

jikin wata katuwar bishiya ya samu ya zauna, dama gurin bishiyar yake zuwa shakatawa idan ya bushi iska, kayan drawing dinnan ya fito dasu a tsanake ya zana hotan copper fatima, haka hotan yay kyau kamar wacce ta tsaya a dauke ta,

yana gama zana hotan ya koma kasan hotan yay ta jero baitocin soyayya, yana gamawa ya mayar da kayan cikin jaka ya zage zip, saman bishiyar ya hau ya sakale jakar  sannan ya sauko ya kama hanya yanufi cikin gari,

tun daga wannan ranar kullum habib sai yaje gurin jakar nan yayi drawing fatima, wani lokacin yaje ya sauko da jakar ya zuba ma hotunan ido yay ta kallo,

kafin wani lokaci habib yafara ramewa, wannan dalilin yasa murja ta sanar da malam sani cewa megida ya kamata ka zaunar da yaron nan domin kaji abinda ke damun sa, domin ni nayi nayi dashi yaki fadamin,

kallon ta malam sani yayi yace ina habib din? tace yana dakin shi, yace kira min shi, yunkurawa murja tayi ta mike tanufi dakin habib, tana lekawa ta iske shi zaune ya zabga uban tagumi, tace aikin kenan, sai kazo baban ka nakira, yace to, gaba tayo ya biyota abaya,

suna zuwa malam sani ya kalle shi yace samu waje ka zauna, habib na zama mahaifin shi ya kalle shi yace wai shin kai meke damunka ne? domin 'yan kwanakin nan duk ka canza mun rasa gane maka,

kai habib ya girgida yace ba komai baba, malam sani yace kodai kayi fada da wani a school dinne? yace aa, yace to naji waya bata maka rai? nifa baba babu abinda ke damuna, malam sani yace to tashi kaje abinka,

kallon murja malam sani yayi yace bansan yaran nan da taurin kai haka ba, amma tunda yaki fada mana ko abokansa ma tambaya, watakil su bazasu rasa sanin abinda ke damun shi ba, murja tace to shikenan zan aika akira min abokan nasa,

zuwa yamma murja ta tura yaro har wajen business din abdurrahaman tasa akira shi, da sauri abdurrahaman ya kama hanya yazo, cikin ladabi ya gasshe ta, sannan ta dago kai ta kalle shi tace malam abdul lamarin abokin ka yafara bamu tsoro, domin ya shiga wani mawuyacin hali wanda mu kanmu iyayen shi yaki fada mana abinda ke damun sa, wannan dalilin yasa na aika kazo, domin wata kila ko kai yafada ma wani daga cikin ku,

kadan abdurrahaman yaja numfashi, yace wallahi umma nima famar da nake tayi dashi kenan, tabbas habib na cikin damuwa, amma nima na tambaye shi yaki sanar dani, numfasawa murja tayi, tace to shikenan nagode abdul jeka abinka, mikewa abdurrahaman yayi yace sai anjima ya koma wajen kasuwancin sa,

yamma nayi malam sani ya dawo daga kasuwa, da sauri murja ta fito da tabarma ta shimfida sannan ta dau kofi ta debo masa ruwan sanyi, sannan taje ta kawo mishi abincin shi,

bayan ya huta ta fada mishi duk yadda suyi da abdurrahaman abokin habib, yace to ba damuwa kibari gobe zan tasa shi agaba mutafi school din nasu naji ko acanne matsala ta hadashi da wani, tace to megida Allah ya kaimu, yace amin,  sannan su shiga wata firar,




from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp   08104550703
Read More»

Fateema Habeeb 09

Fateema Habeeb  09



                     na
Jamilu el hussain zazzau




           dedicated to
      Amina baba kaduna




kawa exam master din school din nanne yakira ni har office din shi yafada min cewa yana sona, kadan kadija taja numfashi tace toke me kice mishi? no ban bashi amsa ba, kawai ce masa nayi ya bari zanyi shawara,

ke kuwa meya hana ki bashi amsa lokacin? kallo fatima ta watso mata, tace wani irin amsa kike ganin ya dace na bashi? murmushi kadija tayi, tace kawai kice kin amince, da sauri fatima ta katseta tace bazan iya wannan shiriritar ba, domin zuciya ta bata da masaukin sakonnin kowa idan bana kamal ba,

kadija tace to shikenan sai kiyi tunanin amsar da zaki bashi, numfashi fatima taja gami da gyara kwanciya taja mayafi,


one week letter, exam master ya sake kiran fatima zuwa office din shi, bayan sun gaisa yace copper naji ki shiru ko har yanzu baki gama yanke shawarar bane? kallo ta watso mishi tace sir kayi hakuri inada wanda nake so, kuma gaskiya mun shaku sosai,

yatsine fuska yayi yace haba fatee kar kiyi min haka mana, ko dai ban miki bane? no sir bahaka nake nufi ba, anriga anmin miji, kai ya girgida yace a zahirin gaskiya bazan iya hakura dake ba, kallo ta watso mishi tace oh haka kake gani? yace of course,

jin haka yasa tai wuf ta fice daga office din tanufi staff, tana shiga staff ta iske copper yusif da kadija zaune suna fira, ganin ta cikin yanayi na damuwa yasa kadija ta tambayeta kawa meke faruwa? muryar ta na rawa ta fada musu,

murmushi kadija tayi, tace ba soyayyar wasa bace kawai saida na fada miki ki amince kin ki gashi yana son ya takura miki, bata rai copper yusif yayi ya kalli kadija yace haba meyasa kike irin wannan maganar ne? fada miki tayi soyayya ya kawo ta, please ki daina irin wannan,

kallon fatima yayi yace sorry ko, kada ki damu idan ya sake aikawa kizo kar kije, idan kiga zai takura miki ki sanar dani, thanks brother tace, sannan ta sami waje ta zauna,

cikin kan kanin lokaci da yawan malaman school din su shiga nunawa fatima soyayyar su afili sam taki amince wa, haka shima a bangaren habib kullum soyayyar fatima kara jefa shi cikin rudani ta keyi saide kash shiya kasa furta mata, domin yana tsoron sakamakon dazai biyo baya,

zaune habib suke shida friend din shi abdurrahaman suna fira, yace abokina dama ko akwai tambayar da nake son nai maka? kadan habib ya saki fuska yace ina jinka? abdurrahaman yace a gaskiya abokina kwana biyu na kasa gane maka, domin duk ka canza, mu'amullar ka ba irin daba, meke damunka ne?

nadan lokacin kadan habib yay shiru, sannan ya dago kai ya kalle shi yace shikenan tambayar naka? abdurrahaman yace eh, numfashi habib yaja gami da cewa gaskiya bani da cikakkiyar amsar dazan iya gamsar dakai,

kallo abdurrahaman ya watso mishi yace me kake nufi da haka, bayan ka daina mayar da hankali a class ko notes a bayar bakason yi,

bata rai Habeeb yayi yace na fada maka bansani ba, kuma banson karin wasu tambayoyi akai, abdurrahaman yace ok haka kafiso? habib yace eh, yace to shikenan idan ta fasu zamu ji ai,

murmushi habib yayi yace da yafi maka alheri, sannan su cigaba da firar su,

yanayi da tsarin zubin hallitar fatima dolene mutane suyita fadawa soyayyar ta batare da sun ankare ba, wannan dalilin ne yasa shima Habeeb ke yawan tsintar kansa acikin rudani saboda yawan tunaninta da yakeyi, domin daka ganshi zaka iya fuskantar cewa yana cikin damuwa,




from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp   08104550703
Read More»

Fateema Habeeb 08

Fateema Habeeb  08



                     na
Jamilu el hussain zazzau



          dedicated to
     Amina baba kaduna




Gaban class ta tawo  ta kalli students tace waye zai fada mana ma'anar  volcanic city a hausan ce?

daga hannu wani yayi, tace fada mana, yace babban birni, murmushi tayi tace bahaka bane, saiwa kuma? wani ya sake dagawa, tace to kai fada muji, yace karamin birni, class su tuntsere da dariya, tace kuyi shiru ya isa haka, tunda kun kasa bari na fada muku,

jin haka yasa Habeeb ya daga hannu, tace to kaine last fada muji, yace girgizan kasa, tace good ku tafa mishi, raf  raf  raf  class duk ya dau  tafi,

tace ko zaka iya fada mana kasa daya da aka taba yi? yace eh, tace to muna jinka, yace China, tace dakyau ku tafa mishi, atare su kara tafa mishi,

lesson ta cigaba dayi, zuwa can taji sautin kararrawa tace to time dinmu ya kare ko, sai mun  hadu a darasi nagaba, da sauri class captain ya dauka mata books dinta ya bita dashi zuwa staff,

tana shiga staff ta iske kadija har ta dawo ta zauna, zuwa can su sake duba time table su koma wasu classes din, 1:30pm time keeper ya buga kararrawar tashi students kowa ya fito yanufi gida,

before one week labarin copper fatima duk ya zagaye fadin school din, da yawa cikin malaman makarantar sun fara tunanin yadda zasu kulla soyayya da ita, daga cikin wanda su fada soyayyar fatima har da exam master na school din,

10 days da zuwan fatima exam master ya kasa hakuri yasa akira mishi ita, da suri fatima ta kama hanya tazo, sallama tayi ya amsa cikin fara'a ya nuna mata kujera yace ga wajenan  zauna ko, tana zama ya dago kai ya kalle ta yace copper ya aiki? kadan tai murmushi tace lafiya,

numfashi yaja, yace amma baki da aure ko? ras gaban ta yafadi ta girgida kai tace eh sir, murmushi yayi yace good haka nake son ji, kallo ya watso mata yace a zahirin gaskiya bazan boye miki ba tunda kuzo wannan school din idanuwa na sukai tozali da wannan kyakkyawan surar taki naji na kamu da sonki a zuciya ta,

saboda haka idan zaki amince zan jira harki gama service dinki muyi aure, shiru fatima tayi tana sauraran shi ko uhum ta kasa cewa, kallo ya watso mata yace yadai naji kinyi shiru? tace no bakomai, amma kabari zanyi shawara tukun,

yace to ba damuwa sai naji ki, tace to, mikewa tayi ta koma staff, har atashi school abin na damunta, cikin dare kowa ya kwanta amma ita tana rungume da fulo tana tunani,

zuwa can kadija ta farka, taga fatima rungume da fulo tayi tagumi, tace kawa lafiya kuwa? kadan fatima ta girgida kai tace bakomai, kadija tace zadai ki boye min dai, amma gashi nan fuskar ki ta nuna alamun damuwa, numfashi taja tace hakane, friend gaskiya akwai abinda yake damuna, kadija tace to ina jinki  menene haka?



from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp  08104550703
Read More»

Fateema Habeeb 07

Fateema Habeeb  07



                    na
Jamilu el hussain zazzau



         dedicated to
    Amina baba kaduna




su fatima na shiga staff kowannen su yaka shirya lesson plan din shi, ana dawowa daga break kowannen su ya duba time table ya tafi class din da yake dashi, kai tsaye fatima ta nufi ss 3B rike da books a hannun ta,

SS 3B shine class din dake da wani student mai suna Habeeb sani, habeeb dalibi ne mai kokari sannan ga kaifin basira, yana da tsafta kuma yana da natsuwa,

cikin siririyar murya fatima tai sallama ta shigo class din, jin sautin muryar fatima yasa habeeb ya dago kai da sauri domin yaga wacece haka,

soyayya kenan, da kallon farko yaji ya afka wani irin ya nayi akanta, tashi guda zuciyar sa tafara jero mishi wasu tagwayen tunani, cewa habeeb wannan ba kalar ka bace, domin ta nada degree kaiko ko secondary school baka gama ba,

daga ganinta diyar masu halice, kai kuwa dan gidan talaka ne fitik, wadan nan suna jerin tunanin da suyi ta yawo a cikin zuciyar habeeb daga ganin fatima,

atare students su mike su gasshe ta, tace ku zauna, tashi guda kyau da kwarjin fatima ya haska duk wani students dake cikin class din, mazan class din na tunanin ina ma ace students ce ita suyi soyayya, matan kuma na kwadayin kulla kawance da ita,

da sauri class captain ya dauko dosta ya share mata black bord, chalk fatima ta dauka ta sami gefen black bord din ta rubuta sunan subject din da zatai musu, geography, sannan ta dawo kasan shi ta rubuta sunan topic earth revolution,

tana gama rubutawa ta juyo ta kalli students, tace kafin mu shiga lesson inason  kowannen ku ya tashi yay min introducing din kan shi, ta nuna kujerar farko tace bari mufara daku,

anan kowa ya tashi yana fadin sunan sa dana mahaifin sa, seat by seat har akazo kan habeeb, habeeb na mikewa domin gabatar da sunan sa yaji kansa ya juye, domin tunda sukai ido biyu da fatima yaji wani kibiyar so ya soki zuciyar shi,

tashi guda yaji jikin sa yay sanyi, gaban sa sai faduwa ya keyi kamar wanda yay laifi, shiru kawai yayi ya kasa cewa komai, kallo fatima ta watso mishi tace kai sauri kai muke jira, tsit class din yayi kowa yay shiru ya koma kallon habeeb,

ganin haka yasa fatima tace class ko kurma ne? students suce aa anty ba kurma bane yana magana, tace ok zauna tunda bazaka fadi sunanka ba, zaunawa habeeb yayi, haka a tsallake shi na kusa dashi su cigaba har agama,

kallo ta watso ma habeeb tace malam naji sunan kowa, kai kadai ne banji naka ba, kadan habeeb ya sunkuyar da kansa kasa, ganin haka yasa students da sauri suce malama sunan shi habeeb,

yatsine fuska fatima tayi, tace ku rufe min baki shi baida baki ne? matsawa tayi zuwa wajen shi ta dafa kan shi tace hala baka jin dadi ne? kadan ya dago kai yace eh, jikina ne yadan canza min,

tace eyyah sorry, kasha magani ko? kai ya girgida yace aa, tace to jeka amsa magani mana, kadan ya numfasa yace bakowani irin cuta ake samun maganin sa acikin school ba,

kallo ta wurgo mishi tace wani irin cuta ne haka? kadan yay ajiyar zuciya yace Allah kadai yasan abinda ke damuna, na dan lokaci kadan fatima tai shiru gami da ajiyar zuciya, tace to Allah ya baka lafiya, yace amin,




from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp  08104550703
Read More»

Fateema Habeeb 06

Fateema Habeeb  06



                 na
Jamilu el hussain zazzau



          dedicated to
     Amina baba kaduna




Tafiya kawai su keyi abinsu suna fira, suna ganin ya nayin garin, gab da sallan magrib su kamo hanya su koma masaukin su,

small gas cooker din su sufito dashi su dora abinci, few minutes yayi su sauke, sannan kowa taje tai sallah, suna idarwa su dauko abincin suna ci suna fira har su gama, bayan sunyi sallan isha kowa ta kwanta saboda gajiyar hanya,

6:00am kadija ta farka, tana duba agogo taga lokaci yaja, da sauri ta tashi fatima suje sukai sallah, suna idarwa su dora ruwan zafi su hada kayan break fast,

suna gama karyawa fatima ta shiga toilet tai wanka, tana fitowa itama kadija ta shiga, bayan sun shirya kowa ta dauki kayan bautar kasanta ta saka, zuwa 7:30am su fito kai tsaye sunufi cikin school din,

suna shiga school din suka tambayi gurin da staff yake, daga can akai directing din su zuwa principal office,

sallama suyi, yace yes shigo, suna shigowa kowa ya samu waje ya zauna, bayan sun gaisa suka mika mishi shaidar bautar kasar su,

yana gama dubawa ya rubuta ma kowa list classes din dazai koyar, geography fatima ta dauka, kadija kuma maths sai yusif economics, bayan  kowa ya amsa time table suka fito daga nan su koma staff,

8:00am time keeper ya buga kararrawa, da sauri students suka nufi assembly, dai dai lokacin seniors suzo suyi ta control din students before malamai su kariso,

jim kadan principal ya taso daga office din sa yanufi staff suka tattauna abubuwan daza su fadama students,

bayan sun gama yayo gaba sauran teachers suka biyo shi abaya zuwa assembly, suna isowa duty preefect yazo ya gabatar da pray da kuma national anthem, yana sauka principal yafara jawabi kamar haka,

da farko muna godiya ga Allah da yasa mu wayi gari lafiya, sannan har kullum ina kara jawo hankulan ku kowani dalibi yayi koyi da kyawawan dabi'u,

banda zuwa school a makare, kadan ya juyo da kan shi zuwa yan mata yace especially ku nasha nanata muku akan sanya guntun hijabi amma da yawan ku basaji, to daga yau duk wacce ta sake mu kwace nata zamu kona,

abu na gaba kuma idan kun duba saman assembly zaku ga sababbin malamai da government ta sake turo mana, saboda haka kowa bari mu bashi dama ya gabatar da kan shi,

waigo dakai  principal yayi ya kalli su fatima yace bissimilah kowa yay introducing din kan shi ga students, yusif yafara gabatar da kan shi, sannan sai kadija sai kuma fatima itama tayi daga karshe,

bayan sun gama principal yace to abinda nake so daku suma kuyi musu biyayya kamar yadda kuke mana, bama son su kawo mana karar wani cewa ya musu rashin da'a saboda haka akula,

yana gama jawabi duty prefect ya dawo ya gabatar da national pledge, students kowa ya wuce class din shi, malamai kuma su koma staff,




from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp   08104550703
Read More»

Fateema Habeeb 05

Fateema Habeeb  05



                     na
Jamilu el hussain zazzau




           dedicated to
   Amina baba kaduna




4:00pm suka isa garin saminaka,
saminaka babban garine, dake da attajirai da yan kasuwa da kuma manyan manoma,

Government secondary school dake garin atura su fatima, suna shiga garin sukai tambaya direct a nuna musu gurin da makarantar take,

suna isa school din su iske bakowa an riga an tashi, sai wani class guda daya dake da mutane aciki suma meeting din addini ya dawo dasu,

waje suka samu sukai parking su sassako,
ganin su yasa wani teacher daga cikin masu meeting din nan ya taso yazo,

bayan sun gaisa sukai mishi bayanin komai game dasu, waya ya dauka yakira principal ya fada mishi, principal yace ok jeka ka kaisu masauki,

teacher din yace to muje ko, yay gaba suka bishi abaya zuwa copper's lodge, suna isa suka iske masu bautar kasa da yawa wadan da aka turo daga wasu states din,

hostel din da zasu  zauna ya nuna musu, sannan yasa a kawo musu abinci,

jim kadan da gama cin abincin su fatima ta dauki waya takira kamal, dai dai lokacin sahibin na kwance bisa katuwar katifar sa yana tunanin ta,

da sauri yasa hannu ya dauko wayar, gami da tausasa murya ya kara a kunni, hello sahiba, murmushi tayi cikin sassanyar murya tace na'am hubby yakake? qalau nake har kun sauka kenan?

eh wallahi yanzu ma haka muna cikin masaukin mu, ajiyar zuciya yayi, yace tanx god toya gajiyar hanya? kadan tai murmushi tace gaskiya garin akwai nisa mungaji sosai,

yace oh Allah sarki, to yanzu abinda ya dace kije ki watsa ruwan sanyi sannan ki kwanta ki huta ko, tace umhum sai anjima, yace ok bye, cike da jindadi ta sauke wayar sannan ta lalubo number mom dinta ta kira,

dai dai lokacin hajia na zaune a falo nusaiba na mata tausa, fuska cike da annuri hajia ta daga wayar, hello maman baban ta har kun isa kenan? murmushi fatima tayi tace eh mom, hajia tace ok toya hanya? tace lafiya qalau mom, hajia tace yayi kyau toya ya nayin garin?

kadan ta numfasa tace ba laifi garin yana da dan girma ba kauye bane sosai, hajia tace ok yayi kyau, sannan ta mikawa nusaiba wayar su gaisa,

suna gama wayar ta yunkura ta dauko bokiti ta debi ruwa ta shiga bandaki ta watsa, tana fitowa ta gyara katifa ta kwanta, kadija na zaune kusa da ita suna fira har bacci ya kwashe ta, ganin bacci ya kwashe fatima yasa kadija ta fito waje gurin sauran copper's su cigaba da fira,

zuwa faduwar rana fatima ta farka, tana farkawa ta sake diban ruwa ta shiga toilet tai wanka, tana fitowa ta bude jakarta ta dauko lotion mai kamshi ta shafa,

sannan ta dauki dogon siket ta saka gami da wata karamar t shirt mara nauyi, wani karamin mayafi ta yafa ta fito, dai dai lokacin itama kadija ta gama shiryawa, kai tsaye su fita cikin gari,




from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp    08104550703
Read More»

Fateema Habeeb 04

Fateema Habeeb  04



                     na
Jamilu el hussain zazzau




            dedicated to
     Amina baba kaduna



Cigaban labari

Washe gari da sassafe fatima ta tashi tai sallah, tana idarwa ta shiga toilet tai wanka, kafin ta fito nusaiba ta riga ta gama shirya musu break fast,

suna gama karyawa dad din su yasa akira mishi ita, fatima na shigowa ta gasshe shi cikin ladabi, sannan yafara yi mata nasiha kamar haka,

me sunan mama yanzu kin manyan ta, kin fara sanin abubuwan dasu dace da kuma wadan da basu dace ba, saboda haka abinda nake so dake shine ki kula da kan ki, ki kasance mai kamun kai aduk inda kike,

sannan ki rike ibada da kyau kada kiyi wasa da sallah, banda kuma yin kawayen banza, domin kinga wannan garin da zakije bakon wuri ne, idan kin kula da kan ki Allah zai taimake ki,

tace insha Allahu zan kula, yace to Allah ya miki al barka, tace amin dad, tana fitowa daga nan ta shiga dakin hajia, kallo hajia ta watso mata tace to fatee sai akula sosai,

banda yawace yawace, sannan kuma ina kara jan kunnin ki cewa ki rikewa kamal alkawari, murmushi fatima tayi tace insha Allah mom,

Cikin falo ta dawo ita da nusaiba su zauna, jim kadan sai ga kamal ya iso, yana parking ya kirata a waya, da sauri ta yunkura ta fito taje ta same shi,

tun daga nesa ta jefo mishi kallo cikin shagwaba, murmushi sahibin yayi yace har kin shirya ko? tace uhm, da wuri na tashi ai, sakin fuska yayi gami da ajiyar zuciya,

sannan ya cire zoben dake hannun sa ya mika mata, cike da annashuwa ta amsa ta saka, sannan itama ta cire nata ta mika mishi, yace wannan shima zai kara taimaka mana akoda yaushe wajen tunawa da juna,

ajiyar zuciya fatima tayi, tace hakane, kamal ya jefo mata wani kallo cikin yanayi na tausayi, yace tawan zan rike miki amana bazan soyayya da kowace mace ba, saboda haka kema inason ki rike min irin wannan alkawarin,

cikin sassanyar murya tace hubby kada ka damu zan rike maka amana aduk inda nake a fadin duniyar nan, kamal yay murmushi yace nagode Allah ya barmu tare, tace amin, fira su cigaba dayi har lokacin wucewar ta yayi,

kanta tsaye ta shiga cikin gida, kamal na tsaye jikin motar sa yana jiran ta,

tana shiga gida ta shiga dakin mom domin suyi bankwana, rungume ta tayi tana kuka, hajia tace to kiyi shiru haka ko, da sauri nusaiba da bashir su dauka mata kayan ta zuwa kofar gida,

but kamal ya bude ya saka kayan, har wajen mota hajia ta rako  fatima, kamal na ganin fitowar su da sauri yazo cikin ladabi ya gasshe da hajia,

kofa ya budewa fatima ta shiga gidan gaba, nusaiba da bashir su zauna a kujerar baya sannan yay ma motar key su wuce,

jim kadan suka isa school din, suna zuwa su iske students kowa ya hallara motocin tafiyar kawai ake jira, jikin wata bishiya kamal da fatima suje su sami kujera su zauna, babu abinda su keyi sai musayar kalaman soyayya,

jim kadan motocin daza su kwashe su suka iso, motar daza ta dauki su fatima na isowa kamal ya rakota har bakin kofar motar, tana zama ya kalli yusif dake zaune kusa da ita yace abokina ga kanwa nai maka ka kula min da ita, murmushi yusif yayi yace kar ka damu,

kowa na gama shiga direba yay key su kama hanya, kamal da fatima sai kallon juna suke ta mirror har motar ta kule,

kamal na tsaye ya dafa motar sa yana tunanin ta, kadan nusaiba tai murmushi tace yaya kamal ai sun wuce mutafi ko, numfashi yaja sannan yay murmushi shima yace ku shiga mu wuce,

da sauri su shiga motar ya mayar dasu gida,

misalin karfe biyun rana kamal yakira ta awaya, tana dubawa tace dan halak kamar kasan kai nake tunani, tana dagawa tace hello hubby,

yace na'am kun isa kuwa? tace aa wallahi har yanzu muna hanya, yace wai ashe garin da nisa, tace wallahi kuwa, yace to shi kenan Allah ya sauke ku lafiya, tace amin,

yace to saina kara kiran ki zuwa anjima, tace ok hubby nagode,




from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp  08104550703
Read More»

Fateema Habeeb 03

Fateema Habeeb  03



                    na
Jamilu el hussain zazzau




         dedicated to
    Amina baba kaduna




Nusaiba ce tare da hajia zaune acikin falo suna fira fatima tai sallama ta shigo, fuska cike da annuri nusaiba ta amsa,

kai hajia ta dago ta kalleta tace kin dawo? kadan fatima tai murmushi tace eh mom, kallo nusaiba ta watso mata, tace anty kun kusa wuce wa kenan? tace eh one week kawai ya rage mana,

waje ta samu ta zauna, hajia tace ba zama zakiyi ba sallah ya kamata ki shiga kiyi  sannan kici abinci, inyaso kya dawo ki zauna, fatima tace to mom, jaka fatima ta dauka ta wuce daki,

tun daga wannan ranar kullum kamal sai yazo gidan su fatima, yazo suyi ta dibar fira kamar baza su rabu ba,

ana gobe fatima zata wuce bautar kasa kamal yazo gidan da yamma, waje ya samu cikin farfajiyar gidan ya faka motar sa, sannan ya sauko kansa tsaye ya nufi cikin gidan,

sallama yayi hajia dake zaune a falo ta amsa, kamal kaine ke tafe? cikin annurin fuska yace eh mom, sannan ya gasshe ta, tace mutumiyar taka na ciki tana shirye shiryen tafiya,  yace to, kan shi tsaye ya nufi cikin dakin,

kadan ya lankwasa murya yay sallama, cike da fara'a sahibar tai fara'a ta amsa, tace hubby well come, yace my dear anata shirin tafiya ko? tace wallahi kuwa,

waje ya samu ya zauna su cigaba da shirya kayan tare, kadan ya dago kai ya kalle ta idanuwan sa cike da kwalla yace fatee zaki aure ni? da sauri ta dago kai ta kalle shi tace hubby wannan maganar kuma a ina katsinto ta?

murmushi yayi, yace baki amsa min tambayata ba, tace to naji, nima zan maka tambaya kafin na amsa maka taka, yace to inaji

hannu tasa ta rufe fuska, tace hubby kana son zama uban 'yayana? ras yaji gabansa ya fadi, da sauri yace eh na amince, duk kunya ta kamasu suka kyal kyale da dariya, sannan su cigaba da shirya kayan,

6:30pm yace mata tawan zanzo na wuce, amma da sassafe zan zo muyi sallama kafin ku wuce, tace ok muje na taka ma,

atare su fito yay ma hajia sallama, har wajen da yay parking fatima ta rako shi, saida ya wuce sannan ta koma cikin gida,

9:00pm fatima subar dinning, direct su wuce toilet suyi brush, sannan su fito kowa ta saka rigar bacci su kwanta,

kallon fatima nusaiba tayi, tace anty shikenan bautar kasa zai raba wasu masoya, murmushi fatima tayi, tace ba gaki ba idan na mutu a can, kinga sai abashi ke, dariya nusaiba tayi tace to ni kuma nawa saurayin fa? kadan fatima ta saki fuska, tace saiya haqura,

nusaiba tace tab, hakan ma bazaiyu ba, sukai murmushi tare, sannan su cigaba da fira har bacci ya kwashe su,


       Hasken Labari

wacece fatima?

fatima haifaffiyar garin minna ce, sunan dad dinta alhaji abdallah, mom dinta kuma hajia zainab, tana da kanni biyu, nusaiba dake binta sai autan su bashir,

alhaji abdallah banufe ne, ita kuwa hajia zainab bafulatana, sak fatima mahaifiyar ta ta biyo, fara ce siririya, sannan ga hanci kamar biro, taji hausa kamar wacce aka haifa a kano,

tayi primary schools da secondary duk acikin anguwar su dake tunga minna, daga nan ta wuce federal university minna inda anan ta sami damar yin degree,

bayan  ta gama ne aka tura su bautar kasa gari daya ita da kawar ta kadija da kuma wani mutum mai suna yusif,




from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp  08104550703
Read More»

Fateema Habeeb 02

Fateema Habeeb  02


                    na
Jamilu el hussain zazzau



          dedicated to
    Amina baba kaduna



Suna gama cin abincin hajia ta rikewa bashir hannu su wuce daki, jim kadan suma su fatima suka tashi suka wuce daki, suna shiga daki su wuce toilet kowa tai brush, sannan su dawo kowa ta saka kayan bacci su kwanta,

ringing fatima taji wayar ta tayi, tana dubawa taga sahibin ne yakira, murmushi tayi ta daga, sannan su fara dibar firar soyayya,


6:00am na asuba fatima ta farka, tana duba agogo taga lokaci yaja, da sauri ta yunkura ta mike ta nufi toilet ta kama ruwa sannan tai alwala ta fito, kanta tsaye ta dauko dadduma ta shimfida tai sallah, tana idarwa taje ta tashi nusaiba, tace tashi kije kiyi sallah lokaci ya kusan kurewa, da sauri itama nusaiba ta tashi ta nufi toilet,

8:00am fatima ta shiga wanka, tana fitowa taje gaban mirror, kusan 20 mint tana zaune a gaban mirror tana makeup, har nusaiba ta fito daga wanka fatima na zaune tana kwalliya,

murmushi nusaiba tayi, tace anty irin wannan makeup haka sai kace zaki gidan biki, yatsine fuska fatima tayi gami da jefo mata harara, tace ina ruwanki, kadan nusaiba ta saki fuska tace Allah ya baki hakuri, suna gama makeup kowa ta saka kaya suka wuce breakfast,

suna gama karyawa fatima ta wuce daki ta dauko bag dinta, tana fitowa kanta tsaye tanufi dakin hajia, kallon ta hajia tayi tace har kin shirya? eh mom, hajia tace to sai kin dawo, tace to,

tana fitowa daga dakin hajia ta wuce dakin dad dinsu, tun daga kofa tai sallama, zaune yake yana tasbihi ya amsa, cikin ladabi ta gasshe shi, yace har kinyi shirin school din? tace eh dad, yace ok adawo lafiya, tace Allah yasa, tana fitowa kanta tsaye tanufi kofar gida, dai dai lokacin direba na tsaye a jikin mota yana jiranta, fuska a sake tai murmushi ta kalle shi tace muje ko, yace to, da sauri ya bude mata kofa ta shiga yay key su kama hanya,

20 mint suka isa school din, waje ya samu yay parking ta sauko, kallo ta watso mishi tace kaje zuwa anjima kadan saika dawo ka dauke ni, yace to, kanta tsaye ta nufi hole din daza suyi taron,

tun daga nesa ta hangi kawar ta kadija, fuska cike da annuri ta daga mata hannu friend, atare sukai murmushi, sannan taje kusa da ita ta zauna,

jim kadan lecturers suka shigo wajen taron, bayan anyi  addu'a farfesa gambo yafara bayani kamar haka,

barkan mu da wannan lokaci, ina mai farincikin taya ku murna na samun damar hada degree dinku, saboda haka ina kira agareku kowa ya zage dantse yayi ma kasa aiki tukuru a kowani fanni da aka tura shi,

jim kadan bayan gama taron aka rufe da addu'a a tashi,
atare fatima da kadija suka fito, suna tafiya suna fira, dai dai lokacin direba na tsaye a park yana jiran ta, kadan ta saki fuska ta kalle shi tace har ka dawo? yace eh tun dazu ina nan ai, tace eyyah sorry ko, nan suka bude motar suka zauna a kujerar baya ita da kadija, key direba yayi su kama hanya,

dai dai junction din da kadija zata sauka direba yay parking ta sauko, fatima ta kalleta tace to friend sai munyi waya, kadija tace to kigai da gida, nan direba yay key su cigaba da tafiya,

suna isa bakin gate yay horn, da sauri megadi ya taso ta bude musu gate su shige, yana parking ta sauko, kanta tsaye ta nufi cikin gida,




from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp 08104550703
Read More»

Fateema Habeeb 01


Fateema Habeeb  01


                     na
Jamilu el hussain zazzau


           dedicated to
     Amina baba kaduna



Bissimillahirrahamanirrahim



Misalin yamma lokacin rana ta fada, ga iska mai dadi na kadawa tako ina, masoyan ke zaune acikin farfajiyar gida suna fira,

cikin sassanyar murya gami da lumshe ido fatima ta kalli kamal, tace hubby ji nake kamar na fasa zuwa wannan bautar kasar, kadan kamal yay murmushi tare da cewa fatima kenan nima tuntuni nake zullumin zuwan wannan lokacin, domin rabuwar mu abune mai taba zuciya, gashi garin da zakuje gurine mai nisa balle na rika kawo miki ziyara lokaci bayan lokaci, tabbas zan zama abin tausayi muddin idanuwa na suka daina tozali da wannan kyakkyawar surar taki,

kadan fatima tai ajiyar zuciya tace hubby kana jefani cikin kogin tunani mai tsananin zurfi aduk lokacin daka tasani agaba da irin wadan nan tausasan kalaman naka masu ratsa, zuciya, dolene nai bakin ciki da juyayin rabuwa dakai,

murmushi sahibin yayi, yace kar ki damu, na miki alkawarin bazaki taba missin din muryata ba, domin tana tare dake akoda yaushe, kuma ina miki albishir cewa ko ina kije muryata tana biye dake ta waya domin isar da sakonnin soyayya agareki,

babu abinda zai zama cikas agaremu illa rashin ganin fuskokin juna, kadan ya saki numfashi, yace koda yake muna da picture din juna, duk da nasan cewa photo bazai iya gamsar da zuciya ababen da take bukata ba, amma zai rage mata zafin radadin da take ji,

dogon numfashi fatima taja, gami da jefo mishi wani munafukin kallo tace hakane hubby, photo bazai iya gamsar damu ba kamar ace gamu tare, amma zai kasance mana garkuwa da kuma ragema zuciya radadin halinda zata tsinci kanta,

kadan ta sake numfasawa tace, duk da nasan cewa zuciya ta karama ce aduk lokacin data sami matsala akan soyayyar ka zata iya fashewa, da sauri kamal ya katseta, yace ki daina irin wannan tunanin, dolene mubaiwa zukatan mu hakuri, tunda a tsari wannan tafiya taku ta zama dole, cikin kan kanin lokaci idanun fatima su kada kamar hawaye zasu zubo mata, kallon ta kamal yayi, yace kinga banason ganin hawayen ki awaje domin hakan na taba min zuciya, ki kwantar da hankalin ki tafiya ba mutuwa bace, shiru tayi tana sauran shi, sannan ya dago kai ya kalle ta yace zanzo na wuce, sai munyi waya, tace ok muje na taka ma, atare su jera har jikin motar sa suna tafiya suna fira, ya bude mota ya shiga, saida ya wuce sannan ta nufi cikin gida,

hajia ce zaune bisa kujera fatima tai sallama ta shigo, kadan hajia ta dago da kanta ta amsa, cikin sakin fuska fatima tace momy nusaiba basu dawo bako? hajia tace eh, basu shigo ba tukun, cikin daki fatima ta shige ta cire hijabi ta dawo falo ta zauna,

sautin sallama suji, nusaiba ce tare da bashir su dawo daga islamiyya, da sauri bashir yaje ya rungumi hajia, murmushi hajia tayi gami da dafa kansa, tace baby boy an dawo? bashir yay dariya yace eh mom, tace ok jeka aje bag din ka cire uniform ko, yace to, waje nusaiba ta samu ta zauna,

jim kadan hajia taji sautin kiran sallah, kallo ta watso musu, tace to kutashi kuje kuyi sallah, atare nusaiba da fatima su tashi zuwa cikin daki, kowa taje tai alwala tai sallah,

8:00pm duk su dawo dinning suna cin abinci suna fira, hajia ta kalli fatima tace kamar naji ance gobe ana nemanku a school ko? kai fatima ta daga tace eh, karfe tara suce muzo, hajia tace ok Allah ya kaimu, fatima tace amin,



from the experience of jamilu zazzau

WhatsApp 08104550703
Read More»

Sunday, October 6, 2019

ZINA BASHI CE


ZINA BASHI CE

Mutumin yana cewa:

A lokacin da ina saurayina nasami Admission a Jami'a, bayan nafara karatun ne sai na hadu da wata Budurwa (Girlfriend) a cikin Jami'ar tamu muka 'kulla soyayya da ita tamkar ma'aurata, hardai tasami juna biyu, (yayi mata ciki kenan).

Da iyayenta suka gane sai suka tambaye ta wanda yayi mata ciki sai tace nine nayi mata.

Sai yayanta yataho nema na a fusace yana nufin
d'aukar mataki a kaina, yana zuwa saiya tambayeni kaine kayima qanwata ciki ko ???

Sai na amsa masa da cewa:

Wace ce, ni banma taba ganinta ba a rayuwata, ban santah ba. Sakamakon rashin hujjar da zasu kamani da ita dole suka 'kyaleni.

Bayan tsawon zamani, wata rana nadawo gida saina tarar da Mahaifiyata a dur'kushe tana tana kuka. Saina dur Qusa na daga ta sai tasake yanke jiki tafad'i 'kasa har sau uku saina tambaye ta a karo na qarshe:

"Ya Ummi Man ladzhi haddath (me ya faru mama)?

Sai tace: Qanwarkace gata can wani yayi mata ciki! Yace sai naji kamar an sokeni da mashi, hankali na ya tashi na tasa 'keyarta muka tafi wurin wanda tace yai mata cikin.

Da mukaje sai yafada min maganar data tayarmin da hankali.

Bawata magana bace face wadda na fadama yayan yarinyar da nayi
ma ciki a baya.(Ban santa ba, banma taba ganinta ba)!

Bayan zamani yaqara yin nisa sai nayi nufin yin aure nafara neman aure nasamu matar da nake so kuma a kasa lokaci akayi biki, ranar farko dana tare da ita saina sameta ba a matsayin budurwa ba.

Ma'ana tariga tayi zina, tuni hankalina ya tashi. Sai ta fadamin wata magana mai shiga rai.

"Don Allah karufa min asiri, ka suturta al'amarina kaima Allah sai ya suturta al'amarinka."

Yace sai nace a cikin zuciyata: Ya Rabby yakfy, yakfy. (Ma-ana Ya Mahalliccina ya isa haka ya isa haka).

Ya cigaba da cewa: Bayan mun kwashe shekaru da matata sai muka
haifi 'ya mace kyakkyawa gata da haske kamar wata. A lokacin da ta cika shekaru 6 a duniya sai gata wata rana ta shigo gida tana kuka. Me yafaru?

Ai me gadine yayi mata fyad'e! INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN
Aljazaa'u min jinsil amal! Wallahi duk tsiyar da kake sheqewa idan Allah
ta'ala yaga dama sai ya hada maka zafi kan zafi irin wannan! Yanzu kunga shi ya lalata 'yar mutane guda daya tak shi kuma an lalata masa guda uku! Yaa Allah ka Qara karemu daga zina, masuyi kuma Allah ka shiryasu
Read More»
Follow Admin On Twitter naimismo1
Join Our Newsletter